Dalilan da suka sa muka kama jami'an hukumar alhazai ta Najeriya - ICPC

Alhazan Najeriya na 2024

ASALIN HOTON,NAHCON

Bayanan hoto,Alhazai 51,447 ne suka yi rajista da hukumar Nahcon a aikin Hajjin 2024

Tun a ranar Laraba ne rahotonni suka ɓulla cewa hukumar yaƙi da rashawa da ayyukan da suka saɓa ƙa'ida ta Najeriya ICPC ta kama wasu manyan jami'an Hukumar Alhazai ta ƙasa wato Nahcon.

Wani babban jami'i a hukumuar ya tabbatar wa BBC da kamen, amma ya ce tuni aka bayar da belin su kuma suna taimaka wa hukumar da bayanai. Sai dai mai magana da yawun hukumar ta ce mutum ɗaya ne aka gayyata.

Bayanai sun nuna cewa hukumar na neman bahasi ne game da yadda aka kashe naira biliyan 90 da gwamnatin tarayya ta bai wa Nahcon a matsayin tallafi ga mahajjatan Najeriya a ibadar 2024 da aka kammala a watan Yuli.

Tun da farko naira miliyan 4.9 ne hukumar ta tsayar a matsayin kuɗin kujerar zuwa aikin Hajjin da maniyyata za su biya, amma sai ta mayar da shi miliyan shida da 800,000 tana mai ɗora alhakin kan karyewar darajar naira.

A wannan yanayin ne kuma rahotonni suka ɓulla cewa gwamnatin tarayya ta tallafa da biliyan 90, wanda hukumar ta ce ta rarraba su tsakanin alhazai 5,447 da suka tafi ta hannun gwamnati.

Me ya sa ICPC ta kama shugabannin Nahcon?

Tun a ranar 30 ga watan Yuli ICPC ta gayyaci shugaban Nahcon, Jalal Arabi, domin ya yi mata bayani game da yadda hukumar ta gudanar da aikin Hajjin na bara.

Wata sanarwa daga hukumar ta ce an gayyace shi ne kawai bisa tsari kamar yadda hukumar ta saba yi duk bayan kowane aikin Hajji.

"Duk da cewa gayyatar tasa za ta haifar da fargaba a zukatan abokan hulɗa, hukumar na tabbatar da abu ne da aka saba yi domin kare kadarorin al'umma kuma bincike ba shi nufin aikata laifi," a cewar kakakin hukumar, Fatima Sanda Usara.

Mataimakin darakta a sashen hulɗa da jama'a na ICPC, Hassan Salihu, ya faɗa wa BBC cewa daga baya sun gayyaci ƙarin jami'ai, waɗanda ta kama a yanzu bayan "sun ƙi amsa gayyatar".

Sai dai bai bayyana sunayensu ba.

"Da a ce sun zo lokacin da aka gayyace su za mu cigaba da yin binciken cikin sirri kamar yadda aka saba yi a duniya," in ji shi, "to taurin kai da raina hukuma ne ya sa aka kamo su, amma an bayar da belinsu."

Da aka tambaye shi game da sunayen mutanen da suka nuna turjiyar, sai ya ce: "Tsarin doka bai bayar da dama a bayyana sunayensu ba."

Sai dai mai magana da yawun Nahcon, Fatima Usara, ta ce mutum ɗaya ne hukumar ta "gayyata".

"Mutum ɗaya ne kuma shi ma bai kai matsayin darakta ba," a cewarta.

"An gayyaci daraktocinmu duka kuma sun amsa gayyatar. Mutum ɗaya na sani wanda bai amsa gayyatar ba kuma suka zo suka tafi da shi."

Badaƙalar da majalisar dattawa ta gano a Nahcon

Sanata Ibrahim Abdullahi Dan Baba, tsohon wakilin Sokoto ta Kudu ne a Majalisar Dattijai ta Najeriya kuma ya shaida wa BBC irin badaƙalar da bincikensu ya gano game da ayyukan wasu daga cikin jami'an Nahcon.

Sanatan ya ce ya gabatar da ƙudirin neman yi wa dokar hukumar gyara da zimmar sauƙaƙa wa alhazai yawan kuɗin da ake biya duk shekara domin zuwa Saudiyya.

Ɗan majalisar ya ce ya bukaci majalisa ta tara da ta gabata ta gudanar da bincike kan badaƙalar da ke cikin aikin Hajji a Najeriya kuma majalisar ta kafa wani kwamitin bincike.

"Biciken ya gano ana sace kuɗaɗen mahajjata, otel da yakamata a kama na kwana 40 sai a kama na kwana 90, sauran kwanakin kuma sai a zuba Larabawa a ɗakunan bayan alhazai sun tafi, sai a raba kuɗin tsakanin masu otel da shugabannin Nahcon na wancan lokacin, inda otel zai ɗauki kashi 25 su kuma shugabanni su ɗauki kashi 75," a cewar sanatan.

Ya ƙara da cewa kaɗan daga cikin kuɗaɗen da aka sace sun kai naira biliyan ɗaya.

Dan majalisar yana ganin naira miliyan uku sun yi tsada ga masu zuwa aikin Hajji, kuma "da an ɗauki matakan da suka dace da kuɗin aikin Hajjin bai kai haka tsada ba," a cewarsa.

An shafe shekaru da dama ana kwan-gaba kwan-baya kan batun yi wa dokar gyara, sai dai babu tabbas ko akwai batun yanzu haka a gaban majalisa ta 10.