NNPCL ya fitar da jadawalin farashin man Ɗangote a faɗin Najeriya

Kamfanin mai na Najeriya, NNPC Ltd ya fitar da jadawalin yadda farashin man da ya sayo daga matatar man Ɗangote, zai kasance a gidajen mai na NNPC a faɗin ƙasar kamar haka:
- Legas - N950.22
- Oyo - N960.22
- Rivers - N980.22
- Sokoto - N999.22
- Kano - N999.22
- Kaduna - N999.22
- FCT - N999.22
- Borno - N1,019.22
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a safiyar ranar Litinin, NNPCL ya ce bisa tsarin dokar albarkatun man fetir ta ƙasa, gwamnati ba ta da hurumin fayyace farashin mai, sai dai ana fitar da farashin ne bayan tattaunawa tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki a harkar.
Sanarwar ta kara da cewa saɓanin yadda yake a rahotanni, kamfanin zai rinƙa sayen man daga Ɗangote da dalar Amurka har ƙarshen watan Satumba, inda sai ranar 1 ga watan Oktoba ne kamfanin zai fara biyan Ɗangote da naira.
Kamfanin ya ƙara da cewa "idan ƴan Najeriya ba su gamsu da farashin ba, to da zarar kamfanin Ɗangote ya yi ragi to su ma za su gaggauta yi wa ƴan Najeriya ragin ɗari bisa ɗari." In ji sanarwar.

Manyan motoci 300 sun yi lodin man daga matatar Ɗangote

A ranar Lahadi 15 ga watan Satumba ne dai kamfanin na NNPCL ya sanar da fara dakon man daga matatar man ta Ɗangote.
Manyan motocin dakon mai 300 ne suka kasance a harabar matatar inda suka yi lodi.
Mamba a kwamitin shugban ƙasar kan saye da sayar da man, Zacch Adedeji, ya ce daga ranar 1 ga watan Oktoba NNPLC, zai fara jigilar ganga 385,000 a kowace rana, kuma kamfanin zai sayi tataccen man ne da kuɗin kasar wato naira.
“Ina mai farin cikin sanar da cewa an kammala duk wani shiri na fara jigilar rukunin farko na mai daga matatar Dangote,” in ji mista Adedeji.
Saura yarjejeniyoyin da kwamitin ya cimma sun haɗa da sayen da man dizel daga matatar ga kowane mai sha'awa, to amma NNPCL ne kawai matatar za ta sayar wa man fetur.
Ana dai sa ran shigar man Dangoten kasuwa, zai kawo sauƙi ga matsalar mai da ƙasar ke fuskanta a baya-bayan nan.
Bayanai kan matatar mai ta Ɗangote

Matatar wadda ke yankin Ibeju-Lekki a birnin Legas na da faɗin hekta kusan 2,635.
A cewar Rukunin Kamfanonin Dangote, matatar man ita ce irinta mafi girma a duniya da ke da cibiya guda ɗaya da ke iya tace ɗanyen mai har ganga 650,000 a kullum.
Matatar na da ƙarfin da za ta wadatar da buƙatar Najeriya dangane da man fetur har ma a yi ragowar da za a fitar wajen domin sayarwa.
An tsara matatar yadda za ta iya tace nau'ika da dama na ɗanyen man fetur, ciki har da na ɗanyen man ƙasashen Afirka da wasu na Gabas ta Tsakiya da kuma na Amurka.
Matatar Dangoten na da tankuna 177 da za su iya ajiye litar mai biliyan 4.742.
A cewar wata sanarwa daga kamfanin, Dangote zai yi amfani da wasu jiragen ruwa na yashe teku mafi girma a duniya domin aikin kwashe yashin gaɓar teku da ya kai zurfin murabba'in mita miliyan 65 a kan yuro miliyan 300.