✓ WAYE KAMAR KA NE?
Kai da idan an taɓa ka Allah da kansa yake zuwa ya rama maka tun kafin ka kai kukan ka, kuma yake rarrashin ka idan an ɓata maka rai. Wanene zai misaltu da kai ? Sallallahu alaika Wasallam.
Kai da Allah ya shafe kowanne addini yace addinin da kazo da shi (Muslunci) shine kaɗai ya sani addini kuma babu wani addini a wurin sa bayan naka. To a ta yaya wani zai kama da kai? Sallallahu alaika Wasallam.
Kai da naji Allah yana shelanta wa kowa yana cewa kar wanda ya bini sai yabi ka, ma'ana dai ba'a bin Allah direct sai an bi ta hannun ka. To wai ma ta wacce hanya bawa zai iya isa ga Allah idan bai zo gare ka ba? Sallallahu alaika Wasallam.
Kai da ko aikin hajji mutum zai yi dole sai yazo garin ka zai yi, kuma komai kuɗi da mulkin mutum dolen sa sai yayi tattaki yazo fadar ka sannan zai zama Alhaji. To kenan a tawanne fanni za'a samu daidai ko kama da kai? Sallallahu alaika Wasallam.
Kai da Annabawan ma dukkanin su yaran ka ne, Mala'iku ma fadawan ka ne, aljannu ma 'yan aikin ka ne, dabbobi tsuntsaye da ma tsirrai duk kaine shugaban su, kafatanin mutane duk ayarin ka ne. Dan Allah ta ina wani zai misali da kai?
Sallallahu alaihi Wasallam ❤️
Malam Annabi fa ya ɗayantu babu inda za'a iya kamanceceniya da shi.
Allah ya ƙara masa girman matsayi da dayan taka.
Khamis Na Annabi
((LA'UZRA SOCIAL MEDIA 🎥))