Lalurar da ke sa a haifi mutum da kayan ciki a baibai

- Amitabha Bhattasali
- BBC News Bangla
Lokacin da Monarani Das daga Bangladesh ta fara jin zafi a bangaren dama na kirjinta a ƴan shekarun baya, ƴan'uwanta sun ɗauka cewa tana fama ne da matsalar tsamin ciki ko zafin ƙirji.
To amma ashe ba su sani ba ƴar'uwar tasu mai shekara 52 tana da wani yanayi ne na daban a halittarta, wanda zai kai ta har ƙasar Indiya domin neman magani.
A wata hira da BBC, Ms Das ta bayyana yadda ta fara jin alamar rashin lafiyar tata.
Ta ce, ''A wasu ranakun idan ciwon ya fara a ɓangaren dama na ƙirjina, nakan sha wahala wajen yin numfashi.”
Daga nan zuwa wani ɗan lokaci sai ta gamu da cutar bugun zuciya. A lokacin da ake yi mata magani ne na wannan bugun zuciya, sai likitoci suka gano cewa akwai alamun wani abu na daban da zuciyarta.
“Ta ce, likitoci a garinmu sun gano cewa zuciyata tana ɓangaren dama ne na ƙirjina.''
Bayan matsalar ɓangaren da zuciyar tata take, akwai kuma wani abin na daban da aka gano, inda wasu muhimman ɓangarorin zuciyar suna kallon baya ne maimakon gaba - inda ya kamata su kasance.
Ƙodarta da huhunta da matatar jininta da kuma tumbinta suna wani ɓangare na daban saɓanin yadda aka san halittar mutum.
Bincike ya nuna cewa ana samun irin wannan bambanci na halitta ne a kan jariri ɗaya cikin jarirai 12,000 da ake haihuwa.

Bayan da ƴan'uwan Ms Das suka ga tana fama da ƴan matsaloli na lafiyarta sai suka yanke shawarar tuntuɓar ƙwararren likitan zuciya a birnin Kolkata da ke gabashin Indiya.
Ƴan ƙasar Bangladesh da dama na ganin asibitocin Indiya sun fi aiki a kan na kasarsu. Saboda haka aka kai Das can.
Dr Siddharth Mukherjee na asibitin Manipal Hospital Broadway, ne ya yi mata aiki a watan Mayu na wannan shekara.
''Yi wa masu irin wannan larura tiyata abu ne mai wuya sosai,'' in ji Dr Mukherjee,'' saboda yawancinmu masu amfani da hannuwanmu na dama ne inda muke tsayuwa a bangaren dama na maras lafiya mu yi masa aiki.
''To a wannan yanayin sai dai mu tsaya a hannun hagu na maras lafiyar da za mu yi wa tiyata, wanda hakan kusan wani sabon abu ne, to amma ma'aikatanmu sun yi kokari suka iya sauyawa,'' in ji likitan.
Yanzu dai an yi mata aiki, kuma aikin ya yi kyau, Ms Das ta koma kasarta Bangladesh, amma za ta dawo nan gaba domin a sake duba ta.
Sauya wa zuciya mazauni
An sake samun wata matsalar ta daban a India, inda a wannan karon aka samu wani mutum a kasar wanda aka haife shi zucuyarsa na kallon bangaren hagu, to amma kuma ta sauya wajen da take daboda yawan tari da yake yi.
Tun da ya taso Reza-ul Karim, mai shekara 66, wanda ke zaune a jihar West Bengal, yake fama da matsalar numfashi sosai.
Ya ce: '' Daga baya na shiga siyasa kusan tsawon shekara 25, saboda haka na rika yawo zuwa wurare daban-daban. Nakan je wajen likita a garinmu wanda yake ba ni maganin da nake sha a kai-a kai
To amma a 'yan shekarun da suka gabata Mista Karim ya ce ya fara jin rauni da rashin kuzari, wanda hakan ya sa 'yarsa ta garzaya da shi zuwa asibitin Medica Super Speciality a Kolkata.

“Numfashina yakan dauke na yi ta fama don na tashi tsaye idan ina sallah,'' in ji Mista Karim ,” ya kara da cewa, ''na taba suma wajen sau biyu ko sau uku a lokacin da nake sallah.”
Likitoci sun gano cewa zuciyarsa ta koma bangaren dama na kirjinsa bayan da ya kamu da cutar tarin fuka yana yaro .
Liktocin sun ce yana bukatar a sanya masa wata 'yar karamar na'ura da za ta taimaka wa zuciyarsa aiki.
A watan Yuni likitoci suka ce ba makawa dole ne a yi masa tiyata nan take.
Bayan tiyatar sa'a uku ta sanya masa wannan na'ura ne aka gaya wa iyalansa yadda wannan matsala tasa take daban.

Dr Dilip Kumar, wanda ya yi masa tiyatar ya ce wannan aikin ya sha bamban da wnda suka saba yi saboda galibi ita wnnan na'ura ana sanya wa masu zuciya a bangaren hagu ne, to amma tashi a bangaren dama take.
Yanzu dai an yi wa Mista Karim aiki, ba tare da wata matsala ba, kuma nan gaba kadan za a duba aikin a ga yadda yake murmurewa.
Likitansa ya ce yanzu ba shi da matsalar numfashi kuma zai iya ci gab da sallarsa ba tare da numfashinsa na daukewa ba.