Wane hali ake ciki kan batun zanga-zanga a Najeriya?

Protest

Yayin da 'yan Najeriya ke shirin fara zanga-zangar gama-gari, tun daga yau Alhamis, 1 ga watan Agusta, domin jawo hankali game da karuwar matsin rayuwa ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa da jama'ar kasar da dama ke fama da su, mun duba shirye-shirye da matakan da aka dauka game da ita wannan zanga-zanga.

Duk da kokarin bangaren gwamnati da shugabannin al'umma da na addini da sauran masu ruwa da tsaki na lallashi da bayar da alwashi, har ma da tabbaci na bin matakan shawo kan matsalolin tsadar rayuwa, domin dakatar da zanga-zangar kwana goma da ake shirin fara gudanarwa a duk fadin Najeriya daga yau, da alamu wadanda suka shirya wannan zanga-zanga suna nan kan bakansu.

Barista Solomon Dalong, tsohon ministan matasa da wasanni, kuma shugaban gamayyar ƙungiyoyin da ke cikin zanga-zangar a yankin arewacin Najeriya ya ce zanga-zanga na nan daram,"bisa ga tsari za a kai kwana goma ana yi, kafin a sake tsara yadda za a ci gaba, domin zanga-zangar nan ita ce yaren da gwamnati ke ji kawai".

"Da safiyar nan za a tada zanga-zangar nuna rashin gamsuwa kan yadda ake mukar mutane a Najeriya, wadda ta haifar da yunwa da talauci da rashin tsaro a ƙasar."

Dangane da fargabar da ake ta bayyanawa, cewa wannan zanga-zangar lumana ka iya rikidewa ta koma tashin-tashina kuwa, jigon zanga-zangar ya ce sun yi tanadin duk abin da ya kamata, don kauce wa hakan.

"Mun ja wa mutanenmu kunne, mun fitar da tsare-tsare da za a gudanar da zanga-zanga ta lumana, kuma duk wanda aka ga cewa zai taɓa kayan wani ko zai fasa shagon wani ko zai taɓa kayan gwamnati, za a kama shi a miƙawa jami'an tsaro."

Kwamred Adamu Sambo yana cikin masu shirya zanga-zangar a yankin kudancin Najeriya, can ma ya ce sun shirya tsaf, "mun yi shirye-shirye da dama duk wani abu da ake buƙata mun riga mun tadana, za a yi zanga-zangar nan ta lumana, ba tare da tashin hankali ba."

Tuni dai jami'an tsaro a matakai daban-daban suka tanadi hanyoyi irin na kandagarki a daukacin jihohin Najeriya, gami da babban birnin tarayya Abuja.

Domin ganin wasu ɓata-gari ba su yi maye fake da agana, sun tayar da zaune tsaye ba, a lokacin wannan zanga-zanga wadda masu shirya ta ke ta nanata cewa, ta lumana ce. Kuma babban abin fata a nan game da zanga-zangar, shi ne a kwashe tuwonta da mara.