Ina aka kwana kan rabon shinkafar gwamnatin tarayya a jihohin Najeriya?

Shugaban Najeriya Bola Tinubu

ASALIN HOTON,NIGERIA PRESIDENCY

Makonni biyu da suka gabata ne Gwamnantin Tarayyar Najeriya ta sanar da matakin tura shinkafa tirela 20 zuwa dukkanin jihohin Najeriya da kuma Abuja, babban birnin ƙasar.

Ministan yaɗa labarun ƙasar, Mohammed Idris wanda ya bayar da sanarwar, ya ce an ɗauki matakin ne domin rage raɗaɗin matsin tattalin arziƙi da al'ummar ƙasa ke fama da shi.

To sai dai tun bayan sanarwar, an ji tsit; ba a ga jihohin sun shiga hada-hadar raba waɗannan buhunan shnkafa da gwamnatin tarayyar ta sanar cewa ta ba su ba.

Wannan ya janyo guna-guni tsakanin al'umma, inda wasu ke tababa game da gaskiyar batun na gwamnatin tarayya, yayin da wasu kuma suka fara nuna wa gwamnoni yatsa.

Hakan ya sanya har sanya haƙurin wasu daga cikin al'umma ya ƙare har suka fara tuhumar gwamnoninsu.

Wasu kuma gwamnonin sun yanke shawarar fitowa da kansu su yi bayani kafin al'umma su fara tuhumarsu.

Buhunan shinkafa

ASALIN HOTON,NIGERIA CUSTOMS SERVICE

Najeriya dai na fama da matsin tattalin arziƙi, inda tashin farashin kayan masarufi da durƙushewar darajar naira suka sanya abubuwa da dama suka gagari talaka.

Farashin buhun shinkafa mai nauyin 50kg a yanzu ya zarce naira 75,000 a yankuna da dama na ƙasar yayin da aka sayar da ita kan naira 35,000 a shekarar da ta gabata.

A rahoton da Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta fitar ta ce hauhawar farashi a ƙasar ta ƙaru zuwa kashi 34.19 cikin 100 a watan Yunin 2024.

Hauhawar ta fi shafar kayan abinci inda sabbin alƙalumman na hukuma suka ce ya kai kashi 40.87 a watan Yunin 2024 idan aka kwatanta da Yunin 2023 inda aka samu ƙaruwar kaso 15.6.

Wannan na daga cikin dalilan da wasu matasa a ƙasar ke dogaro da su wajen shirya wata zanga-zanga da suka ce za su fara yi daga ranar ɗaya ga watan Agusta.

Sai dai tun bayan ɓullar batun yin zanga-zangar ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara fitowa tana sanar da ɗaukan wasu matakai na rage raɗaɗi, wanda rabon shinkafar na daga cikinsu.

To amma yayin da aka kwashe mako biyu bayan sanarwar da gwamnatin tarayyar ta bayar, jihohi da dama sun fito sun bayyana cewa ba su ji ɗuriyar shinkafar ba.

'An ce sun bayar, amma muna jiran tsammani'

A lokacin da ya tattauna da BBC, Sakataren yaɗa labaru na gwamnan jihar Adamawa Humwashi Wonosikou ya ce har yanzu jihar ba ta samu buhunan shinkafar da gwamnatin tarayya ta ce ta ba su ba.

Ya ce "An ce sun bayar amma har yanzu muna jiran tsammani...abin da bai zo hannunka ba ba naka ba ne."

Wonosikou ya ce da zaran wannan shinkafa da gwamnatin Najeriyar ta alƙawurta ta iso hannun jihar, to kuwa za ta raba ta ba tare da ɓata lokaci ba.

A nata ɓangaren ma gwamnatin jihar Gombe ta bayyana cewa har yanzu ba ta samu shinkafar ba.

Isma’ila Uba Misilli, wanda shi ne mai magana da yawun gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya ce "har yanzu shinkafar gwamnatin tarayya ba ta kai ga isa hannun gwamnatin jihar Gombe ba."

Tun farko a ranar Talata, gwamnan jihar ya fitar da sanarwa ta hannun daraktan yada labaran nasa yana nuna damuwa kan rashin karɓar tirelolin shinkafar na gwamnatin tarayya.

Jihar ta Gombe ta bayyana cewa ta riga ta tsara yadda za ta gudanar da rabon kayan tallafin tun kafin ya isa jihar.

'Mun samu namu kason'

Sai dai a nata ɓangaren, jihar Kaduna ta ce ta samu tirelolin shinkafar kuma tana nan tana tsara yadda za ta fara rabo.

Muhammad Lawal Shehu, wabda shi ne mai magana da yawun gwamnan jihar Kaduna ya faɗa wa BBC cewa "Ina tabbatar maka cewa sun iso Kaduna kuma ana nan an tsara yadda za a raba.

"An riga an kafa kwamiti wanda ke yin kyakkywarn shirin ganin yadda za a yi rabon ba tare da an samu matsala ba," in ji shi.