- Rebecca Morelle and Alison Francis
- BBC News Science
Hoton ne ya sa da gani za a gane cewa jirgin na Titanic ne- jirgin ya ƙara tunsurewa yana ƙara bayyana daga cikin duhun tekun.
Sai dai wani sabon bincike ya gano yadda zagwanyewar jirgin ke tafiyar hawaniya, inda har yanzu mafi yawansa ke zirya a ƙarƙashin tekun.
An gano wasu sassan jirgin ne- wanda aka fim wanda Jack da Rose suka taka rawa a ciki- bayan wasu masu bincike sun kai ga wajen da jirgin ya maƙale a bana. Hotunan da suka ɗauko sun nuna yadda jikin jirgin ke canjawa bayan sama da shekara 100 a ƙarƙashin ruwa.
Jirgin ya kife ne a Afrilun 1912 bayan ya ci karo da ƙanƙara, inda mutum 1,500 suka mutu.

“Yanayin jikin jirgin akwai ban mamaki. Tunanin da zai zo maka ke nan da zarar ka ga baraguzan jirgin, " inji Tomasina Ray, daraktan tattara sakamakon bincike na RMS Titanic Inc, wanda shi ne kamfanin da ya ɗauki nauyin tafiya binciken.
"Wannan yana cikin abubuwan da suke nuna yadda abubuwa suke tafiya a kullum. Mutane suna yawan tambaya: 'Shin har zuwa yaushe ne jirgin Titanic zai cigaba da kasance a can ƙaƙarshin teku?' muma dai ba mu sani ba, amma muna nan mun zura ido muna kallo,"

Masu binciken sun gano cewa sashen ƙarfen jingina na jirgin, wanda yake da tsayin kimanin mita 4.5 ya karye a cikin shekara biyu da suka gabata.
Hotuna da wasu masu bincike suka ɗauko a shekarar 2022 ƙarƙashin jagorancin kamfanin Magellan and documentary makers Atlantic Productions sun nuna a lokacin cewa ƙarfen bai ɓalle ba, duk da cewa ya fara ɓallewa a lokacin.
"Daga baya sai ƙarfen ya karye, ya faɗi," inji Tomasina Ray.


Ba ƙarfen jinginan ba ne kaɗai ya ɓalle ya nuste a cikin ruwa, duk ƙarafan da ke jikin jirgin ma yanzu sun zama abincin wasu ƙananan ƙwayoyin halitta na cikin ruwa.
Wasu masu ziyarar binciken na baya sun gano cewa wasu sassan jikin na jirgin suna ɓalɓalcewa. Masu bincike a cikin ruwa da suka je a ƙarƙashin kamfanin Victtor Vescovo a 2019 sun dawo da hotuna da ke nuna cewa wani sashe na wajen zaman hafsoshin cikin jirgin ya lalace, ciki har da wajen jagoran jirgin wato captain.
Wannan ziyarar ta bana da kamfanin RMS Titanic ta ɗauki nauyi, an yi shi ne a tsakanin Yuli zuwa Agusta.
Na'urorin ɗaukar hoto daga gida na ROVs guda biyu sun ɗauko sama da hotuna miliyan biyu na sassan jirgin, wanda ke ɓalɓalcewa, inda gaban jirgin da bayansa suka watse da kusan 800m a tsakaninsu, sannan kuma baraguzan jirgin ne lulluɓe da su.
Yanzu kamfanin na cigaba da nazarin hotunan, sannan daga baya zai fitar da cikakken kundin hotuna ta hanyar amfani da fasahar 3D domin nuna cikakken rahoton ziyarar.
Za a ga hotuna da dama da aka ɗauko daga jirgin nan da wasu watanni masu zuwa.

Masu binciken sun kuma bayyana gano wani abun tarihin daban.
A shekarar 1986, wani mai ɗaukar hoto mai suna Robert Ballard ya bayyana hoton wani mutum-mutumi da ake kira Diana of Versailles, bayan ya gano jikin jirgin Titanin a shekarar baya.
Amma ba a gano ainihin inda mutum-mutumin mai tsawon inchi 60 yake ba, wanda hakan ya sa ba a iya adana bayaninsa ba.
Amma yanzu an gano shi a kwance a ƙarƙashin tekun kusa da baraguzan jirgin na Titanic.
"Kamar gano allura ne cikin duhun suma, kuma gano shi da aka yi a bana abu ne mai muhimmanci," inji James Penca, mai bincike a kan Titanic sannan mai gabatar da shirin Witness Titanic.
A kan nuna mutum-mutumin ga mazauna ɓangaren fasinjoji na musamman na jirgin Titanic.
"Ɓangaren fasinjojin na musamman shi ne ya fi kyau da tsari a cikin jirgin ruwan, sannan abun da ya fi kyau a cikin ɗakin shi ne mutum-mutumin na Diana of Versailles," inji shi.
"Amma abin takaici da jirgin ya kife, ya rabe biyu, sai wajen fasinjojin na musamman ya tsage. A cikin wannan ruɗun ne mutum-mutumin Diana ya ɓace a cikin duhun teku."

Kamfanin RMS Titanic Inc yana da ikon zuwa wajen jirgin na Titanic, kuma shi kaɗai yake da ikon cire wani sashe daga cikin jirgin.
A shekarun da suka gabata, kamfanin ya ciro dubban abubuwa daga baraguzan jirgin, inda wasu daga cikin abubuwan ake baje-kolinsu a wurare da dama na duniya.
Kamfanin ya bayyana shirinsa komawa wajen jirgin a baɗi domin gano wasu abubuwan- sannan mutum-mutumin Diana na cikin abubuwan da suke sa ran dawowa da shi a ziyarar tasu ta baɗi.
Sai dai wasu na ganin baraguzan da ma yankin baki ɗaya tamkar ƙaburbura ne bai kamata a riƙa taɓawa ba, ballanta ciro wasu abubuwa.
"Gano mutum-mutumin Diana ya ƙara tabbatar da cewa akwai buƙatar a bar jirgin Titanin ɗin nan kawai, " inji Mista Penca.
"Wannan aikin fasaha ne da aka yi domin a riƙa kalla ina jin daɗi, amma yanzu a ce irin wannan ƙayataccen abu yana kwance a ƙarƙashin ruwa a cikin duhun teku na tsawon shekara 112.
"Dawo da Diana domin mutane su cigaba da kallo - wannan zai ƙara bayyana tarihi da ƙauna da fasaha, Ba zan iya barin irin wannan muhimman abun a ƙarƙashin teku ba."
Da ƙarin bayani daga Kevin Church