Ta yaya TikTok zai yaƙi yunƙurin haramta shi da Amurka ke shirin yi?

Bajon TikTok a kan waya

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,Bajon TikTok a kan waya

Kamfanin China da ya mallaki dandalin sadarwa na TikTok zai kai ara kotu a ranar 16 ga watan Satumbar nan domin ƙalubalantar umarnin da Amurka ta ba shi na sayar da dandalin ko kuma ta haramta amfani da shi.

ByteDance zai nemi a dakatar da barazanar rufe TikTok, inda zai nemi kotun ta ayyana hakan a matsayin take haƙƙin faɗar albarkacin baki da ke ƙunshe a kundin mulkin Amurka.

Ta yaya Amurka ke yin barazanar rufe TikTok?

A watan Afrilun 2024, Shugaban Amurka Joe Biden ya saka hannu kan wata doka mai suna Protecting Americans Against Foreign Adversary Controlled Applications Act - wato dokar kare Amurkawa daga manhajojin ƙasashen waje - wadda ta samu karɓuwa sosai a majalisar ƙasar.

Dokar ta haramta wa manhajojin da ƙasashen da ba ƙawayen Amurka ba suka mallaka kamar Rasha, da China, da Iran, da Koriya ta Arewa amfani da su a ƙasar.

Hukumomi sun yi amfani da dokar a kan kamfanin da ya mallaki TikTok, inda suka umarce shi da ya sayar da dandalin ko kuma a rufe shi. An ba su wa'adin zuwa 19 ga watan Janairun 2025.

ByteDance denies this Akwai damuwa a Amurka kan cewa ƙila kamfanin ByteDance na kwashe bayanan 'yan ƙasar ta hanyar amfani da TikTok domin bai wa gwamnatin China. Amma kamfanin ya musanta hakan

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,Akwai damuwa a Amurka kan cewa ƙila kamfanin ByteDance na kwashe bayanan 'yan ƙasar ta hanyar amfani da TikTok domin bai wa gwamnatin China. Amma kamfanin ya musanta hakan

Hukumomin Amurkar sun damu ne musamman kan TikTok. Kamfanin ByteDance ne ya mallaki kashi 20 na hannun jarin TikTok, sauran kuma masu zuba jari ne da kuma ma'aikatan kamfanin.

Majalisa da kuma Fadar White House na ganin ByteDance zai iya miƙa wa hukumomin leƙen asiri na China bayanan Amurkawa masu amfani da dandalin su miliyan 170, abin da zai iya taimaka mata wajen leƙen asirin Amurka.

TikTok kan ajiye bayanan masu amfani da shi kamar yadda sauran dandalin sada zumunta ke yi, kamar Facebook, da Instagram, da Snapchat, da YouTube. Bambancin kawai shi ne gwamnatin Amurka ta aminta da su saboda na cikin ƙasarta ne.

Akwai kuma fargabar za a iya yin amfani da tsarin TikTok na "For You" (wanda ke kawo wa masu amfani da shi abubuwan da yake ganin za su so kallo) a matsayin hanyar sauya tunanin Amurkawa.

Ta yaya za a iya rufe TikTok?

Idan hukumomin Amurka na son toshe TikTok, ana tsammanin za su yi hakan ne ta hanyar goge shi daga shagunan sauke manhaja - kamar na Apple da Google - inda za a hana sauke shi a Amurkar.

Hakan na nufin masu amfani da shi a Amurka ba za su iya sabunta manhajar ba a ƙasar.

Haka nan, kamfanonin da ke ba da layin intanet za su saka takunkumi kan layukan da ke taimaka wa TikTok.

Amma gwamnatin Amurka ta ce tana so ne ta ƙwace mallakin TikTok ɗin daga hannun China maimakon rufe shi baki ɗaya.

Wane ne ke ƙalubalantar haramcin, kuma me suke cewa?

Shugaban TikTok, Shou Zi Chew, ya ce rufe dandalin zai saɓa wa dokar 'yancin ra'ayi ta Amurka

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,Shugaban TikTok, Shou Zi Chew, ya ce rufe dandalin zai saɓa wa dokar 'yancin ra'ayi ta Amurka

A ranar 16 ga watan satumba, wata tawagar alƙalai na kotun ɗaukaka ƙara a gundumar District of Columbia Circuit za su saurari ƙorafin rukuni uku na mutanen da suka shigar da ƙara kan sabuwar dokar.

Su ne: ByteDance da reshensa na Amurka, TikTok Inc; rukunin jama'ar da ke amfani da dandalin; da kuma wata ƙungiyar siyasa mai tsattsauran ra'ayi mai suna BASED da ke samar da bidiyo a TikTok.

Masu ƙorafin sun ce tun da dai dubban Amurkawa na wallafa bidiyo a TikTok, rufe shi zai zama saɓa wa haƙƙinsu da tsarin mulki ya ba su na 'yancin faɗin ra'ayi.

Shugaban dandalin na TikTok, Shou Zi Chew, ya faɗa wa masu amfani da dandalin: "Muna da ƙwarin gwiwa kuma za mu ci gaba da yaƙin kare 'yancinku a kotu. Hujjoji da tanadin tsarin mulki na ɓangarenmu...Ku sani cewa ba za mu je ko'ina ba."

'Yan Amurka da yawa na adawa da dokar da majalisa ta amince da ita wadda ka iya rufe TikTok

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,'Yan Amurka da yawa na adawa da dokar da majalisa ta amince da ita wadda ka iya rufe TikTok

Donald Trump ya yi yunƙurin toshe manhajar a 2020 lokacin da yake shugaban ƙasa.

Sai dai kuma yanzu ya buɗe shafi a dandalin har ma yana adawa da toshe shi. Ya goyi bayan maganar da ByteDance ke yi cewa toshe shi zai bai wa dandali kamar Facebook ƙarfin iko mai yawan gaske a kasuwar.

Kamfanin ya ce ba a China ake ajiye bayanan Amurkawan da ke amfani da shi ba, kuma ya haƙiƙance cewa ba za a turawa can ba. Ya ce yana gina rumbun ajiye bayanai a Texas musamman don ajiye bayanan Amurkawa.

Wane tasiri toshe TikTok a Amurka zai yi kan duniya baki ɗaya?

Dama an haramta amfani da TikTok a Indiya, da Nepal, da Afghanistan, da Somalia. Sannan an rufe sashen ƙasashen duniya na TikTok ɗin a China kanta.

Hukumar Tarayyar Turai ta faɗa wa ma'aikanta da kada su sauke manhajar a na'urorinsu na aiki, haka ma gwamnatin Birtaniya da majalisar ƙasar.

Idan Amurka ta rufe TikTok, ana tunanin sauran ƙawayenta za su bi sawu.

Hukumomin China sun garƙame manhajojin Amurka da yawa tsawon shekaru.