'Abin da ya sa nake so ɗana ya mutu'

Nirmala Rana tana jinyar ɗanta Harish, a gidansu da ke Delhi

ASALIN HOTON,BBC/RANA FAMILY

Bayanan hoto,Harish ya faɗo ne daga bene na huɗu a lokacin yana karatu a sashen nazarin kimiyyar tsara gine-gine a Jami'ar Chandigarh a shekarar 2013.
  • Marubuci,Kirti Dubey
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari,BBC News Hindi
  • Aiko rahoto dagaDelhi

''Waye zai so dansa ya mutu?" inji Nirmala Rana mai shekara 60 a lokacin da take zaune a kusa da ɗanta Harish mai shekara 30.

A shekarar 2013 ce Haris wanda a lokacin yake karatu a sashen nazarin kimiyyar tsara gine-gine ya faɗo daga bene na huɗu na Jami'ar Chandigarh da ke Arewacin Indiya, inda ya samu raunuka da dama a kansa.

Tun a lokacin ne yake kwance yana jinya, ba ya iya magana, ko kuma yin wani katabus na tsawon shekara 11- matakin da likitoci suka bayyana da "rai a hannun Allah.''

"Mun kai shi duk inda ya kamata mu je domin neman magani-asibitocin gwamnati da na kudi-amma ba a dace ba," in ji mahaifinsa, Ashok.

"Mun karanta, kuma mun sha jin labaran waraka da ake samu, amma mu dai mun yi addu'o'in, mun yi magani, amma ba mu dace ba."

Akwai agogon bango kafe a gefe ɗaya na ɗakin, da kuma kalandar watannin addini a ɗaya bangon. Duk da cewa agogon na tafiya, a wajen iyayen Haris, tun lokacin da ya faɗo daga benen duniya ta tsaya musu cak.

Marasa lafiya da suke rai a hannun Allah da ake magana a nan, ba a sume suke ba, amma ba su san komai da ke wakana ba, kuma ba su ma san wanda yake kansu ba saboda ƙwaƙwalwarsu ta samu matsala.

Da yammaci ne a lokacin, inda fuskar Nirmala ta nuna gajiya kasancewar ko karyawa ba ta yi ba. Ta kwashe sama da shekara 10 babu abin da take yi sai hidimar jinyar ɗanta-gyara masa shimfiɗa, canja masa kaya da sauran buƙatunsa na yau da kullum.

Haris, wanda ya kasance mai daga ƙarfe, yanzu ya koma ɗan ƙarami kamar wanda bai kai shekara 30 ba, fuskarsa da fatarsa duk sun tsuke ya zama kamar ƙwarangwal.

An sanya masa wani bututu ne da yake cin abinci da shi kai tsaye. Yanayin kwanciyarsa ma ta masa illa sosai, inda ta haifar masa da mikin da yake ƙara masa ciwo kan ciwo.

Yana kwance ne a kan gadonsa kawai, ba ya iya cewa komai sai kallon mutane yana ƙifta iɗo.

"Har na gaji da kuka na daina," inji mahaifiyarsa.

Nirmala Rana, mai shekara 60, da ɗanta Harish. Harish ya kasance a ƙwance rai a hannun Allah ne tun bayan da ya faɗo daga bene a 2013.

ASALIN HOTON,BBC/RANA FAMILY

Bayanan hoto,Ta wani bututu ne da aka saka ta cikinsa Harish yake cin abinci, kuma ba ya iya yin magana.

A bara dole iyayensa suka fara neman a samu likitoci su masa allular mutuwa cikin sauƙi domin ya huta, kasancewar daɗewar da yi yana jinya, sannan duk sun kashe kuɗadensu.

Euthanasia tsari da ke ba mutum damar yanke shawarar barin duniya domin hutawa da wahalar jinya ta hanyar allura ko shan wasu kwayoyi.

"Na gaji. Yanzu idan wani abu ya same ni, wa zai cigaba da kula da shi?" inji mahaifiyarsa.

"Muna so mu kyautar da wasu gabbansa-Gabban da ba za su masa amfani ba za su yi wa wasu amfani," inji ta, sannan ta ƙara da cewa, "za mu riƙa ganin mutanen tamkar ɗanmu ɗin, sannan shi ma ya huta da wahalar jinya."

Sai dai wata kotu a Delhi ta ƙi amincewa da buƙatar tasu.

Kotun cewa ta yi, "alamu sun nuna cewa mai jinyar yana cigaba da rayuwa ba tare da tallafin wasu injuna ba."

"Ke nan mai jinyar yana cigaba da rayuwa, don haka babu wanda ya ke da damar kashe wani ta hanyar ba shi wasu ƙwayoyi-ko da kuwa an yi haka ne domin a sauƙaƙa wa mara lafiyar wahalar jinya."

Abubuwa masu daure kai

A 2011, Kotun Ƙolin Indiya ta shiga tsaka mai wuya bayan ta ƙi amincewa da buƙatar wata nas mai suna Aruna Shanbaug wadda ta kwshe gomman shekaru tana kwance rai a hannun Allah bayan wani ma'aikacin asibiti ya kai mata hari a shekarar 1973, inda kotun ta ƙi amincewa da buƙatarta ta buqatar mutuwa.

Kotun ta yanke hukuncin cewa binciken da ta yi ya nuna mata cewa ƙwaƙwalwar Shabaut na aiki, don haka bai kamata ta mutu ba.

Haka Shanbaug ta cigaba da zama rai a hannun Allah har mutuwarta a shekarar 2015.

Amma wani hukunci da kotun ta yanke a shekarar 2011 ne ya buɗe wani sabon babi a game da matsayar doka a kan kashe kai saboda jinya.

A baya, babu irin ciwo da wahalar da za ta ba mutum damar mutuwa a Indiya, amma a wani hukunci da kotun ta yanke, ta ce, "idan ya kasance mara lafiyar ba ya iya cin abinci, za a iya lura da buƙatarsa.

A shekarar 2018, an samu wani cigaban, inda Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin cewa babu laifi a doka wanda yake rayuwa rai a hannun Allah na dindindin ya zaɓi mutuwa.

Sai dai an fayyace cewa dole mai buƙatar hakan ya tura buƙatarsa zuwa ga kotu, sannan ya haɗa da wasiƙar rantsuwa daga likita.

Matsalar ta sake dawowa ne a lokacin da maganar Harish Rana da bayyana, wanda iyayensa yanzu suke so su kai qara Kotun Ƙoli bayan ƙaramar kotu ta ƙi amincewa da buƙatarsu.

Duk da matsalar da suka fuskanta, iyayensa na da ƙwarin gwiwar cewa Kotun Ƙolin za ta amince da buƙatarsu.

Yanzu haka a Indiya, doka ta amince mai jinyar da yake rayuwa rai a hannun Allah, kuma yake rayuwa da wasu abubuwan da ba zai iya rayuwa ba sai da su ya yi amfani da wasu magunguna wajen mutuwa, amma har yanzu ba doka ba ta amince ba ya mutu ta hanyar shan magunguna ko allura.

"Kotun ta ce ai ba yana rayuwa ba ne tare da wasu abubuwan da ba zai iya rayuwa ba sai da su," inji lauya Manish Jain.

"Sai dai cin abinci ta bututu ai shi ma wani abu ne da yake tallafa rayuwa," inji shi.

"Yanzu Kotun Ƙoli za mu je domin ɗaukaka ƙara."

Wata rana a Agusta

A wani yammci ne na 5 ga Agustan 2013 lokacin da aka kira Ashok Rana ta waya, ake bayyana mata cewa ɗanta ya samu rauni.

Shekara goma ke nan, yanzu Harish ta bututu yake cin abinci da aka saka masa a ciki a wani aiki da aka masa da yake cin kuɗi har Rs 15,000 duk wata ($179) . Idan aka haɗa kuɗin da suke kashewa wajen jinyarsa a wata, yana cin tsakanin Rs 25,000 zuwa 30,000 ($357).

Domin samun kuɗaɗen jinyar, dole iyayensa suka sayar da gidansu da ke Delhi, suka koma wani ƙaramin gida mai ɗaki biyu a bayan gari.

Amma duk da haka suna fama da ƙalubalen cigaba da ɗaukar nauyin jinyarsa.

Fanshon Ashok Rana a wata na Rs 3,600 ba ya isa ɗaukar ɗawainiyar gida, ballantana a haɗa da kuɗin jinyar Harish. Domin ƙara samun wani kuɗin shiga, dole Ashok ya fara sayar da sandwiches da burgers a ranakun ƙarshen mako a wani filin wasan kiriket.

Idan har Kotun Ƙolin ta ƙi amincewa da buƙatarsu ta ba su damar mutuwar, iyayen sun ce suna so a mayar da shi asibitin gwamnati, sannan gwamnati ta cigaba d daukar ɗawainiyar jinyarsa.

Ashok Rana, mai shekara 63, yana shafa kan ɗansa cikin tausayi.

ASALIN HOTON,BBC/RANA FAMILY

Bayanan hoto,Mahaifin Harish, Ashok, yana shan fama wajen ɗawainiyar jinyar ɗansu, sannan yana fargabar halin da yaron zai shiga idan ya gaza.

Wasu ƙasashe irin su Switzerland da Spain da Australia da jihohi 11 a Amurka sun amince da dokar mutum ya iya mutuwa sabosa jinya da wahala.

Sai dai har yanzu kasashe da dama ba su amince da matakin ba.

Dokoki a Birtaniya daga misali, na hana mutane su yi amfani da magani domin mutuwa- duk da cewa akwai wani ƙuduri sabo game da batun da za a fara tattaunawa a Majalisar Scotland.

"Mutane sun yi amannar cewa Allah ne Yake ba da rayuwa, don haka Shi kaɗai Yake da haƙƙin kashewa ta yadda Ya so," inji RR Kishore wanda likita ne kuma mai rajin kare hakkin ɗan Adam wanda kuma lauya ne a Kotun Ƙoli, kuma Shugaban Ƙungiyar bibiya ta Indian Society for Health and Law Ethics.

"A irin wannan yanayin akwai abubuwa masu ɗaure kai. Don mutum yana kwance rai a hannun Allah a yau, wataƙila ya samu sauƙi gobe.

"Amma idan muka kashe mutum, ai mun yanke duk wata dama da yake da ita ta warkewa.

"Misali a batun Harish, zai fi kyau a samu ƙwararrun likitoci da suka haɗa da masana ƙwaƙwalwa da likitan jiki da sauransu, su haɗu su duba shi, sannan su tantance ko lokaci ya yi da za a cire masa abubuwan da suke taimaka masa na rayuwa.

"Babban abin lura shi ne kotu kaɗai ba ta ikon yanke hukunci kai tsaye."

A da Nirmala Rana kullum tunaninta shi ne sauraron ranar da ɗanta zai warke, amma yadda kwanaki suka tafi, kwanci-tashi har ya kai shekaru, "Na tuna lokacin da yake zuwa yana atisaye a gida, sai ya zo ya ce in gwada masa yanayin qarfin jikinsa," inji mahaifiyar.

Yanzu ta cire tsammani, kawai jiran ranar mutuwarsa take yi.