by MUHAMMAD AUWAL UMAR
July 11th 2024.

Ƙananan yara 12 sun mutu a hatsarin mota a Afirka ta Kudu

...

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Ƙananan yara 12 sun mutu a wani hatsarin motar ɗaukar ɗalibai a Afirka ta kudu, bayan motar ta yi karo da wata.

Direban motar ya mutu, yayin da aka garzaya asibiti da wasu ƙananan yaran bakwai.

Hotunan da aka ɗauka a wajen da lamarin ya faru sun nuna yadda motocin suka tarwatse, kuma hayaƙi ya turnuƙe wajen.

Hukumomi sun ce yaran sun ƙone ƙurmus, ta yadda ba a gane kowa a cikin su.

Hatsari ya faru ne a a yankin Merafong,mai nisan kilomita 70 daga birnin Johannesburg.

Har yanzu hukumomi ba su fitar da bayanan yaran da lamarin ya shafa ba.

Ƴan sanda sun ƙaddamar da bincike a kan abin da ya janyo hatsarin.

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
Search Website

Search

Explore

Categories

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support