Select a date and time slot to book an Appointment
Date Of Appointment
Masana kimiyya sun yi gargaɗin cewa miliyoyin rayuka ka iya salwanta idan dai ba a ɗauki matakan gaggawa ba wajen daƙile bujerewar da cutar malariya mai saurin yaɗuwa a nahiyar Afirka ke yi wa ga magani ba.
Yanzu haka dai akwai nau'in cutar maleriya da ke bujere wa maganin cutar na artemisinin a yankin Gabashin Afirka.
Girman bujerewar cutar ya ƙaru a wasu sassan nahiyar daga ƙasa da kaso ɗaya zuwa fiye da kaso 20 a tsawon shekaru uku.
Lokaci na ƙarshe da aka samu irin wannan bujerewar ga maganin na cutar a nahiyar Afirka ya janyo ruɓanyar mutuwar ƙananan yara.
Masana kimiyya guda 28 da suke jagora a fagen binciken cutar zazzabin cizon sauron daga ƙasashe 10 sun yi kiran ne a wata mujallar kimiyya.
Maganin maleriya nau'in artemisinin yana kashe ƙwayoyin cutar ne kuma shi ne kan gaba wajen magance cutar.
A karon farko an samu ƙwayoyin cutar da ke bujere wa maganin na artemesinin a ƙasashen Afirka da suka haɗa da rwanda da Uganda da Eritrea.
Kuma nau'in zazzaɓin ya bazu a tsakanin ƙasashen da ma masu makwabtaka.
Yanzu haka fiye da kaso 10 na masu zazzaɓin cizon sauron a ƙasashen Ethiopia da Eritrea da Rwanda da Uganda da tanzania na fama da nau'in da ke bujere wa maganin.
“Yanzu lokaci ya yi da za a ɗauki mataki tun kafin miliyoyin jama'a su mutu sakamakon ƙaruwar magungunan da ba sa iya magance cutar," in ji Farfesa Olugbenga Mokuolu na sashen kula da lafiyar yara na jami'ar Ilori da ke Najeriya.
A shekarar 2016, ba a cika samun na'uin cutar da ke bujere wa maganin na malaeriya ba a arewacin Uganda. To sai dai a shekarar 2019, kaso fiye da 20 na ƙwayar cutar sun nuna bujerewar a yankuna da dama.
Tawagar masana kimiyyar sun ce ci gaba da yaduwar ƙwayar cutar mai bijere wa magani ka iya zama wani abun da ba "za a iya tsaida shi" ba.
Dr Mehul Dhorda, daga cibiyar binciken magunguna ta Mahidol Oxford Tropical Medicine Research Unit a ƙasar Thailand, ya faɗi cewa har yanzu babu tabbas dangane da yadda hakan zai faru cikin gaggawa.
Sai dai kuma an samu irin yanayin bujirewar a yankin gabashin kudancin Asiya inda can ma maganin na artemesinin ya fara gaza yin aiki.
"An samu shekaru 10 zuwa 15 daga lokacin da aka fara gano nau'in cutar ya zuwa lokacin da zama ruwan dare," in ji shi.
An taɓa samun irin wannan yanayi a baya. Cutar zazzaɓin ta bujure wa maganin chloroquine - a gabashin Afirka a shekarar 1970 inda bujerewar ta ci gaba har zuwa yammacin gaɓar kogi a shekarun 1980.
Mace-mace sakamakon maleriya a nahiyar Afirka ta ƙaru daga 493,000 a 1980 zuwa miliyan ɗaya da 600,000 ya zuwa 2004.
"Ina fatan wannan ba wani abu ba ne da zai faru a nahiyar Afirka ba," in ji Dr Dhorda.
"Idna har maganin zazzaɓin maleriya na artemisinin ya fara gaza warkarwa to fa za a samu karuwar yawan mace-mace."
Waɗanda suka yi binciken sun bayar da wasu jerin shawarwari da za su daƙile ƙwayar cutar da kuma sauron da ke yaɗa ƙwayoyin cutar.
Sun kuma bayar da shawarar ƙara wani maganin kan haɗe-haɗen maganin na artemesinin domin ƙara masa ƙarfin da zai yaƙi kwayar cutar.
Sai dai kuma Dr Dhorda ya ce ƙarin zai haifar kashe ƙarin kuɗi: "Za mu iya kashe ƙarin kuɗi amma kuma gwara mu kashe da wurin kafin lokacin da za mu kashe makudai wajen shawo kan cutar lokacin da ta wuce gona da iri."
Sun kuma nemi da:
“Muna kira ga masu samar da kuɗaɗe musamman Gidauniyar samar da kuɗi domin yaƙar cuta mai karya garkuwar jiki ta Aids da tarinfuka da maleriya da kuma shirin shugaban Amurka na yaƙar maleriya..." in ji Ntuli Kapologwe, darektan sashen rigakafi na ma'aikatar lafiya a Tanzania.
We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!
Have a great day!
Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support