Select a date and time slot to book an Appointment
Date Of Appointment
Asalin hoton, Bola Ahmed Tinubu
Gwamnatin Najeriya ta sake jaddada cewar babu batun luwaɗi da maɗigo a cikin yarjejeniy Samoa da suka san ya hannu akai a ƙarshen watan yunin da ya gabata, kamar yadda wasu ƴan ƙasar ke zargi.
Minisitan watsa labaran Najeriya Muhammmad Idris ya shaidawa BBC Hausa cewa yarjejeniyar ta ƙunshi ayyukan ci gaban al'umma ne, kuma an yi ta ne a tsakanin ƙasashen Afrika da na yankin Caribbean, da mutanen Pacific wato OACPS.
Haka kuma Minisitan yaɗa labaran Muhammmad Idris ya ce akwai wata yarjenejiya mai suna OACPS da ta samu goyon bayan ƙasashen Turai da suka sa mata hannu a lokacin da ake taron majalisar ɗinkin duniya na 73.
Ya ci gaba da cewa "Akwai ƙa'idoji har 103 da aka cimma kan wannan yarjejeniya, amma babban al'amari da ya kamata a fahimta a nan shi ne, an yi waɗannan yarjejeniyar ne bisa tsarin shari'a da zai ba da damar haɗin gwiwa tsakanin OACPS da Tarayyar Turai domin cigaban al'umma, da daƙile sauyin yanayi, da samar da kuɗaɗen zuba jari, ba wai yadda mutane ke ta yaɗawa ba.
Ministan yada labaran na Najeirya Muhammad Idris ya ce 'Ko kadan babu gaskiya a cikin wannan zargi, don kafin mu saka hannun kan waɗannan ƙa'idoji 103 sai da aka kafa kwamiti da ya yi taza da tsifa a kansu, wanda ministan kasafin kuɗi Atiku Bagudu ne ya jagoranci kwamtin, sannan akwai minisntan harkokin wajen Najeriya, da Ministan shari'a wanda kuma sai da suka tabbatar da cewar babu wata ƙa'ida daga cikin ƙa'idojin da ta ci karo da dokokin Najeiya sannan aka amice da saka hannun" in ji ministan.
Haka kuma ya ce "ya zama wajibi mu tabbatar wa da 'yan Najeriya cewar Najeriya, da gwamnatin Bola Tinubu ba za ta saka hannu kan wata yarjejeniya ba da za ta ci karo da muradan mutanenten ƙasar nan ba " A cewar Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris.
Ministan yaɗa labaran na Najeriya Muhammad Idris ya ce tun da fari Najeirya ta ƙi amincewa ta sa hannu kan yarjejeniyar ne don kaucewa kisto da kwarkwata da zai kai ga fadawa tarkon irin zargin amincewa da abin da ya saɓa da dokokin ƙasar.
"In ka ga an ƙi amincewa da abu da ba, to akwai dalili, misali an duba an ga akwai wasu abubuwa da suka saɓa da dokokin mu, wadannan dole ne a tsaya a tantance su a zare su, a fitar da su daga cikin yarjejeniyar" Inji minsitan.
Ya kuma ƙara da cewa 'Yanzu an kawo lokacin ne da ke nuni da cewar yarjejeniyar ba ta ci karo da addinin mu ba, ko zamantakewar mu, ko al'adun mu, ko dokokin ƙasar mu ba, don haka ina mai tabbatarwa da al'ummar Najeriya cewar ,da su kwantar da hankulansu, gwamantin Bola Tinubu ba zata taɓa amincewa da abin da ya ke cin karo da dokokin ƙasar nan ba" a cewar Muhammad Idris ministan yaɗa labaran Najeriya.
A ranar Laraba ne wasu rahotonni suka ambato cewa gwamnatin tarayya ta saka hannu kan yarjejeniyar, wadda ta ƙunshi wasu alƙawurra tsakanin ƙasashen Tarayyar Turai, da gamayyar ƙasashen yankin Karebiya da na Pacific .
Rahotonnin sun ambato cewa baya ga ayyukan raya ƙasa da cigaban al'umma, yarjejeniyar ta kuma ƙunshi batun amincewa da gwagwarmayar neman 'yanci da masu fafutikar luwaɗi da maɗigo ke yi a ƙasashen.
A shekarar 2014 Najeriya ta amince da dokar haramta alaƙar aure tsakanin jinsi ɗaya, abin da ke nufin luwaɗi da maɗigo haramtattu ne a ƙasar.
We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!
Have a great day!
Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support