Abu biyar game da zanga-zangar da matasa ke shiryawa a Najeriya

- Nkechi Ogbonna
- BBC News, Lagos
A Najeriya, ƴan ƙasar da dama sun shirya gudanar da zanga-zangar nuna adawa da hauhawar farashin kayan masarufi a ƙasar, wadda ke cikin ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziƙi a Afrika.
Masu kiran yin zanga-zangar sun ce za ta fara ne daga ɗaya ga watan Agustan 2024.
Ƙasashe da dama dai na fuskantar tsadar rayuwa da hauhauwar farashin kaya, amma abin ya yi ƙamari a Najeriya sanadiyyar cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi da kuma karyewar darajar naira kan dalar Amurka da sauran kuɗaɗen ƙasashen yamma.
Me ya sa ƴan Najeriya ke cikin damuwa?
Yunwa na ɗaya daga cikin babban dalilin da ya jefa ƴan Najeriya cikin ƙunci da rashin jin daɗi kuma ita ce ke ingiza batun gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar.
A baya-bayan nan ne dubban ƴan kasar suka yi zanga-zanga a wasu jihohin arewancin ƙasar da suka haɗa da Neja da Kano da Kogi da kuma Oyo da ke kudu maso yamma domin neman gwamnati ta samar da abubuwan da za su sauƙaƙa wa al'umma tsananin rayuwa da suke ciki.
A Kano, inda farashin kayan masarufi kamar shinkafa da gero da masara suke hawa, mutum wajen miliyan 10 ne ka zama cikin talauci, wanda shi ne mafi girma a ƙasar.
A makon da ya gabata ne Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta bayar da rahoton cewa, hauhawar farashin ta haura zuwa kashi 35.4 daga kashi 29.9 cikin ɗari sakamakon tashin farashin kayan abinci wanda shi ne mafi girma a cikin kusan shekaru 30.

Yaya tsadar abinci yake a Najeriya?
Farashin burodi - ɗaya daga cikin abincin da iyalai a ƙasar suka fi amfani da shi wajen karin kumallo - ya haura daga naira 500 zuwa naira 1,500 a cikin shekara ɗaya.
Farashin sauran kayan abinci da suka haɗa da ƙwai, da kifi da nama da shinkafa, da man girki, duk sun haura.
Farashin buhun shinkafa mai nauyin 50kg a yanzu ya kai naira 75,000 yayin da aka sayar da ita kan naira 35,000 a shekarar da ta gabata.
A baya dai, ƙungiyar ƙwadago ta bai wa gwamnatin ƙasar wa'adin kwana 14 don magance matsalar tattalin arziƙi da ƙasar ke fuskanta inda ƙungiyar ta yi barazanar shiga yajin aiki a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu idan gwamnati ba ta biya buƙatunsu ba.
Ƙungiyar ta ce matsalar tattalin arziƙin ƙasar ta fi shafar ma'aikata da gwamnati ke biya albashi mafi ƙanƙanta na naira 30,000 wato dala 20 ke nan duk wata.
Bankin bunƙasa ƙasashen Afrika ya yi gargaɗin cewa Najeriya da Habasha da Angola da kuma Kenya na cikin haɗarin fuskantar tashin hankali sakamakon hauhawar farashin man fetur da kayan masarufi.

Waɗane nau'ukan abinci ƴan ƙasar suka koma amfani da?
A wasu ɓangarorin Arewancin ƙasar, mazauna na amfani da duddugar shinkafa da ake zubarwa a matsayin abinci. Duddugar shinkafar da ake amfani da shi a matsayin abincin kifi da ake kiwo yanzu ya zama abincin da wasu ƴan Najeriya ke ci don magance yunwa.
Faya-fayen bidiyo da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda iyalai ke kasafta ɗan abincin da suke da shi yayin da suka rage yawan abincin da suke ci a rana.
Ɗaya daga cikin bidiyon ya nuna yadda wata mata ke raba kifi ɗaya zuwa yanka tara a maimakon yanka huɗu. Matar ta ce tana yin hakan ne domin iyalinta su iya cin kifi aƙalla sau biyu a rana.

Me gwamnati ke yi kan lamarin?
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya sanar da kafa wani kwamiti da zai riƙa sarrafawa da kuma daidaita farashin abinci. Gwamnati ta kuma umarci a raba tan 42,000 na hatsi da suka haɗa da masara da gero.
Wannan ba shi ne karo na farko da gwamnati ke cewa a raba wa ƴan Najeriya da ke cikin talauci da masu rauni kayan agaji ba.
Amma kuma ƙungiyoyin ƙwadago sun sha sukar gwamnati kan hanyoyinta na rarraba kayan abinci inda suka ce ba ya kai wa ga masu ƙaramin ƙarfi da ke da buƙata.
Su wane ne kuma ke ƙoƙarin nemo mafita?
A ƙoƙarin samun sauƙin matsalar tattalin arziƙin ƙasar, wasu ma'aikatu sun rage wa ma'aikatansu ranakun zuwa aiki, ta haka, za su samu sauƙin kuɗin mota da suke kashewa.
Wasu kamfanonin kuma sun ƙara wa ma'aikatansu albashi da kashi 50 cikin ɗari.
Wasu masu sarrafa abincin dabbobi kuwa sun ce za su dakatar da sayen kayan abinci da suke amfani da shi wajen sarrafa abincin dabbobi da suka haɗa da masara da dawa saboda mutane su samu isassun kayan a kasuwanni.
Wannan shawarar dai ta shafi masana'antar dabbobi, wani muhimmin ɓangare a harkar abinci a Najeriya.