Wace ce kungiyar Hezbollah a Lebanon, ko za ta gwabza yaki da Isra'ila?

Harin makamin roka da aka kai yankin Golan da Isra'ila ta mamaye, da ya hallaka yara da matasa 12, sannan Isra'ila ta zargi Hezbollah da kai wa, ya haddasa zaman ɗarɗar da fargabar ta yiwu yaki ya barke tsakanin ɓangarorin biyu.
Shi ne hari mafi muni da aka kai iyakar arewacin Isra'ila, cikin watanni 10 da aka dauka Isra'ila da Hezbollah na musayar kai wa juna hare-hare.
Wacece Hezbollah, kuma a ina Lebanon ta ke?
Ita dai kungiyar Hezbollah ta musulmai mabiya mazhabar Shi'a ce, tana da karfi sosai a fannin siyasa da ikon yawancin manyan sojin Lebanon.
A shekarar 1980 manyan masu karfin fada a ji na 'yan Shi'a a Iran suka kafa kungiyar, da nufin kalubalantar Isra'ila. A wancan lokacin sojojin Isra'ila sun mamaye kudancin Lebanon a lokacin yakin basasar kasar.
An dama da Hezbollah a lokacin zaben 1992, a nan ne ta zama babbar mai fada a ji a bangaren siyasa.
Dakarun kungiyar sun kai munanan hare-hare kan dakaruin Isra'ila da na Amurka. A lokacin da Isra'ila ta janye daga Lebanon, kungiyar Hezbollah ta yi amfani da wannan damar tare da cewa ita ce ta fatattake su.
Tun daga lokacin, Hezbollah ta tara dubban mayaka da kafa wani kataren wurin adana makamai masu linzami a kudancin Lebanon.
Kungiyar ta ci gaba da kalubalantar Isra'ila musamman a iyakar kasasshen biyu.
Kasashen yamma da Isra'ila da kungiyar kasashen larabawa da wasu daga ciki sun ayyana Hezbolla a matasayin ta 'yan ta'adda.
A shekarar 2006, cikakken yaki ya barke tsakain Isra'ila da Hezbollah, lokacin da Hezbollah ta kai mummunan samamaye a iyakar Isra'ila.
Sojojin Isra'ila sun mamaye kudancin Lebanon, lamarin da ya sa fargaba ga Hezbollah. Amma duk da hakan, sun yi nasara sakamakon kara yawan mayakan da suke da shi da kuma samun manyan makamai na zamani masu inganci.
Wane ne Hassan Nasrallah shugaban kungiyar Hezbollah?
Tun shekarar 1992 fitaccen malamin addinin musulunci mabiyin darikar Shi'a, Sheikh Hassan Nasrallah ke jagorantar kungiyar Hezbollah
Ya taka muhimmiyar rawa wajen sauya kungiyar zuwa ta siyasa, da inganta sojinta da mayaka.
Yana da alakar ta kusa da jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Hakan ya samo asali tun shekarar 1981, a lokacin da jagoran addinin musulunci na farko a Iran Ayatollah Ruhollah Khomeini, ya nada shi mukamin mataimaki na musamman a Lebanon.
Shekaru da dama ba a ga Nasrallah a bainar jama'a ba, watakila saboda fargabar Isra'ila na iya kashe shi.
Amma duk da hakan, suna da alaka mai karfi da Hezbollah, kuma yana gabatar da jawabi sau daya a kowanne mako.
Wane karfi dakarun Hezbollah ke da shi?
Hezbollah na daya daga cikin kungiyoyi masu karfin dakaru, dakarun da ba karkashin tsarin gwamnatocin duniya ba.
Kasar Iran ce ke daukar nauyin dukkan makamai da abubuwan bukatunsu.
Sheikh Hassan Nasrallah ya yi ikirarin, kungiyar Hezbollah na da mayaka 100,000, sai dai bincike mai zaman kan shi da aka gudanar ya nuna mayakan ba za su wuce 20,000 zuwa 50,000 ba.
Yawancin dakarun an ba su horo na musamman, kuma sun fafata a yakin basasar Syria.

Cibiyar bincike ta think tank, ta yi kiyasin Hezbollah ta harba makaman roka da masu linzami 130,000 zuwa Idra'ila.
Sai dai yawancinsu kanana da rashin inganci, sai dai bayanai sun nuna kungiyar tana da makaman kare sararin samaniya da kakkabo jirage da jirgin ruwa na kariya daga makamai masu linzami, da kuma za su iya kai hari har zuwa Isra'ila.
Wannan shi ne abu mafi daga hankali, idan aka kwatanta da abin da Hamas da ke zirin Gaza ke da shi.
Shin Hezbollah za ta fara yaki da Isra'ila?
A baya-bayan nan fada ya barke tsakaninsu ranar 8 ga watan Oktobar bara, kwana guda bayan Hamas ta kaddamar da hari kan Isra'ila, ita kuma Hezbollah ta harba makamai Isra'ila a matsayin goyon baya da karfafa gwiwa ga Falasdinawa.
Tun daga wannan lokacin, ta fara kaddamar da hare-haren makaman roka arewacin Isra'ila da wuraren da Isra'ilar ta mamaye a tuddan Golan, da harba tankokin yaki da makamai masu linzami da kai hari kan sojojin Isra'ilar ta amfani da jirage marassa matuka.
Rundunar sojin Isra'ila ta mayar da martani ta harba makamai masu linzami da na atilari, ita ma a wuraren da Hezbollah ke iko da su a Lebanon.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce harin ya tilastawa mutane 90,000 tsere wa muhallansu a Lebanon, sannan farar hula 100 da mayakan Hezbollah 100 hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai sukai ajali.
Can a Isra'ila kuma, jami'ai sun ce farar hula 60,000 ne suka fice daga gidajensu domin tsira, an kuma kashe wasu 33 ciki farar hula 10 ne sauran jami'an tsaro sakamakon harin da Hezbollah ta kai.
Duk da fadan da ake gwabzawa, masu sa ido na cewa har yanzu dukkan bangarorin na taka-tsan-tsan da kaucewa wuce makadi da rawa, domin fargabar abin da ka je ya zo idan yaki ya barke tsakaninsu.
Amma, fargabar ita ce idan aka ci gaba da kai hare-hare da kisan mutane lamarin ka iya kazancewa da za a gagara shawo kan matsalar.