Rikicin siyasar Kaduna ya ɗauki sabon salo
.
Asalin hoton, Nasir El-Rufai
Wasu tsofaffin kwamishinonin tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i, sun zargi Majalisar Dokokin jihar da shaci fadi, cikin rahoton da ta fita na zargin tsohon gwamnan jihar da handame dukiyar al'umma.
Tsaffin kwamishinonin sun ce an yi hakan ne da gayya, kana aka ƙi ba su damar bayyana a gaban kwamitin da aka kafa domin gudanar da wannan bincike domin su fayyace komi, a maimakon hakan ma sai aka tsaurara ƙa'idojin da aka sanya.
Ɗaya daga cikinsu Já’afaru Sani, ya faɗawa BBC cewa wasu daga cikin basussukan da rohoton ya ce sun karɓo shifcin gizo ne, ba a karɓa ba, kuma basu shiga asusun gwamnatin jihar Kaduna a zamanin mai gidan na su ba.
Ya ce "Basussuka da ake magana mun karɓo na kasashen waje mun ga kusan guda biyar, a ciki akwai na dala miliyan 280 don gina hanyoyi a karkara, bamu karɓi wannan ba, akwai kuma wani na dala miliyan150 na aikin gona a wani wuri na musamman, shima ko sisi ba a saka a asusun gwamnati ba'' Inji Jafaru Sani.
Har Ila yau, ya ce "Akwai wani bashi da kwamitin majalisar ya ambato na dala miliyan 130 da wata dala miliyan ɗari bakwai na mayar da yara da ke gararanba a tituna zuwa makaranta, sai wani na dala miliyan 20 da aka shirya amfani da su kan yadda za a farfaɗo da kiwon dabobi, dukkansu ba a ƙarbo su ba kuma babu ɗaya daga cikinsu da ya shiga asusun gwamnati"
Ya bayyana cewa jami'ar tsohuwar gwamnatin da ta gabata ba sa fargabar amsa gayyatar EFCC don ba da ba'asi.
BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin ɓangaren majalisar dokokin jihar ta Kaduna kan waɗannan zarge-zarge, sai dai wani daya daga cikin ƴan kwamitin da majalisar da ta kafa don gudanar da binciken ya ce za su mayar da martani a lokacin daya dace.
Makusantan tsohon gwamnan na ganin cewa gwamnatin jihar karkashin Uba Sani ce ke shirya wa tsohon gwamnan wannan gadar zare.
Wannan rikicin siyasar da ya kunno kai tsakanin tsohon gwamnan jihar ta Kaduna Nasir El-Rufai, da magajinsa Uba Sani dai, a iya cewa ya dauki wani sabon salo, a yayin da lamarin ke ci gaba da mamaye da'irar siyasar jihar.
Tun farko Majalisar Dokokin jihar ce ta bankado zarge zargen da ake yi wa tsohon gwamnan jihar na salwantar da wasu maƙuden kuɗi da yawansu ya kai Naira biliyan 420 a tsawon shekaru 8 da ya shafe yana mulki.
Kwatsam ranar Alhamis ɗin nan, sai aka ga masu zanga zanga da dama sun taru a wajen gidan gwamnatin jihar riƙe da alluna alamomi, wadanda ke ɗauke da rubuce-rubuce daban daban na neman gwamna Uba Sani ya gudanar da bincike tare da gurfanar da tsohon mai gidan na sa a gaban hukumomin yaki da rashawa, don ya girbi abun da suke zargin ya shuka.
Wasu allunan da suke dauke da su, cewa 'za mu mamaye dukkan hukumomin gamnati don korar duk waɗanda ake tuhuma a cikin rahoton'
Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ta shaida wa BBC cewa 'Muna rokon a kira El-Rufai, domin wadannan kudi ba kanana bane, muna son a ƙwato su a mana ayyukan da suka kamata'
Wani kuwa ya ce 'Gwamnatin da ta gabata, ta yi wani waje da kudaden al'umma, majalisa ta yi aikinta, yanzu ya rage wa gwamna shima ya yi nasa'
Itama wata mata da ta shiga zanga zangar nuna fushi da nuna damuwa kan zargin da ake yi wa tsohon gwamnan, ta ce 'Cin hakkin talakawa da yawa musamman na yan jihar Kaduna ya jefa mu cikin wahala'
Magoya bayan tsohon gwamnan a jihar na zargin da gayya aka shirya wannan zanga-zanga, domin kware masa baya, da kuma yarfen siyasa.
A ranar 30 ga atan Maris din, 2024, Gwamna Uba Sani ya bayyana a wani taro cewa jihar na fuskantar ɗimbin basuka, da ya ce sun gada daga gwamnatin da ta gabata, ta tsohon mai gidan na sa.
Ya ce sama da kashi 70 na kuɗaɗen da jihar ke samu na tafiya wajen biyan basussukan.