Ƙasar da ta fi yawan masu kashe kansu a duniya

Matlohang Moloi’s home.
  • Marubuci,Andre Lombard
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari,BBC Focus on Africa, Hlotse & Maseru
  • Aiko rahoto dagaLesotho

Hanyar zuwa gidan Matlohang Moloi mai shekara 79 da ke zaune cikin tsaunuka a Lesotho ba mai sauki ba ce, kuma hakan na cikin dalilin da ya sa ta zama ɗaya daga cikin mafiya girma a duniya.

Mahaifiyar mai 'ya'ya 10 ta nemi na je gidanta mai cike da tsafta, inda take nuna hoton wasu daga cikin iyalanta. Na zo nan ne domin tattaunawa kan ɗaya daga cikin yaranta - ɗan fari mai suna Tlohang.

Ɗan shekara 38 ɗin na cikin masu nuna fushi. Lesotho ta kasance ƙasar da aka fi aikata kisan kai a duniya.

"Tlohang yaro ne mai hankali. Ya faɗa mani matsalolin kwakwalwa da yake fuskanta," in ji Ms Moloi.

"A ranar da ya kashe kansa, ya zo wajena ya faɗa min cewa mahaifiyata, wata rana za ki ji cewa na kashe kaina".

"Mutuwarsa ta ɗimauta ni. Na so da ya faɗa min abubuwan da ke damun sa. Ya shiga damuwar cewa idan ya faɗa wa mutane za su yi tunanin cewa shi rago ne wanda ba zai iya magance matsalolinsa ba."

Tlohang's ID card.
Bayanan hoto,Wannan shi ne Tlohang, ɗan Matlohang Moloi', wanda ya kashe kansa

A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, kashi 87.5 cikin mutum 100,000 na al'ummar Lesotho ne ke kashe kansu a kowace shekara.

Hakan ya ninƙa na ƙasar da ke biye mata, Guyana da ke kudancin Amurka, inda alkaluman ba su fi kashi 40.

Adadin ya kasance fiye da kashi 10 na alkaluman masu kashe kansu a duniya, wanda ya nuna cewa mutum tara cikin 100,000 ne ke kashe kansu.

Hakan ne ya sa wata ƙungiya mai zaman kanta - mai suna HelpLesotho - ke zimmar kawo sauyi na rage masu kashe kansu ta hanyar bai wa matasa horo da yadda za su kare lafiyar kwakwalwarsu.

A garin Hlotse, wanda ke da nisan sa'a biyu daga Maseru, babban birnin ƙasar, na zauna cikin wata ƙungiya mai bai wa wasu 'yan mata horo na yadda za su kare kansu, wanda Lineo Raphoka, mai rajin kawo sauyi a cikin al'umma, ke gudanarwa.

"Mutane na ganin kamar hakan ya saɓa da tsare-tsarenmu a Afirka, da al'adunmu, da kuma addini, da kuma a matsayin al'umma baki ɗaya," kamar yadda Patience mai shekara 24 ta faɗa wa mutanen da ke ɗaukar horo a ƙungiyar.

"Sai dai kuma mutane ba su son fitowa su yi magana kan abin duk da cewa yana faruwa. Ina magana ne saboda na rasa ƙawayena guda uku waɗanda suka kashe kansu, nima na taɓa yunkurin aikata haka."

Lineo Raphoka na bai wa mutanen da suka yi yunkurin kashe kansu shawarwari
Bayanan hoto,Lineo Raphoka na bai wa mutanen da suka yi yunkurin kashe kansu shawarwari

Da yawa daga cikin mutane sun taɓa tunanin kashe kansu, ko kuma sun san wanda ya kashe kansa.

Ntsoaki mai shekara 35 ta shiga ɗimuwa lokacin da take faɗa wa ƙungiyar labarin fyaɗe da aka yi mata a asibiti.

"Likitan ya faɗa min cewa ina da kyau. Daga nan ya fitar da bindiga ya faɗa min cewa yana son ya kwanta da ni, indai na ki zai kashe ni.

"Kowane lokaci ina tunanin cewa kashe kaina shi ne kaɗai mafita. Ba zan iya ba, ba zan iya aikata hakan ba. Abu guda da ya sa rayuwata ta ci gaba da gudana shi ne ganin fuskokin ƴan'uwana. Sun yi imanin cewa ina da karfin juriya, amma na san ba ni da shi."

Ƙungiyar ta jaddada mata cewa tana da karfin juriya saboda bayar da labarin da ta yi.

Yayin da lokacin bayar da shawarwarin ya kare, dukkan matan suna ta tattaunawa da kuma yin murmushi, inda suka ce sun ji daɗi saboda faɗan labaransu.

Da yawa dai, dalilan da suke janyo mutane ke kashe kansu na da tsarkakiya, kuma yana da wahala a ce ga dalili guda da ke janyo hakan. Duk da haka, Ms Raphoka ta ce tana ganin abin da ya sa aka bayyana Lesotho a matsayin ƙasar da aka fi aikata kisan kai.

"Yawanci mutane na shiga matsaloli kamar fyaɗe, rashin aikin yi, rashi saboda mutuwa. Shan giya da kuma kwayoyi."

A cewar wani rahoton hukumar Kula da Al;umma ta Duniya na 2022, ya ce kashi 86 na mata a Lesotho sun fuskanci cin zarafi.

A gefe guda, Bankin Duniya ya ce mutum biyu cikin biyar ba su da aikin yi ko zuwa makaranta.

"Ba sa samun isasshen taimako daga wajen iyalansu, abokai ko kuma duk wanda suka yi mu'amala da shi," in ji Ms Raphoka.

Abu ne da ake yawan ji a Lesotho. Mutane sun sha faɗin cewa ba sa jin daɗin magana kan matsalar kwakwalwarsu - kuma mutane za su yanke musu hukunci a kan haka.

Zaune a wata mashaya a wani yammaci, inda wani ke shan giya da kuma tattauna batun siyasa yayin da ake kallon kwallo a talabijin ɗin da ke wurin, daga nan na jagoranci tattaunawa kan lafiyar kwakwalwa.

"Muna tattauna batun, muna cewa a fito a yi magana," kamar yadda Khosi Mpiti ya faɗa min.

Khosi Mpiti (hagu) ya ce maza na samun sauki wajen taimaka wa juna
Bayanan hoto,Khosi Mpiti (hagu) ya ce maza na samun sauki wajen taimaka wa juna

Wasu na fargabar cewa idan suka fito suka faɗi matsalolinsu za a yi ta magana a kai, duk da hakan, ya ce abubuwa na sauyawa.

"A matsayinmu na abokai, muna taimakawa juna. Idan ina da matsala ina faɗa wa ƙungiyarmu, kuma muna taimakawa juna."

Idan mutane suka nemi taimako, suna fuskantar matsaloli ganin cewa tsarin kiwon lafiyar ƙasar ya shiga wani hali.

An soki sashen kula da kwakwalwa ɗaya tilo da ƙasar ke da shi a bara - daga wurin wata jami'i wanda aikinta shi ne duba abubuwan da mutane ke so - saboda rashin samun likita ko ɗaya mai kula wa kwakwalwa tun 2017. Ta kuma bayyana yadda ake samun batutuwan cin zarafi, ciki har da yanayin rayuwa da saɓa wa ƴancin ɗan'adam.

Babu kuma wani tsari na ƙasa don magance matsalar kwakwalwa a ƙasar a baya, duk da da cewa gwamnati - wadda aka zaɓa a 2022 - ta ce tana cikin shirin samar da irin wannan tsari.

"Matsalar kwakwalwa ta zama annoba a duniya," in ji Mokhothu Makhalanyane, wani ɗan majalisa wanda ke jagorantar kwamitin majalisa da ke duba batutun lafiya.

Ɗanmajalisa Mokhothu Makhalanyane ya ce kawo karshen tsangwama da ake yi wa mutanen zai kawo babban sauyi
Bayanan hoto,Ɗanmajalisa Mokhothu Makhalanyane ya ce kawo karshen tsangwama da ake yi wa mutanen zai kawo babban sauyi

"Muna tabbatar da cewa an ƙara kaimi wajen wayar da kai, daga makarantun firamare, zuwa manyan makarantu, da wuraren da matasa ke taruwa, kamar gasannin kwallon kafa da ake shiryawa," kamar yadda ya faɗa wa BBC.

"Tsarin zai kuma bijiro batun jinya da za a yi mutane, zai kuma bai wa waɗanda lamarin ya shafi su je su samu horo wajen sake tunani."

Ya kuma ce Lesotho za ta iya ɗaukar darasi daga yaƙin da take yi da cutar HIV.

A 2016, ta zama ƙasa ta farko da ta ɓullo da tsarin "gwaji da kuma jinya", abin da ke nufin za a fara yi wa mutane jinya da zarar an yi musu gwaji. Alkaluman masu kamuwa da cutar ya ci gaba da raguwa.

"Abin da muka sani shi ne fitowa a yi magana, ba tare da ɗora laifi ko kuma sukar mutane kan yanayi da suke ciki, zai taimaka wajen sauya abubuwa."

Komawa kan tsaunukan, Ms Moloi ta yi ƴar tafiya zuwa wurin kabarin ɗanta Tlohang.

An saka wata alama a kan kabarinsa domin a ci gaba da tuna shi.

Wurin da aka binne ɗan Matlohang Moloi ba shi da nisa daga gidanta
Bayanan hoto,Wurin da aka binne ɗan Matlohang Moloi ba shi da nisa daga gidanta

Ms Moloi na ɗaya daga cikin mutane da yawa a Lesotho da ke fama da rashin na kusa da su, sakamakon kashe kansu.

Yayin da muka zo tafiya ta ce tana da sako ga waɗanda ke da niyyar kashe kansu kamar yadda ɗanta ya yi.

"Zan faɗa wa mutane cewa kashe kansu ba shi zai taɓa zama mafita ba. Abin da ya kamata ku yi shi ne yi wa waɗanda ke kusa da ku magana domin su taimaka muku."