by MUHAMMAD AUWAL UMAR
July 23rd 2024.

Gwamnatin Najeriya ta ce ba daidai ba ne matatar Dangote ta rinka samar da fetur ita kadai

.

ASALIN HOTON,ALIKO DANGOTE

Gwamnatin Najeriya ta fara yunƙurin sasanta saɓanin da ya kunno kai tsakanin matatar mai ta Dangote da hukumomin da ke kula da harkokin man a ƙasar.

Matakin gwamnatin na zuwa ne bayan wani zama da aka yi tsakanin shugaban rukunin kamfanonin na Dangote, Alhaji Aliko Dangote da sauran masu ruwa da tsaki a harkar man fetur karkashin jagorancin karamin ministan man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, da sauran shugabanin bangarorin kula da harkokin man getir din a Najeriya a yammacin jiya Litinin

Alhaji Faruk Ahmed, shi ne shugaban hukumar da ke sanya ido kan harkokin man fetur a Najeriya watau NMDPRA, kuma ɗaya daga cikin wadanda suka halarci taron na ranar Litiin, a yayin hirarsa da BBC ya musanta zargin cewa suna kokarin yi wa Dangote zagon kasa.

“Shi da kansa ya ce muna taimaka masa muna da ma’aikata fiye da mutum 10 da ke wannan matata suna aiki babu dare ba rana domin ganin komai ya tafi yadda ya kamata kuma shi da kansa ya zo ya yi godiya, don haka batun a ce muna yi masa zagon ƙasa, ba dai-dai ba ne'' in ji Alhaji Faruk Ahmed.

Ya ƙara da cewa ''Abin da mutane ba sa so shi ne a saka musu dokoki, wataƙila sun fi so a bar su, su yi abin da suka ga dama”

Tun bayan fara aiki a watan Janairu, matatar ta Dangote ta riƙa samun saɓani da kamfanin mai na Najeriya NNPCL, inda kamfanin ya fara cewa sinadarin sulfur da ke cikin man matatar ya zarta adadin da ake buƙata.

Saɓanin har ya yi zafin da har Aliko Dangote ya bayyana cewa a shirye yake ya sayar wa NNPCL da matatar ta biliyoyin daloli.

"NNPCL na iya sayen matatar don tafiyar da ita yadda yake so. Sun bayyana ni a matsayin mai babakere a harkar kasuwanci. Wannan ba gaskiya ba ne kuma bai dace ba, amma babu laifi. Idan za su saya, aƙalla za su yi maganin wanda suka kira mai babakere," kamar yadda Dangote ya shaida wa jaridar Premium Times.

Matatar Dangote ta kuma ce tana tattauna wa da ƙasashen Libya da Angola domin samo ɗanyen mai bayan rashin samun wadatarsa a Najeriya, ƙasar da ta fi arziƙin mai a Afirka.

Faruk Ahmed ya ce babu wata matsala a kan matatar man Dangote, sai dai ba abu ne mai yiwuwa a amince da bukatarsa tagamin cewa an dakatar da wasu yan kasuwa daga shigo da man ba, a siya a wajensa shi kadai, wanda kuma kasuwa ba haka take ba, ba zai yiwu a ce mutum daya shi zai yi kasuwancin abu ba.

Game da ingancin man da matatar ke samarwa kuwa, ya kuma ce suna da takardu da suka nuna ingancinsa bai kai na wanda ake shiga da shi kasar daga waje ba.

“Dokokin kasashen Ecowas sun ba da damar duk da haka za a iya aiki da man da ingancinsa bai kai na wannan ba ma, don haka muka ce shi ma za a iya amfani da shi, don haka babu maganar a ce ana msa kutunguila'' inji shugaban hukumar da ke sanya ido kan harkokin man fetur a Najeriya watau NMDPRA.

Ya nanata cewa suna bai wa hamshakin dan kasuwar Aliko Dangote hadin kai, domin a cewarsa ''Shi dan Najeriya ne kuma dan arewa, mu ma ƴan arewa ne, shi Musulmi ne, muma haka, a,mma dole ne a kare jama'a, a kasuwa ba a cewa dole sai dai a sayi abu daga wajen wane''.

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
Search Website

Search

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support