Select a date and time slot to book an Appointment
Date Of Appointment
Asalin hoton, Getty Images
Aikin Hajji na ɗaya daga cikin manyan muhimman batutuwa a musulunci, kasancewarsa ɗaya daga cikin shika-shikan addinin, ya kasance wajibi a kan duk mutumin da yake da dama a ƙalla sau ɗaya a rayuwarsa.
A kowace shekara a irin wannan lokaci, miliyoyin musulmi daga ko'ina a faɗin duniya kan taru a ƙasa mai tsari (Saudiyya) domin gudanar da aikin hajjin.
Sai dai a lokuta da dama, wasu mutanen da suek je ibadar ba sa komawa ƙasashensu da rai, wasu daga cikinsu kan gamu da ajalisu a lokacin ibadar sakamakon wasu dalilai da suka haɗa da turmutsitsi da hatsari ko rashin lafiya.
A wannan aikin Hajji na shekarar 2024 da muke ciki, kawo yanzu an samu rahoton mutuwar maniyyatan Najeriya biyu, da suka mutu a birnin Makka, kamar yadda hukumar alhazan ƙasar (NAHCON) ta bayyana.
Shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, ya fitar da wata sanarwa da a ciki ke jajantawa iayalan marigayan tare da addu'ar samaun rahama gare su.
To ya ake yi ga gawarwakin maniyyatan da suka mutu a lokacin aikin Haji, musamman 'yan wasu ƙasashe kamar Najeriya?
Ko mutuwa a lokacin aikin Hajji na da wata fa'ida a addinance?
A rayuwa, musamman ta al'ummar Afirka, mutane kan so binne 'yan uwansu da suka mutu a maƙabartun garuruwansu. A lokuta da dama idan mutanen da suka kai wani matakai a rayuwa suka mutu, 'yan uwnsu kan kashe maudan kuɗi domin mayar da gawarwakinsu zuwa garuruwansu na sali domin binne su a can.
"Amma ban taɓa ganin an mayar da gawar maniyyancin da ya mutu a Saudiyya ba," in ji Umar Haruna, malamin addinin musulunci a Najeriya.
"A taƙaice dai alfarma ce hutuwa a ƙasa mai tsarki. Duk da cewa 'yan uwan mamaci za su ji zafin mutuwar, to amma za su ji sauki idan suka tuna cewa ya mutu ne a ƙasa mai tsarki, kasancewar hakan ni'ima daga ubangiji.''
Kasancewar musulunci ya tanadi gaggauta binne gawar mutum da zarar ya mutu, kuma galibi hakan ba ya wuce sa'o'i 24 da rasuwar mutum.
"Don haka ba abu ne mai sauƙi ba a tsara yadda za a dawo da gawar maniyyacin da ya mutu a Saudiyya cikin kwana guda ba, don haka ake binne su a ƙasar'', in ji Malam Haruna.
Mallam Imam Nurudden, malamin addinin musulunci a Najeriya - wanda ya sha zuwa aikin Hajji - ya shaida wa BBC cewa akwai maƙabartu masu yawa da ake binne maniyyatan da suka mutu a lokacin aikin Hajji.
Wasu daga cikin fitattun maƙabartun sun haɗa da Jannat Al-Mala da ke Makkah, da Jannat Al-Baqi da ke Madinah, da Al-Adl da, Al-Haram Martyr da Al-Rabway da kuma maƙabartar Arafat da ke kusa da dutsen Arfa.
A lokacin aikin Hajjin shekarar 2015, fiye da maniyyata 2,000 ne suka mutu a lokacin wani turmutsitsi a Minna, a lokacin hukumomin Saudiyya sun ce sun tanadi maƙabartu shida domin binne gawarwakin mutanen da suka mutu a lokacin turmutsitsin.
Akwai wasu fitattun 'yan Najeriya da suka mutu a lokacin ciki har da Adeola Maurufudeen Adefolabi, tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Legas, da Farfesa Tijani El-Miskin na jami'ar Maiduguri da fitacciyar 'yar jaridar ƙasar Hajiya Bilkisu Yusuf.
Sulaiman Aliyu, wani likita a Asibitin Koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya shaida wa BBC matakan da ake bi kafin a binne maniyyacin da ya mutu a lokacin aikin Hajji.
Aliyu ya kasance cikin tawagogin likitocin Najeriya a lokutan aikin Hajji da dama da suka gabata.
Ya ce ya danganta da wurin da maniyyaci ya mutu. Maniyyaci kan mutu a asibiti, ko cikin ɗakunan shan magani da hukumar NAHCON ke tanadarwa aƙasa mai tsarki, ko kuma ya mutu a masaukinsa.
"Idan a asibiti ya mutu, hukumomin asibitin kan rubuta rahoton mutuwarsa domin aike wa hukumar alhazan Najeriya, daga nan sai NAHCON ɗin ta kira hukumar alhazai ta jihar da maniyyacin ya mutu domin sanar da ita labarain mutuwar, daga nan sai su aike da rahoton zuwa ga hukumomin tsaron Saudiyya da hukumar ma'aikatar lafiyar ƙasar da kuma gwamnatin ƙasar''.
"Ana yin haka ne domin tabbatar da an bi duk matakan da suka dace da kuma sanar da duka ɓangarorin da suka dace kafin fara jana'izar''.
Haka kuma, Imam Tajudeen ya ƙara da cewa babu wani bambanci kan yadda ake yin jana'izar da yadda musulmai ke yinta a ko'ina a duniya.
"Da farko za a wanke gawara yi wa gawar wanka, sannan a sanya masa likkafani, sanna a ɗauke shi zuwa maƙabarta daga nan sai a yi masa sallar janaza, sai kuma a binne shi," in ji shi.
We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!
Have a great day!
Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support