by MUHAMMAD AUWAL UMAR
August 5th 2024.

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/08/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/08/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Muhammad Annur Muhammad

  1. Za a sanya harajin mallakar kyanwa a Kenya

    Hoton mage

    ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

    Mutanen da suka mallaki kyanwa ko mage ko kuma mussa a Nairobi, babban birnin Kenya, na ta nuna damuwa kan abin da suke gani wani shiri na gwamnati na sanya harajin mallakar dabbar.

    A dokokin da hukumar birnin ke shirin yi, za a bukaci duk wani mai kyanwa ya yi wa dabbar tasa rijista.

    Hakan zai bukaci mutum ya biya kudin lasisin mallakarta Sulai 200 (na kasar) kwatankwacin dala 1.50 ko fam 1.20 a duk shekara tare da shedar cewa an yi wa dabbar rigakafin cutar hauka.

    Bayan haka, dole ne kowane mai kyanwa ya dauki alhakin halayyarta ko abin da ta yi - kamar yawo a gari ko unguwa, sannan mutum ya tabbatar ba sa kara ko kuka da zai damu jama'a.

    Bugu da kari, dole ne idan kyanwa tana cikin lokacin bukatar barbara, mai ita ya tsare ta a waje daya.

    Hukumomi sun ce za a yi dokar ne domin inganta hanyoyin kula da lafiyar maguna, abin da wasu ke suka a kai.

    A kwanan nan Kenya wadda ke gabashin Afirka ta yi fama da tarzoma a kan kara haraji da gwamnati ta yi, har ta kai matsi ya sa ta janye karin.

  2. Isra'ila ta kashe gomman Falasdinawa a wani hari a makarantu

    hari a makaranta a Gaza

    ASALIN HOTON,EPA

    Gomman mutane ne suka mutu a wani hari da Isra'ila ta kai na sama kan wasu makarantu biyu a Gaza, kamar yadda masu agaji na Falasdinawa da kafafen yada labarai suka bayyana.

    asu daga cikin wadanda aka kashe Falasdinawa ne 'yan gudun hijira da ke zaune a makarantu.

    Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da kai harin tana mai cewa ta hari cibiyoyin Hamas ne a cikin makarantun a Gaza.

    Harin shi ne na uku a cikin mako daya, da Isra'ila ke t kaddamarwa a kan makarantu a Zirin.

    Kafofin yada labarai na Falasdinawa sun ce mutum akalla 30, wadanda suka hada da mata da yara aka kashe a harin.

    Rahotanni na nuna cewa ana ganin akwai karin mutane a karkashi da cikin buraguzai.

    An kai harin ne a kan makarantar al-Nasr da kuma Hassan Salama a rayau din bayan wani harin da Isra'ilar ta kai a kan wani sansani na 'yan gudun hijira a cikin wani asibiti da ke tsakiyar Gaza, harin da ya kashe akalla mutum biyar.

    Ko a jiya Asabar harin da sojin na Isra'ila suka kai kan makarantar Hamama a birnin ya kashe akalla mutum 17, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

    aka kuma kwanki kafin wannan harin da suka kai kan makarantar Dalal al-Mughrabi ya hallaka mutum 15, in ji jami'ai.

    A wani lamarin na daban, a yau Lahadi da safe wani Bafalasdine ya hallaka 'yan Isra'ila biyu da wuka a birnin Holon, daga bisani an harbe maharin, in ji 'yansanda.

  3. Kamala Harris na tantance wadanda za ta zaba domin taya ta takara a zaben Amurka

    Kamala Harris

    ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

    Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris na ganawa da masu neman ta ba su mukamin mataimakinta a zaben kasar da za a yi a watan Nuwamba.

    Harris tana tantance su ne domin zabar wanda zai rufa mata baya a zaben, kafin ta shiga yakin neman zabe na jihohi bakwai masu matukar muhimmanci a zaben kasar, a mako mai zuwa.

    Daga cikin wadanda ke tafiya zuwa Washington, DC, domin ganawa da Ms Harris, akwai Gwamna Josh Shapiro da Sanata Mark Kelly da Gwamna Tim Walz.

    An takaita masu neman mukamin zuwa mutum biyar kamar yadda kafar yada labarai ta CBS, mai hulda da BBC a Amurka ta bayyana.

    Ana bukatar ta zabi wanda zai mara mata baya kafin babban taron jam'iyyarsu ta Democrat, wanda za a fara ranar 19 ga watan nan na Agusta a Chicago.

    Ba a sani ba ko sauran masu neman wannan mukami da suka hada da gwamnan Kentucky Andy Beshear ko Sakataren sufuri Pete Buttigieg, su ma za su gana da ita.

    A ranar Juma'a ne kamala ta tabbata 'yar takarar shugaban kasa ta jam'iyyar Democrat a hukumance, bayan kuri'ar da wakilan jam'iyyar suka kada.

  4. An kashe sama da mutum 70 a zanga-zanga a Bangladesh.

    Masu zanga-zanga

    ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

    An kashe mutum sama da 70, da suka hada da 'yansanda sama da 12 a Bangladesh, a dauki-ba-dadin da ake yi tsakanin masu tarzomar kin jinin gwamnati da 'yansanda.

    An sanya dokar hana zirga-zirga a kokarin da hukumomi ke yi na dakatar da zanga-zangar da ake yi a fadin kasar, ta neman Firaminista, Sheikh Hasina, ta sauka.

    Zanga-zangar da dalibai ke jagoranta ta faro ne da bukatar soke tsarin daukar aiki na gwamnati na raba-dai-dai mimakon duba cancanta a watan da ya gabata.

    To amma kuma yanzu zanga-zngar ta fadada zuwa ta kin jinin gwamnati gabadaya.

    'Yansanda na amfani da hayaki mai sa hawaye da harsashi na roba da ma na gaske, kamar yadda wasu rahotanni suka nuna, domin tarwatsa zanga-zangar a sassan kasar ta Bangladesh.

  5. An kama gomman masu zanga-zanga a Birtaniya

    ..

    ASALIN HOTON,REUTERS

    Fiye da masu zanga-zanga 90 aka kama bayan bazuwar zanga-zangar da masu ra'ayin riƙau suka shirya a garuruwa da biranen Birtaniya.

    An samu hatsaniya a biranen Hull da Liverpool da Bristol da Manchester da Stoke-on-Trent da Blackpool da kuma Belfast, inda ka lalata shaguna tare da harba hayaƙi mai sai hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar.

    Firaminitsan ƙasar, Sir Keir Starmer ya alƙawarta bai wa 'yansanda ''cikakken goyon baya'' domin ɗaukar mataki kan ''masu tsattsauran ra'ayin'' da ke yunƙurin haifar da ''cikakkiyar ƙiyayya a ƙasar''

    Lamarin dai ya fara ne bayan da aka kashe wasu yara mata uku a wani gidan rawa a Southport a farkon wanann makon.

    Kusan masu zanga-zangar ƙyamar baƙi dubu, suka yi arangama da jami'an tsaro yayin da wasunsu ke rera waƙokin ƙin jinin musulunci.

    A gefe guda kuma an samu fitowar ɗaruruwan masu zanga-zangar adawa da ƙyamar baƙin da rana yankin Liverpool, suna masu kiraye-kirayen haɗin kai da juriya, inda suke rera waƙoƙin ''muna maraba da 'yan gudun hijira''.

    'Yansanda sun samu nasarar shiga tsakanin ɓangarorin biyu ba tare da sun yi aranagama da juna ba, bayan da suka riƙa harba hayaki mai sa hawaye da amfani da karnuka domin kwantar da tarzomar.

    An cinna wa wani ɗakin karatu a kusa da birnin Walton, yayin da masu zanga-zangar suka yi yunƙurin hana 'yan kwana-kwana kashe wutar, a cewar 'yan sandan birnin.

    An yi ta ɓalle shaguna tare da ƙona robobin ajiye shara.

  6. 'Za mu ci gaba da zanga-zanga saboda jawabin Tinubu bai taɓo buƙatunmu ba'

    ...

    Ƙungiyar 'The Take it Back Movement', ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka shirya zanga-zagar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya ta ce ''zanga-zangar za ta ci gaba'', duk kuwa da kiran dakatar da ita da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi.

    Cikin jawabin da ya gabatar wa ƙasar ranar Lahadi da safe, shugaba Tinubu ya yi kira ga waɗanda suka shirya zanag-zangar su dakatar da ita tare da rungumar hanyar tattaunawa.

    To sai cikin wani saƙo da ƙungiyar 'The Take it Back Movement' ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce shugaban bai taɓo buƙatunsu cikin jawabin nasa ba, sannna ya kasa ɗaukar alhakin ''kisan gillar da aka yi wa masu zanga-zangar''.

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Amnesty International ta ce mutum 13 jamai'an tsaro suka kashe ranar Alhamis.

    To sai rundunar 'yansandan ƙasar ta musanta amfani da ƙarfin da ya wuce kima kan masu zanga-zangar, tana mai cewa mutum bakwai ne kawai suka mutu.

    Rundunar 'yansandan ta kama kusan mutum 700.

    A ranar Lahadi wasu mutane da ake zargin ɓata-gari ne sun tarwatsa masu zanga-zangar a birnin Legas da ke kudancin ƙasar.

    Masu zanga-zangar na buƙatar gwamnati ta mayar da tallafin man fetur da ta cire domin rage farashin fetur da na lantarki, haka kuma suna buƙatar hukumomin ƙasar su magance matsalar tsaro da cin hanci da rashawa.

    Ana sa ran ci gaba da zanag-zangar a faɗin ƙasar har zuwa ranar Asabar mai zuwa.

    Shugaban ƙasar dai ya umarci jami'an tsaro su ci gaba da tabbatar da doka da oda.

    Yayin da ake fargabar samun ƙarin arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro.

  7. Amnesty ta buƙaci gwamnan Kano ya kafa kwamitin bincike kan kashe masu zanga-zanga a jihar

    ..

    ASALIN HOTON,X/ABBA KABIR YUSUF

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya gaggauta kafa kwamitin shari'a mai zaman kanta domin binciken kisan da ƙungiyar ta bayyana da na ''ganganci'' kan aƙalla masu zanga-zanga 10 a unguwannin Kurna da Kofar Nasarawa.

    Cikin wata sanarwa da daraktan ƙungiyar, Isa Sanusi ya fitar, ya ce dole ne kwamitin ya yi aikinsa, ba tare da katsalandan ba, kuma ya zama wajibi gwamnati ta ba shi duk abin da yake buƙata don gudanar da aikinsa.

    Ƙungiyar ta kuma ce dole ne a binciki yadda jami'an tsaron Najeriya suka tinkari zanga-zangar, da kuma irin ɓarnar da ''yan dabar'' da aka yi zargin hayarsu domin kawo fitina a lokacin zanga-zangar.

    “Rashin gudanar da bincike kan kashe-kashe da lalata dukiyoyi da aka yi a Kano tun daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa yau, ka iya kawo tarnaƙi ga bin doka da Oda''

    Sanarwa ta ƙara da cewa rashin binciken zai sa ɗabi'ar nan ta rashin hukunta masu laifi ta ci gaba da wanzuwa a ƙasar, kamar yadda dama ba sabon abu ba ne a Najeriya, in ji sanarwar.

    An dai samu hatsaniya a lokacin zanga-zangar adawa da matsin rayuwa da aka gudanar a Kano cikin makon nan, inda aka zargi jami'an tsaro da harbe masu zanga-zangar.

  8. Ƙasashen duniya sun buƙaci al'umominsu mazauna Lebanon su fice daga ƙasar

    ..

    ASALIN HOTON,EPA

    Ƙasashen duniya da dama ciki har da Amurka, na ci gaba da kiraye-kiraye ga al'umominsu da ke zaune a Lebanon su gaggauta ficewa daga ƙasar, sakamakon ƙaruwar fargabar ɓarkewar yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Iran ta sha alwashin mayar wa Isra'ila mummunar martani kan zarginta da kisan shugaban Hamas Ismail Haniyeh a birnin Tehran ranar Laraba.

    Har yanzu dai Isra'ila ba ta ce komai ba game da kisan shugaban na Hamas.

    Mutuwarsa na zuwa ne sa'o'i bayan harin Isra'ila ya kashe babban kwamandan ƙungiyar Hezbollah Fuad Shukr a birnin Beirut.

    Jami'an ƙasashen Yamma na fargabar cewa ƙungiyar Hezbollah a Lebanon da ke samun goyon bayan Iran za ta taka rawa a martanin da Iran ɗin za ta mayar, wanda kuma ka iya haifar mummunar martani daga ɓangaren Isra'ila.

    Amurka da wasu ƙasashen Yamma na ci gaba da yunƙurin yayyafa ruwa ga wutar da ke ƙoƙarin tashi a yankin.

    Kawo yanzu dai ƙasashen Amurka da Birtaniya da Sweden da Faransa da Canada da Jordan sun umarci al'umominsu da ke zaune a Lebanon su gaggauta ficewa daga ƙasar.

  9. Kada ku yarda wani ya ce muku gwamnatinku ba ta damu da ku ba - Tinubu

    ..

    ASALIN HOTON,BOLA AHMED TINUBU/X

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi kira ga 'yan ƙasar kada su yarda wani ko wasu mutane su yaudare su da wasu maganganu domin su ga baiken gwamnatinsa.

    Cikin jawabin da ya yi wa 'yan ƙasar, Tinubu ya ce a matsayinsa na shugaban ƙasar, yana iya bakin ƙoƙarinsa don ganin ya saisaita tattalin arzikin ƙasar don cin moriyar duka 'yan ƙasar.

    ''Kada ku yarda wani ya faɗa muku ƙarya ko ya yaudare ku da labaran ƙanzon kurege kan ƙasarku, ko ya ce gwamnatinku ba ta damu da ku ba. Duk da cewa a baya an kasa cimma fatan da aka yi, amma yanzu muna cikin sabon babi'', in ji shugaban ƙasar.

    ''Muna iya bakin ƙoƙarinmu, kuma za a ga sakamako nan ba da jimawa ba kowa zai gani a ƙasa'', in ji shi.

  10. Buga gyam ya kai ni ƙasashen waje - matashi ɗan Najeriya

    Farouk Manzo, matashi ne da ya ƙware wajen buga wasannin gyam (game) a kan kwamfiyutarsa, inda har ya mayar da baiwar da yake da ita sana'a.

    Matashin mai shekara 21 ya ce buga wasannin gyam ya kai shi ƙasashen duniya kamar Faransa da Masar da Ivory Coast.

    Ya ce wasan gyam bai hana shi neman ilmi ba, inda zuwa yanzu ya karanta fannin tattalin arziƙi.

    Ya ce a wannan shekara ma, yana shirin zuwa ƙasar Saudiyya don buga gyam

    Bayanan bidiyo,Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  11. Gwamnatin Somaliya ta kama manyan jami'an tsaron ƙasar kan harin Lido

    ..

    ASALIN HOTON,..

    Gwamnatin Somaliya ta kama wasu manyan jami'an tsaron ƙasar a Mogadishu bayan wani harin ƙunar baƙin wake da na bindiga da aka kai wurin shaƙatawar bakin ruwa na Lido ranar Juma'a.

    Aƙalla mutum 37 ne suka mutu wasu fiye da 200 suka jikkata, kamar yadda ma'aikatar lafiyar ƙasar ta bayyana.

    Firaministan ƙasar, Hamza Abdi Barre ya ce an kama jami'an ne bisa sakacin tsaro da ya faru har aka kai harin.

    A ranar Asabar, shugaban ƙasar, Hassan Sheikh Mohamud ya yi ganawar gaggawa da hukumomin tsaron ƙasar domin nazarin harin.

    Fitaccen wurin shaƙatawar na Lido na unguwar AbdiAziz a Mogadishu, babban birnin ƙasar.

    Kuma ya kasance wuri mai matuƙar tsaro, sannan unguwar da manyan jami'an gwamnati ke zaune.

    A baya ƙungiyar Al-Shabaab ta sha yunƙurin kai wa unguwar hare-hare.

  12. Mun bai wa jihohi fiye da naira biliyan 570 don tallafa wa talakawa- Tinubu

    Shugaba Tinubu

    ASALIN HOTON,BAYO ONANUGA/X

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya ta bai wa jihohin ƙasar 36 fiye da naira biliyan 570 domin faɗaɗa shirye-shiryen tallafa wa talakawansu.

    Hakan na ƙunshin cikin jawabin da shugaban ƙasar ya yi da sanyin safiyar yau Lahadi.

    Ko a kwanakin baya ma gwamnatin tarayyar ta ce ta bai wa kowace jiha tirela 20 ta shinkafa domin raba wa talakawan ƙasar, kodayake a baya-bayan nan wasu jihohin sun ce ba su samu kasonsu ba.

    Haka kuma shugaba Tinubu ya ce masu ƙananan sana'o'i 600,000 ne suka samu tallafin bashi daga gwamnatin tarayyar.

    Ya ƙara da cewa yanzu haka gwamnati na tantance masu matsakaitan sana'o'i mutum 75,000 domin samun bashin naira miliyan guda kowanennsu, da za su fara samu cikin wannan wata.

    ''Su kuwa masu manyan kamfanoni za mu ba su bashin naira biliyan ɗaya kowannesu don bunƙasa kasuwancinsu'', in ji shugaban ƙasar.

    A ranar 1 ga watan Agusta ne dai wasu 'yan ƙasar suka fantsama kan titunan ƙasar domin gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da suke fuskanta a ƙasar.

  13. Atiku ya yi Allah wadai da harbin masu zanga-zanga a Najeriya

    .

    ASALIN HOTON,ATIKU ABUBAKAR/FACEBOOK

    Jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai kan amfani da harsasai kan masu zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya fitar, ya zargi jami'an tsaron ƙasar da harbin wasu masu zanga-zangar.

    Atiku Abubkar ya ce harbin masu zanga-zangar lumana abin takaici ne, da ya yi kama da na lokacin mulkin kama karya na sojoji.

    ''Yana da kyau in tuna wa gwamnati da jami'an tsaro game da babban haƙƙinsu na tabbatar da tsaro ga 'yan ƙasar da ke son gudanar da zanga-zangar, wadda ke cikin 'yancinsu da kundin tsarin mulkin ya tanadar musu'', in ji Atiku Abubakar.

    A lokacin zanga-zangar an samu rahotonnin harbi a jihohin Kano da Borno da Kaduna da wasu jihohin ƙasar.

    To sai dai Atiku Abubakar ya ce, a duk lokacin da jami'an tsaro suka buɗe wuta kan masu zanga-zanga, to babu abin da hakan zai haifar illa tayar da yamutsi.

    Tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam'iyar PDP ya yi kira ga majalisar Dinkin Duniya da Kotun Duniya su sanya idanu kan abin da ke faruwa a Najeriya tare da tuhumar jagororin ƙasar da jami'an tsaro kan abin da suke aikatawa.

  14. 'Yan tawayen M23 sun ƙwace iko da wani gari a gabashin DR Kongo

    .

    ASALIN HOTON,.

    Rahotanni daga gabashin Kongo na cewa ƴan tawayen M23 sun ƙwace iko da wani gari dake kusa da kan iyakar Uganda.

    Lamarin ya faru ne ranar Asabar, daidai lokacin da wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta ta wata guda ta zo ƙarshe.

    Mazauna garin sun ce dakarun da ke goyon bayan gwmanati sun janye daga garin bayan da ƴan tawayen suka shiga garin.

    Wata sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a gabashin Kongon da Angola ta shirya tare da sa hannun- Kongo da Rwanda, za ta fara aiki yau.

    Sai dai ƴan tawayen M23 ɗin sun kafe cewa ba su cikin yarjejeniyar da gwamnatocin Kongo da ta Rwanda suka sanya wa hannu a ranar Alhamis.

  15. Hezbollah ta ce ta harba gomman rokoki zuwa Isra'ila

    ..

    ASALIN HOTON,..

    Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta ce ta harba gomman rokoki zuwa arewacin Isra'ila.

    Hezbollah ta ce harin wani ɓangare ne na martanin hare-hare ta sama da Isra'ilar ta kai a ƙauyuka biyu na Lebanon a jiya Asabar.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun daƙile harin ta hanyar kakkaɓo rokokin, yayin da wasu kuma suka faɗa bayan gari inda babu mutane.

    A 'yan kwanakin baya-bayan nan an samu ƙaruwar zaman ɗarɗar a yankin Gabas ta Tsakiya bayan kisan shugaban Hamas Ismail Haniyeh a birnin Tehran da kuma kisan wani kwamandan ƙungiyar Hezbollah a Lebanon.

  16. Assalamu alaikum

    Masu bin shafinmu na BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki, musamman Najeriya da makwabtan ƙasashe.

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

mukhzafaya@gmail.com
Search Website

Search

Explore

Categories

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support