by MUHAMMAD AUWAL UMAR
August 25th 2024.

✓ A garin Makka wata rana Sayyadina Rasulallah (S A W) ya jingina a jikin katangar gidan wata mata (Kafira) sai wannan mata ta leƙo ta tagar gidan ta ta faɗa ga Annabi Alaihissalam cewar ya kauce mata daga jikin gidan ta. Anan take Annabi yana tsaye sai mala'ika Jibrilu (AS) ya zo yace ya Rasulullah Allah ya ce ka bar mata gidan nata. Sai Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya amsa ya ƙyale mata gidan ta, ya tafi yana saurayin murmushin sa, shi dama kunsanshi da cikar alkunya baya fushi sai an taɓa Ubangijin sa (S A W). 
 Sai ya riƙe hannun sayyadina Abubakar yace da shi: Ya Abubakar yanzu da mamaki wannan matar ta Muslunta? 
 Sai Abubakar yace ya Rasulullah ta yaya matar da tace ka bar mata kofar gidan ta zata yi imani da kai? 

 Ana haka Annabi s a w yana zaune tare da Abubakar sai ga wannan mata ta taho da hanzari wurin da Annabi yake zaune ana tare ta tana faɗuwa tana cewa ku kaini wurin Annabi ayi mini iso gareshi. Sai Sayyadina Rasulallah ya dubi Abubakar yace shin ka gane wannan matar?. Sai yace eh ita ce wacce tace ka bar mata gidan ta.

 Sai wannan mata ta iso wurin Annabi s a w tace wallahi Allah Allah ne, kai kuma bawan Allah ne (na sallama nayi imani). Sai Annabi s a w yace da Abubakar ai lokacin da na jingina a jikin wannan katangar gidan nata sai naji daɗin jinginar, sai yace to ta ya Allah zai ƙona wanda yayi wani abu da naji daɗi. (Kuma gashi Allah ba ruwan sa da kafiri).
 Wannan jin daɗin da Annabi yayi a jikin katangar ta shine Allah ya nufe ta da yin imani domin itama Allah ya jiyar da ita daɗin rahmar sa saboda farantawa Annabi da tayi. Sallallahu alaihi Wasallam.

 Da wannan nake tunawa 'yan uwa masoya Annabi watan da Annabi ya sauka a irin sa yana kusanto mu, mu ƙara shiri domin neman farantuwar Annabi da hidma gare sa da nuna tsantsar soyayya. Allah ya horewa kowa abin yiwa Annabi hidima.

 Allah muna rokon ka bamu damar yin abinda Annabi zai yi farin ciki da mu.

Khamis Na Annabi
08026407773
              
((LA'UZRA SOCIAL MEDIA 🎥))

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support