Ko YouTube zai iya mayar da Kannywood kan ganiyarta?

- Isiyaku Muhammed
- Digital Journalist
- Aiko rahoto dagaAbuja
Alamu sun fara nuna cewa harkokin fina-finan Hausa na Kannywood sun fara dawowa matuka gaya ganin yadda ake ta fitar da fina-finai sababbi, da kuma samun sababbin 'yan fim.
Ana ganin kila wannan cigaban ba zai rasa nasaba da yadda aka koma sanya fina-finai a YouTube ba, inda furodusoshi da dama suka dawo da karfinsu.
Harkar Kannywood ta shiga tsilla-tsilla ne tun bayan da satar fasaha ta gurgunta kasuwancin CD, inda ya kasance ana ta fitar da fina-finai, amma ba a samun riba.
Masana a harkar fina-finai sun ce duk masana’antar da kasuwancin fina-finanta ya durkuse, ita ma dole ta durkushe.
Musamman Kannywood wadda masu aiki a cikinta ne suke rike da ita.
Wannan ya sa masu ruwa da tsaki a harkar suka shiga nemo hanyoyin da za su inganta kasuwancin fina-finansu.
Nuna fim a sinima
Ana tsaka da haka ne a shekarar 2015 aka bude katafaren kantin Ado Bayero Mall a Kano.
A ciki aka bude sinima ta zamani. Haka kuma a shekarar 2021 an sake bude wata sinimar ta biyu a birnin na Kano.
Bude wadannan sinimomin ya faranta ran masu harkar fina-finan Hausa, inda suka yi tsammanin nesa ta zo kusa.
Sai dai ba a samu nasarar da ake bukata ba.
Binciken BBC ya gano cewa fim din da ya fi samar da kudi kamar yadda shafin Kannywood Box Office ya nuna, shi ne fim din Aisha.
Fim din na furodusa Abubakar Bashir Maishadda, ne inda aka samu kudin da suka ki har naira 5,641,000 a kansa.

Komawa YouTube
Sakamakon rashin nasarar da aka yi hasashe a sinima, sai aka fara komawa gidan jiya a harkar fina-finan Kannywood din.
Wannan ya sa masu shirya fina-finan suka fara tunanin hanyoyin da za su bi domin dawo da harkar cikin hayyacinta.
A daidai wannan lokacin ne fim din ‘Izzar so’ na Lawal Ahmed, wanda ake nunawa a tashar YouTube ya samu karbuwa.
Lawan Ahmed ya bude tasharsa ta YouTube ne a Janairun 2014, sannan an fara sanya fim din ‘Izzar so’ a Afirilun 2020.
Zuwa lokacin hada wannan labarin a watan nan na Agustan 2024, tashar tana da masu bibiyarta akalla miliyan 1 da dubu 200, inda aka dora bidiyo kimanin 370, sannan ta samu masu kallo 173,430,021.
Haka shi ma wani fim da aka yi wa lakabi da ‘A duniya’ wanda shi ma ake nunawa a YouTube, an bude tashar ne a 2018 kuma ta samu karbuwa.
An fara nuna ‘A duniya’ ne a Agustan 2020, sannan zuwa lokacin hada wannan labarin, tashar tana da masu bibiya dubu 580, an dora bidiyo guda 503, sannan ta samu masu kallo 60,410,292.
Nasarar wadannan fina-finan guda biyu ta sa manyan furodusoshi suka fara komawa YouTube domin dawo da harkar yim fim din kan kadaminta.
Sai dai har yanzu masu ruwa da tsaki suna ci gaba da tattauna yiwuwar amfani da YouTube domin mayar da harkar kan ganiya.
‘Akwai alheri a YouTube amma…’
Furodusa Abubakar Bashir Maishadda, ya bayyana wa BBC cewa lallai akwai alheri a YouTube.
Da BBC ta tambaye shi ko yana ganin kafar YouTube za ta iya dawo da harkar ganiya?
“Abin da yake faruwa shi ne duk abin da ya zo, karbarsa ake yi.
"Youtube ya zo, kuma Alhamdulillah, ya zo mana da alheri sosai saboda gaskiya ana samun kudi fiye da yadda kake tunani.
"Duk da wani lokacin karbuwar fim a YouTube na da wahala.
"Shi ya sa za ka ga idan fim ya karbu a Youtube an dade ana yinsa, saboda idan ka sake shi, ka dauko wani, ba dole ba ne ya karbu.
"Yanzu idan ka dauki fim irin su Labarina da Gidan Sarauta, kasuwanci ake yi mai kyau, kuma komai yana tafiya da kyau.”
Da aka tambaye shi yadda zai kwantanta samun riba a tsakanin sinima da Youtube, ya ce YouTube ya fi.
A game da shirin fuskantar gaba, musamman wajen dora fina-finansu a manhajojin kallon fina-finai na duniya.
A irin manhajojin, wato video-on-demand ko kuma VoD a takaice irin su Netflix ne ake samun makudan kudade.
“Abin da muke jira ke nan. Ni kaina na tura musu fim din Aisha, amma har yanzu ban samu kwakkwarar amsa ba.
"Babban aikin da ke gabanmu shi ne fahimtar da Netflix abun da muke yi. Ka san fim a Netflix ya fi daraja, amma za mu kai wajen.”

Harkokin Kannywood sun dawo sosai- Naziru Dan Hajiya
A nasa bangaren, furodusa Naziru Auwal, wanda aka fi sani da Dan Hajiya ya ce komawa YouTube ya zama tilas ne.
“Dama haka ya kamata, duk lokacin da sana’a ta yi shiru, sai aka ga wuri kaza ne mafita, sai a zuba jari a ci gaba da yi.
"Yanzu dai aikace-aikace a Masana’antar Kannywood sun dawo sosai Alhamdullillah.”
Da aka tambaye shi yaya harkokinta suke a yanzu da kuma lokacin CD, sai ya ce, “Gaskiya ba za a hada lokacin CD da yanzu ba.
"YouTube na bukatar ya zama kana da yadda za ka iya tallata fim din, shi kuwa CD akwai ‘yan kasuwa da suke da alaka da jihohi, har da ma irin su Nijar.
"Don haka da zarar babban dan kasuwa daya ya sayi fim dinka, ya san ina zai tura.”
Ya kara da cewa, “A bangaren riba ma YouTube na kokari sosai, saboda in dai fim dinka ya samu karbuwa, to za ka samu riba sosai.”
Sai dai ya ce duk da ribar da ake iya samu, “YouTbe ba zai iya wadatar da Kannywood ba, ai ko da muka dawo YouTube zamani ne ya dawo da mu.
"Amma yanzu mun kara wayewa. Idan yanzu kana da YouTube dole kana bukatar fara tunanin manhajojin nuna fim na duniya irin su Netflix.
"Amma idan kana son fina-finanka su shiga wadannan manhajojin, kana bukatar kudi sosai.
"Amma ina da yakinin zuwa badi, akwai fina-finanmu da za su shiga Netflix da dama.”

Abin da ake bukata domin dawo da Kannywood ganiyarta- Muhsin Ibrahim
Dokta Muhsin Ibrahim, malami a Jami'ar Cologne da ke Jamus, wanda ya wallafa littafin ‘Kannywood: Unveiling the overlooked Hausa industry’, ya ce “Kamar yadda muka sani babu kasuwar kaset, ta mutu, kuma ba na jin za ta dawo.
"Don haka dole ’yan Kannywood su nemi hanyar da za ta bulle musu. YouTube na daga cikin hanyoyin nan.
"Sai dai ba ita ce hanyar da ta fi ba. A yanzu babu laifi za ta dan samar musu da kudi, shi ma din sai idan ka yi sa’a kana da tasha mai karfi.
"Amma furodusoshi da daraktoci masu tasowa za su sha wahala kafin su iya mayar da kudinsu, ba ma a zancen riba.”
A game da abin da ya sa ba a samu nasara a sinima ba, ya ce: “Tarihi ya nuna mutane da yawa ba su karbi sinima ba da farkon zuwanta.
"Wasu kadan da suka karba kuma ana musu kallon mutanen banza.
"Shi ya sa har yanzu akwai wanda ba zai taba zuwa ba, kuma ba zai bar wani nasa ya je ba.
"Na biyu kuma talauci. Wani zai ga gwara ya sayi abinci da ya sayi tikitin kallon fim.
"To gaskiya wadannan dalilan ne suka sa sinima ke da wahalar bullewa ga masana’antar.
"Fim don ya kawo naira miliyan biyar ai kudin da za a ba wani jarumin ke nan watakila idan ka dauko dan Kudu.
"Sannan kuma ai miliyan biyar din rabawa za ku yi da masu sinimar, to me miliyan biyu da rabi za ta yi wa wanda watakila ya yi bajet din miliyan 50 ko kwatankwacin haka?”
Dakta Muhsin ya ce, “A takaice dai hanyar da za ta bulle wa Kannywood ita ce manhajojin sanya fina-finan da ake kira VoD.
"Hakan ma sun gwada da irin su Northflix da su Kallo.com da Haske.
"Amma duk da haka an samu matsala saboda wadanda suka shigo da su ‘yan kasuwa ne, kuma alaka mai kyau ta ki kulluwa tsakaninsu da ’yan fim.
"Sannan mu kanmu masu kallo muna da tsantsenin bayar da bayananmu na banki a manjojin domin a rika cire kudi daga bankinmu idan muna kallo.
"Shi ya sa yanzu haka da muke magana irin wadanann manhajojin kusan sun mutu.
"Su kuma manya irin su Netflix matsalar ita ce yawancin irin fina-finan da muke yi ba su kai ingancin da suke bukata ba.
"Idan ma an yi, kasancewar kamfanonin suna can Legas, sai yake yi wa mutanenmu wahalar kulla alakar kasuwanci da su, sai abin ya ci tura," in ji Muhsin.
A game da mafita kuwa, Muhsin cewa ya yi, “Ni a ganina mafita ita ce su dage su rika shirya fina-finai masu ingancin da za su karbu a manhajojin.
"YouTube din kuma su ci gaba da yi suna samun na abinci. YouTube din ma za a iya samun riba, amma sai ka kafu. Kamar irin su Aminu Saira da suke samun talla, bayan kudin YouTube din.”