by MUHAMMAD AUWAL UMAR
July 21st 2024.

Yadda rahoton BBC ya daƙile shirin korar ƴan Arewa daga jihar Delta

.

ASALIN HOTON,SHERIFF OBOREVWORI

A yanzu haka dai hankalin 'yan arewacin Najeriya mazauna garin Abavo da ke jihar Delta ya kwanta, biyo bayan janye wa'adin da ake zargin masarautar garin ta ba su na kwanaki hudu da su fice daga garin, saboda yawaitar matsalar sace-sacen jama'a da ta addabi yankin.

Janyewar wannan wa’adi dai ta biyo bayan kwarmata lamarin da 'yan arewar suka yi a sashen Hausa na BBC, abin ya kai ga kunnen fadar shugaban Najeriyar, da gwamnan jihar ta Delta, da shugaban ƙaramar hukumar Ika ta Kudu, da Haɗakar ƙungiyoyin kare fararen hula na arewacin Najeriya ta CNG, na shiga tsakani.

Sarkin Hausawan garin na Abavo, Usman Alasan ya shaidawa BBC cewar “mun yi sallah lafiya ranar juma’a babu wanda ya ce mana kanzil, gwamnan jihar ya turo mana wakilai don jin halin da muke ciki, sannan aka tura DPO ya je wajen sarakunan yankin, inda kuma ya dawo ya sanar da su cewar an janye wannan wa’adi da aka ba su''

Sarkin Hausawan garin na Abavo ya ce “Dukkan ɓangarorin an yi kira garesu tare da jan hankalinsu da dukkan su zauna da juna lafiya ba tare da wata fargaba ba” inji shi.

''Babu wani sharadi da aka shimfida mana na ci gaba da zama a garin, muna ci gaba da jan hankalin Hausawan da ke yankin da su ci gaba da kiyaye doka da oda, kar su ɓata mana suna, sannan su ci gaba da kasuwancinsu, tunda babu wani sharadi ko matakai da aka gindaya mana” Inji Sarkin Hausawan.

A makon da ya gabata ne hankalin al'ummar arewacin ƙasar da ke zaune a garin Abavo da ke jihar Delta, yake a tashe, sakamakon wa'adin kwanaki huɗu da ake zargin masu garin sun ba su, na barin garin, kan yadda ake satar mutane a yankin.

Sai dai a yayin wata hira da BBC, Sarkin Hausawan garin Usman Alhassan ya ce lamarin ya dama lissafin wasu daga cikinsu, saboda yadda suke fama da kuɗin cin abinci bare ta mota, kuma wa’adin kwana huɗu da suka basu ya yi kaɗan.

Sai dai wani ɗan majalisar masarautar garin na Abavo ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin," sai dai ya ce an ɗauki matakin ne don yawaitar sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa, da sauran maganganu da ya ce lokacin faɗarsu beyi ba sai wani lokaci.

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
Search Website

Search

Explore

Tags

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support