by MUHAMMAD AUWAL UMAR
July 21st 2024.

*AHLIL-KISA'I DARUL-MUIQAMATY*

*ZUBAR DA JINI DA KARKASHE "YA'YAYEN ANNABI(S) DA WASU SUKA YI, A CIKIN ADDININ NAN😭*
              *~(KASHI NA 25)~*



*YA UBANGIJI, MAFI GIRMAN SALATY DA AMINCI DA GAISUWARKA SUYI TA GUDANA GA KYAKKYAWAN BALARABANKA S.A.W. TARE DA IYALANSA TSARKAKAN MA'ASUMAI, DA KUMA DUK SAHABIN DA YAKE DA GIRMA A ZUCIYAR SAYYIDA FADIMA A.S*

*Bayan shafe kwanaki uku da su sayyida Zainab suka yi suna Makoki a karbala, a rana ta Hudu sai Imam Zainal-Abidin A.S  ya Umarci kowa da ya shirya za'a Huce Madina.*

*Sai Sukaina taje ta Rungumi Kabarin Babanta Imam Hussain A.S tana masa bankwana, ta fashe da kuka mai tsanani! Tana rera wasu Baituka masu motsa zuciya da sa zubar Hawaye! Mata suka barke da kuka da sowa.*

*Sayyida Zainab ta tashi ta nufaci kaburburan 'Ya'yan Manzon Allah(S) da na 'Yan'uwanta, tana musu bankwana! Ta je wannan kabarin ta fadi tana kuka ranta kamar zai fita, ta sake ta shi da kyar ta je Kan wani.*

*Sai Imam Zainal-Abidin ya ce kowa ya tashi ya hau kan Abin Hawansa a tafi, Sai wasu suka nemi a dan jinkirta, sai Imam Zainal-Abidin A.S ya ce musu: "Ya ku mutane! Shin ba ku ganin abinda nake gani ne?*

*Wallahi ina tsoran kar Goggona Zainab ta mutu ne! Ba ku ga yadda take tashi daga wannan Kabarin zuwa waccan ba? Sai mata suka zo suka kama sayyida Zainab S.A za su daga ta, suka ce mata:*

*"Tashi Ya Zainab mu tafi" sai ta ce: "Ina zamu je? "Sai suka ce mata: zamu koma Madina" sai ta ce musu: "Wa ya rage min a Madina balle in je Wajensa?! Sai da Imam Zainal-Abidin Ya zo ya Rarrasheta sannan ta Tashi suka Tafi*

*SAYYIDA ZAINAB (S.A) A BIRNIN MADINA!😭*

*Tawagar su sayyida Zainab S.A sun baro Karbala sun doshi Birnin Madina, Bashar bn Hazlam ya ce: lokacin da muka iso Daf da Madina, sai Aliyu dan Hussaini Zainal-Abidin A.S ya sa aka Yada zango, aka sauke kaya, mata ma suka sauka.*

*Sai ya ce: "Ya Bashar! Allah ya yi Rahama ga Mahaifinka, ya kasance Babban mawaqi ne, shin ka ga ji wani abu na Fasahar Wakarsa?" Bashar ya ce: Kwarai na gada Ya dan Manzon Allah!(S)" Sai Imam Ya ce mun: "To ka shiga Madina ka rera waka kan Abinda Ya samu Aba-Adallah.*

*Bashar ya ce: " Sai na hau kan dokina na sukwane shi, na shiga Madina, na je Masallacin Manzon Allah(S) na d'aga Sauti na rera Waka kan kashe Imam Hussaini (S.A) da aka yi, sai Jama'a suka Barke da kuka!*

*Sannan sai na ce musu: Ga Aliyu dan Hussaini nan Tare da Goggonsa Zainab da 'Yan uwansa Mata sun Makwabci garinku, sun yada zango a Bayan gari, Ni dan aikensu ne zuwa gareku don in sanar da ku dawowarsu! Sai Imam Zainal-Abidin A.S  ya tashi, Ya Umarci tawagar da karasa cikin Madina!*

*Mu hadu a kashi na 26 da Yardar Allah*

*~Zamzam Baqurasshen Umma na supy 08033567648~*

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support