Cutuka na yaɗuwa a Gaza saboda ɓallewar ruwan kwatami

Wani Bafalasɗinen yaro kenan yake tsaye a kusa da ruwan kwatami ba babu takalami a tsakiyar Birnin Gaza (ranar 19 ga watan Yulin 2024)

Asalin hoton,Getty Images

Bayanan hoto,Wani Bafalasɗinen yaro kenan yake tsaye a kusa da ruwan kwatami ba babu takalami a tsakiyar Birnin Gaza (ranar 19 ga watan Yulin 2024)
  • Marubuci,Ahmed Nour, Abdirahim Saeed, Lamees Altalebi & Paul Cusiac
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari,BBC Arabic

Launin ruwan kogunan da suka fito daga tekun Baharrum waɗanda suka ratsa Zirin Gaza sun fara sauyawa zuwa makuba yayin da ƙwararru ke gargaɗin ɓarkewar cutuka sakamakon ɓallewar hanyoyin kwatami.

Hotunan da aka ɗauka na tauraron ɗan'adam, waɗanda Sashen Larabci na BBC ya nazarta, sun nuna yadda wani babban kwatami ya buɗe a gefen kogin da ke birnin Deir al-Balah.

Wani jami'in yankin ya faɗa wa BBC Arabic cewa mutanen da aka kora daga muhallansu kan kora bahaya da fitsarinsu kai-tsaye zuwa cikin koguna.

"Hakan na faruwa ne saboda ƙaruwar mutanen da aka kora daga gidajensu kuma da yawansu kan haɗa banɗakunansu hanyoyin wucewar ruwa kaɗai," a cewar Abu Yazan Ismael Sarsour, shugaban kwamatin agajin gaggawa na Deir al-Balah.

Wim Zwijnenburg, ƙwararre kan muhalli a ƙungiyar Pax for Peace, ya tabbatar da cewa ruwan kwatami na tunkarar teku daga sansanoni bayan nazartar hotunan.

Hoton tauraron ɗan'adam da ke nuna yadda kwatami ya kwarara zuwa cikin tekun meditaraniya a gaɓar Zirin Gaza a ranakun 25 da 2 ga watan Agusta
Bayanan hoto,Hoton tauraron ɗan'adam da ke nuna yadda kwatami ya kwarara zuwa cikin tekun meditaraniya a gaɓar Zirin Gaza a ranakun 25 da 2 ga watan Agusta

Kwatamin da aka gani a hotunan da aka ɗauka ranar 2 ga watan Agusta, sun shafe kusan nisan murabba'in kilomita biyu (2 sq km). Bayanai sun nuna kwatamin ya fara kwarara ne a watan Yuni kuma ya ci gaba da tafiya daidai tsawon wata biyu.

Sai dai babu tabbas ko kwatamin na cigaba da ƙaruwa saboda babu sabbin hotuna da aka ɗauka.

Munanan hare-haren Isra'ila sun jawo lalacewar kayan kula da shara a Gaza, kamar yadda wani rahoton kwamatin Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana a watan Yuni.

Hukumar da ke kula da tsaftar muhalli a yankin Falasɗinawa da ke ƙarƙashin ma'aikatar tsaron Isra'ila mai suna Cogat, ta faɗa wa BBC Arabic cewa an kafa wani kwamati na musamman da zai taimaka wajen shawo kan lamarin a Gaza.

A cewar wata sanarwa, a ƴan watannin nan Cogat ta taimaka wajen gyara rijiyoyi da matatun ruwa a Gaza.

BBC ba za ta iya tantancewa ba ko an samu ingantuwa a lamarin tsaftar a Gaza. Isra'ila da Masar ba su barin ƴan jarida su shiga Gaza ba tare da rakiya da kuma sa-idon dakarun sojan Isra'ila ba.

An tilasta wa mutanen da aka kora daga muhallansu a Gaza kafa tantina a gefen koguna, inda kwatami ke wucewa

Asalin hoton,Getty Images

Bayanan hoto,An tilasta wa mutanen da aka kora daga muhallansu a Gaza kafa tantina a gefen koguna, inda kwatami ke wucewa

Ƙwararru a harkokin lafiya na nuna damuwa kan cutukan da yaɗuwa ta ruwa bayan wani jariri ɗan wata 10 ya gamu cutar shanyewar ɓarin jiki sakamakon cutar shan'inna (polio) - karo na farko a Gaza cikin shekara 25.

Jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) da na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun yi kira da dakatar da buɗe wuta na tsawon mako biyu sau biyu domin su samu damar yi wa yara 600,000 allurar rigakafi a Gaza.

Sai dai masu sa'ido kan ce kai rigakafin zai gamu da ƙalubalen da sauran kayan agaji suka fuskanta, inda za a samu cikas wajen raba su ga masu tsananin buƙata.

Da take amsa tambayoyin BBC Arabic, Cogat ta haƙiƙance cewa ba a hana kayayyakin kula da lafiya shiga zirin.

Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafukan zumunta ta ce "za a shigar da ƙarin rigakafi 60,000 domin yi wa yara sama da miliyan ɗaya" a cikin makonni masu zuwa.

Ƙungiyar ba da agaji ta Oxfam ta faɗa wa BBC Arabic cewa kusan kashi ɗaya cikin huɗu na al'ummar Gaza sun kamu da cuta saboda cutukan da ke yawo a ruwa.

"Muna ji muna gani annoba na shiri n ɓallewa," in ji Lama Abdul Samad, wata ƙwararriya kan ruwan sha da tsafta a Ocfam.

"Shan'inna cuta ce da ke yaɗuwa a ruwa kuma ana alaƙanta ta da matsalar tsafta."

"An lalata kayayyakin kula da tsafta sosai ta yadda kwatami ke bin tituna, kuma mutane ke zaune a gefen kwatamin," kamar yadda ta bayyana.

Hotunan wani rafi kenan a unguwar Sheikh Radwan da ke Birnin Gaza ranar 10 da 26 ga watan Yulin 2024

Rafin da ke unguwar Sheikh Radwan a arewacin Gaza, wanda ke da ruwa mai tsafta a baya, ya fara tumbatsa da gurɓataccen ruwa.

A bayyane take cewa ruwan ya gurɓata ne da kwatami, in ji Ms Abdul Samad bayan ta ga hotunan.

"Ruwan kwatami na shiga gidajenmu saboda cikar da Rafin Sheikh Radwan ya yi," kamar yadda Ibrahim Hamza ya bayyana.

Contaminated water in Sheikh Radwan lagoon in northern Gaza (21 July 2024)

Asalin hoton,Getty Images

Bayanan hoto,A baya mutane kan yi amfani da Rafin Sheikh Radwan a matsayin ruwan sha

A gefe guda kuma, wani ma'aikaciyar agaji a Ghada al-Haddad ya tura wa BBC Arabic wani bidiyo da aka ɗauka a wani sansani da ruwan kwatami ya taru kusa da jama'a. Ta ce warin wurin "mai gigitarwa" ne da "ba a iya jurewa".

A farkon wannan watan, hukumar Unrwa ta MDD ta bayar da rahoton 40,000 da ke da cutar hanta ta Hepatitis A - wadda za a iya ɗauka ta hanyar shan gurɓataccen ruwa - a Gaza tun bayan fara yaƙin idan aka kwatanta da mutum 85 da ke da cutar kafin yaƙin.

Ƙwararru na kuma yin gargaɗi game da ɓarkewar amai da gudawa.

Zafi da rashin ingantaccen ruwa sun jawo ɓarkewar annobar cutukan fata musamman tsakanin yara

Asalin hoton,Reuters

Bayanan hoto,Zafi da rashin ingantaccen ruwa sun jawo ɓarkewar annobar cutukan fata musamman tsakanin yara

Hukumomin ba da agaji a Gaza na fama wajen kula da masu cutar atini, da lumoniya, da sauran cutukan da suka shafi fata saboda matsala a ɓangaren kula da lafiya.

"Dalilin yaɗuwar waɗannan cutuka shi ne lalacewar harkokin tsafta gaba ɗaya," a cewar Dr Ahmed al-Farra, wani likitan yara.

MDD ta yi ƙiyasin cewa akasarin mutum miliyan 2.3 na Gaza na zaune ne a sansanoni tun bayan kakar da ta gabata.

Da yawan mutane na zaune ne a wuraren da ke da banɗaki ɗaya ga mutum 600, a cewar WHO a watan Yuli.