by MUHAMMAD AUWAL UMAR
July 23rd 2024.

  1. BBC HAUSA Labarai da dumi-dumi,Gwamnatin Najeriya na yunƙurin sasanta Dangote da hukumomin man fetur

    Matatar mai ta Dangote

    ASALIN HOTON,@SENLOKPOBIRI

    Bayanan hoto,Daga hagu zuwa dama: Gbenga Komolafe, Heineken Lokpobiri, Aliko Dangote, Mele Kyari, Farouk Ahmed

    Gwamnatin Najeriya ta fara yunƙurin sasanta rikicin saɓanin da aka samu tsakanin matatar mai ta Dangote da kuma hukumomin da ke kula da harkokin man a ƙasar.

    Ƙaramin Ministan Man Fetur Heineken Lokpobiri ya ce ya jagoranci wani zama da Aliko Dangote shugaban kamfanin Dangote, da Mele Kyari shugaban kamfanin NNPCL, da Farouk Ahmed shugaban hukumar Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA), da Gbenga Komolafe shugaban Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission (NUPRC) a yammacin yau Litinin.

    "Ganawar wani yunƙuri ne na gano maganin matsalolin da matatar ke fuskanta," in ji ministan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

    "Dukkan ɓangarorin sun nuna aniyarsu ta nemo bakin zaren kuma sun nuna jin daɗinsu da yunƙurin sasantawar da ake yi."

    Wannan ne karon farko da ɓangaren gwamnati ya yi magana kan cecekucen da ɓangarorin ke yi bayan hukumomin sun zargi matatar Dangote da fitar da man dizel maras inganci, wanda ta musanta ta hanyar gudanar da gwaji a gaba 'yanmajalisar tarayya ranar Asabar.

    Aliko ya koka kan yadda kamfanonin cikin gida suke ƙin sayar wa matatar tasa ɗanyen man fetur ɗin domin fara tace shi da kuma sayar da shi a Najeriya.

    Rahotonni sun ce matatar ta mayar da hankali wajen sayo ɗanyen man daga ƙasashen Libya da Angola domin tace man da za ta fara fitarwa kasuwa a watan Agusta mai zuwa.

    Matatar mai ta Dangote

    ASALIN HOTON,@SENLOKPOBIRI

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
Search Website

Search

Explore

Categories

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support