by MUHAMMAD AUWAL UMAR
July 13th 2024.

An kashe mutane aƙalla 71 a harin sama da Isra'ila ta kai Gaza

Gaza

ASALIN HOTON,REUTERS

Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce Falasɗinawa aƙalla 71 aka kashe, wasu da dama kuma suka jikkata a wani hari da aka kai birnin Khan Younis da ke kudancin Gaza.

Yankin Mawasi mai cinkoson mutane ya kasance daga cikin yankunan da a baya Isra'ila ta ce yana da tabbacinn tsaro, inda fararen hula ke neman mafaka a can.

Mutanen yankin sun ce a baya an umarce su da komawa wajen saboda tabbacin tsaron sa, amma sai gashi an jefa masu bam.

Sun kamanta munin harin da girgizar ƙasa.

Rahotanni sun ce likitoci a wani asibiti da ke kusa suna fafutukar ganin sun tallafawa waɗanda lamarin ya shafa.

Majiya daga sojin Isra'ila ta ce harin ya yi gagarumar nasara.

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
Search Website

Search

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support