Wasan mari da gayyatar sojojin China zuwa Ivory Coast cikin hotunan Afirka

Zaɓaɓɓun ƙayatattun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya

Dan wasan kokawa na atisaye ranar Lahadi 4 Agusta 2024.

ASALIN HOTON,JAMES OATWAY / REUTERS

Bayanan hoto,Dan wasan kokawana yin atisaye a dandamali a ranar Lahadi, a shirye-shiryen fara gasar wasan mari a garin Kagiso, a yammacin birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu...
Dan wasa ya shirya shan mari, a lokacin wasan a garin Kagiso

ASALIN HOTON,JAMES OATWAY / REUTERS

Bayanan hoto,A lokacin wasan Marin, an sake bai wa dan wasa dama idan wanda aka mara ya ko da kifta ido ne...
'Yan kallo sun dauki hoto tare da egungun, ya sha kwalliya da kayan gargajiya na kabilar Yarbawa a Porto-Novo, Benin - Lahadi 4 Agusta 2024

ASALIN HOTON,YANICK FOLLY / AFP

Bayanan hoto,A ranar Lahadi a Porto-Novo babban birnin Benin, wani mutum ya yi kwallia da kayan gargajiya a lokacin wani bikin baje kolin al'adu...
Jerin gwanon masu shigar gargajiya ta Zangbe

ASALIN HOTON,YANICK FOLLY / AFP

Bayanan hoto,Gwamman mutane ne sukai jerin gwano, sanye da kayan gargajiya da takunkumin rufe fuska, nau'i daban-daban a bikin gargajiya na ta takunkumi a wato Porto-Novo Mask Festival a turance.
Maza biyu na ciyar da maguna, a ranar Talata 6 Agusta 2024

ASALIN HOTON,GERALD ANDERSON / GETTY IMAGES

Bayanan hoto,A ranar Talata a birnin Nairobi na kasar Kenya, wadannan mazan na bai wawata mage da jariranta abinci, inda suke lallaba su saboda kulawa.
Daya daga cikin tawagar 'yan wasan ninkaya na kasar Masar, ranar Laraba 7 Agusta 2024

ASALIN HOTON,AMIN MOHAMMAD JAMALI / GETTY IMAGES

Bayanan hoto,Wanshekare, 'yar wasan ninkaya 'yar Masar kenan, ke baje kolin fasaharta a gasar wasannin guje-guke da tsalle-tsalle na. Tawagarsu ta nuna bajinta, sai dai dakyar suka kai mataki na goma a gasar da ake yi a birnin Faris na Faransa.
Soja na busa, ya yin da wasu ke kae-kade a Lilongwe na kasar Malawi,Juma'a 2 Agusta 2024

ASALIN HOTON,AMOS GUMULIRA / AFP

Bayanan hoto,Makadan baduja na sojojin Malawi, sun cika titin Lilongwe da kade-kade da bushe-bushe ranar Juma'a a wani bangare na shirye-shiryen zaben da za a gudanar a shekara mai zuwa.
Sojojin China na yin fareti a kasar Ivory Coast, ranar Laraba 7 Agusta 2024

ASALIN HOTON,SIA KAMBOU / AFP

Bayanan hoto,A ranar Laraba an gayyaci sojojin China zuwa Ivory Coast, domin bikin cikar kasar 64, inda suka gudanar da kayataccen fareti a wurin shakatawa na Grand- Bassam, nisan kilomita 42 babban birnin kasar, Abidjan.
Mawaki dan Iraqi, Kadim al-Sahir ke baje fasaharsa a kasar Tunisia ranar 3 Agusta 2024.

ASALIN HOTON,FETHI BELAID / AFP

Bayanan hoto,A ranar Lahadi, mawaki Kadim al-Sahir dan asalin kasar Iraqi, ya baje fasaharsa a wurin bikin kalankuwar mawaka na kasa da kasa, wato Festival of Carthag. An yi bikin a wajen birnin Tunis na kasar Tunusiya.
Jami'in gwamnati na ajiye furanni kan kabarin 'yan kasar Bostwana 7 da suka mutu a harin bam.  2 Agusta 2024.

ASALIN HOTON,MOISE KASEREKA / EPA

Bayanan hoto,Da jijjibin ranar Asabar, a garin Kibati na Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo, masu makoki sun ajiye furanni kan kaburburan wadanda harin bam ya hallaka ranar 15 ga Yuli....
Hoton mata na cike da alhini, da kuka a zaman makokin da aka yi a ranar  2 Agusta 2024.

ASALIN HOTON,MOISE KASEREKA / EPA

Bayanan hoto,Mata na ta rusa kuka a wurin zaman makokin.
Wani matashi na sakale falanken Fizza a birnin  Algiers ranar Litinin 5 Agusta 2024

ASALIN HOTON,BILLEL BENSALEM / GETTY IMAGES

Bayanan hoto,A ranar Litinin aka bude bikin baje kolin kayan kwalama na Fizza, kuma babban birnin kasar Algeria wato Algiers ne ya bude gasar, inda mutane 50 suka shiga da kuma za a zabi gwanaye uku daga cikinsu a karshen gasar.
Imane Khelif ta na naushin 'yar wasan damben Thailand Janjaem Suwannapheng  6 Agusta 2024.

ASALIN HOTON,AYTAC UNAL / GETTY IMAGES

Bayanan hoto,A ranar Talata, 'yar wasan dambe 'yar Algeria, Imane Khelif ta yi nasarar daukar lambar Zinare a gasar Olympic, inda ta doke abokiyar karawarta 'yar Thailand Janjaem Suwannapheng.
Masoyan 'yar wasan dambe Imane Khelif', a kauyensu Biban Mesbah ke murna lokacin da ta kai wasan karshe a gasar Olympic,  a birnin Faris-Talata 6 Agusta 2024

ASALIN HOTON,HAMZA ZAIT / GETTY IMAGES

Bayanan hoto,Can a kauyen Bibah Mesbah na Aljeriya kuwa, masoyan 'yar wasan damben sun taru domin kallon wasan, tare da murna lokacin da ta yi nasara.