by MUHAMMAD AUWAL UMAR
June 15th 2024.

Mutumin da ya yi aikin faɗaɗa Ka'aba ba tare da karɓar ko sisi ba

Masjid al- Haram

Asalin hoton, Getty Images

BBC HAUSA 

Bayanan hoto, Aikin faɗaɗa masallacin Ka'aba da aka yi a lokacin sarki Fahd shi ne mafi girma da aka gudanar cikin ƙarni 14.


Muhammad Kamal Ismail shi ne mutumin da ya aiwatar da ɗaya daga cikin ayyuka mafiya girma na faɗaɗa masallatan harami da ke ƙasar Saudiyya.

Ɗan asalin ƙasar Masar, an haife shi ne a shekarar 1908, kuma tsohon sarkin Saudiyya, marigayi Fahd ne ya zaɓe shi domin ya shugabanci faɗaɗa masallacin Ka'aba da ke Makka da kuma masallacin annabi da ke Madina.

An bayyana aikin a matsayin mafi girma da aka taɓa yi wa masallatan a tsawon ƙarni 14.

Duk da matsawa da Sarki Fahd da kuma kamfanin ayyukan gine-gine na Bin Laden suka yi na ganin an biya shi, Isma'il ya ƙi karɓar ko kwabo.

Ya ce: "Ta yaya zan karɓi kuɗi don na yi aikin gyaran masallatai masu tsarki. Me zan faɗa wa Allah ranar tashin ƙiyama?

Masjid an-Nabawi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ismail ya sadaukar da rayuwarsa gaba ɗaya wajen ibada

Iliminsa da aure

Isma'il ya kafa tarihin zama wanda ya kammala karatunsa da mafi ƙanƙantan shekaru kuma shi ne mutum mafi ƙanƙantar shekaru da ya shiga kwalejin harkar ƙere-ƙere ta Royal School of Engineering da ke ƙasar ta Masar.

Daga nan an tura shi zuwa ƙasashen Turai domin samun ƙarin ƙwarewa kan harkar zane-zane da suka shafi Musulunci.

Ya yi aure yana da shekara 44 da haihuwa, inda matarsa ta haifi ɗa namiji kafin rasuwarta.

Daga nan Mista Isma'il ya mayar da hankali kacokan wajen bauta wa Allah har zuwa lokacin da ya rasu yana mai shekara 100 a duniya.

Ya kuma yi ƙoƙarin ganin ya kauce wa kafafen yaɗa labaru.

Daɓen farin dutse

Isma'il shi ne mutumin da ya kawo shawarar fara amfani da fararen duwatsu wajen yin daɓe a masallacin Ka'aba domin rage yanayin zafi da ake samu a Saudiyya.

Fararen duwatsun, waɗanda ba kasafai ake samun su ba, an samo su ne a ƙasar Girka.

Duwatsun sun kasance masu ɗaukan ido kuma suna taimakawa wajen sanyaya gini.

Daga baya, Sarki Fahd ya buƙaci Isma'il ya yi amfani da irin waɗannan duwatsu wajen yin daɓen masallacin annabi da ke Madina.

Ka'aba ne masallaci mafi daraja a addinin Musulunci.

An gudanar da ayyukan faɗaɗa masallacin a tsawon tarihi domin ya iya ɗauke ƙarin yawan masu ibada da ke ziyartar masallacin domin aikin Hajji ko na Umara.

Bayan aikin faɗaɗa masallacin a lokacin sarki Fahd, girmansa ya ƙaru zuwa murabba'in mita 356,800 kuma zai iya ɗauke masu ibada 820,000 ranaku na yau da kullum, sannan yakan iya ɗauke mutane sama da miliyan ɗaya a lokacin aikin Hajji da kuma watan Ramadan.

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
Search Website

Search

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support