Mining: Sana’a ko son banza?

- Isiyaku Muhammed
- Digital Journalist
- Aiko rahoto dagaAbuja
A wani yanayi da za a iya kira da sabon salo musamman a Arewacin Najeriya, yanzu da zarar ka ga matasa, ko dai maza ko mata sun himmantu wajen latsa waya, a lokuta da dama ‘mining’ suke yi.
Wannan ya sa matasan, waɗanda suke kiran su da ƴan baiwa za ka ji suna batun ko dai ‘za ta fashe’ ko dai ‘ta fashe’ ko kuma ‘yaushe za ta fashe’ ko kuma ‘za a kai mu Dawanau,’ musamman idan ba a samu kuɗaɗen da aka yi hasashe ba.
Wannan ne yake haifar da zazzafar muhawara a tsakanin mutane, inda wasu suke ganin masu mining ɗin ai son banza kawai yake jan su, wasu kuma suke ganin ai sana’a ce.
Abin da ke jan hankalin matasa zuwa mining
Hamster na daya daga cikin kirifto da aka fi mainin din shi a duniya, inda aka yi kiyasin cewa akalla mutum miliyan 155,514,148 suke shiga manhajar a duk wata. Mai biye masa shi ne Dogs, sai kuma Bulum.
Akwai kuma Pi da aka yi shekaru ana yi, har yanzu bai shiga kasuwa ba.
Abdullahi Salihu Abubakar, wanda aka fi sani da Baban Sadik, masani ne kuma mai bincike a kan fasahar sadarwar zamani da tasirinsu ga al’umma a kasashen Afirka, musamman Najeriya.
A tattaunawarsa da BBC Hausa, ya ce matasa sun himmatu wajen gudanar da harkar kirifto a Najeriya, ba ma Arewacin ƙasar kawai ba.
Sai dai ya ce akwai bambancin tsakanin biyun, inda ya ce akwai masu gudanar da asalin kasuwancin kirifto kai tsaye; ta hanyar saya da sayarwa, da ajiya da dai sauran al'amuran da suka shafi wannan harka kai tsaye.
“Ɓangare na biyu kuma su ne masu "Mainin" - Wannan kalma dai, ta ɓangarenmu a nan Afrika da ƙasashen Latin Amurka da Gabashin Asiya, ta shahara ne amma ba a bisa asalin ma'ana ko haƙiƙaninta ba. Hasali ma dai, kalmar na nufin "Mobile mining" ne, wato tsarin amfani da wayar salula don haƙo ire-iren waɗannan kuɗaɗe.
“Ita kanta wannan kalmar gurɓatacciyar ma'ana take ɗauke da shi. Domin asalin tsarin haƙo kuɗaɗen kirifto bai taɓa yiwuwa ta hanyar wayar salula ba. Ana amfani ne da manyan kwamfutoci masu girman mizani da ƙarfin ƙwaƙwalwa wajen iya warware lissafin da ke sa a hako.”
A nasa ɓangaren, fitaccen ɗan kirifto da mining a Arewacin Najeriya, Sanusi Ɗanjuma Ali ya ce yanayin ƙasar ta samu kanta na taɓarɓarewar arzikin na cikin abubuwan da suke jan hankalin matasa.
“Canji ne Allah Ya kawo wa duniya, sai al’ummar duniya ba na Najeriya ba kadai suka karkata, musamman matasa a fadin duniya. A nan Najeriya kuma duba da halin da ake ciki na talauci ya taimaka wajen jawo hankalin matasa zuwa harkar. Mutane suna samun alheri, wanda shi ne ya jawo matasa.
Ya ƙara da cewa duka biyun ana samun alheri idan mutum ya fahimce shi. “Shi cyrpto na buƙatar jari, saɓanin mining wanda idan mutum na da babbar waya, zai iya shiga ya samu alheri.”
Kalmar mining
Baban Sadiq ya ce "mining" da matasa ke shagala da shi, hanya ce ta kasuwanci da ake amfani da ita yanzu idan wani kamfani na son fitar da wani sabon kuɗi kasuwa. Masu mining ta hanyar waya su ake kira "Community", wato ragowar ya-ku-bayi ke nan a tsarin zuba jarin kirifto.
“Tabbas matasanmu sun kifu ma wannan fanni ne saboda dalilai da dama. Mafi girma daga cikinsu shi ne ƙarancin aikin yi, da hanya mafi sauƙi na samun daloli da tsarin ke ɗauke da shi idan an yi ƙaddamar kuma mutum ya dace.”
Sai dai ya ƙara da cewa idan matashi ya koyi yadda ake gudanar da wannan harka ta hanyar ilmi, da jajircewa, tabbas tana iya zama sana'a, muddin zai jure riba da asarar da ke cikinta, kamar yadda kowane irin nau'in kasuwanci yake.
“Amma idan burin matashi shi ne kawai ya samu kuɗi yanzu-yanzu da zarar ta fashe, to, zai sha mamaki. Kana iya kashe lokaci, da cajin waya da data, a ƙarshe ba ka samu komai ba.”
Shin za a iya riƙar mining a matsayin sana'a?

Sanusi Ɗanjuma Ali ya ce, “ba son banza ba ne. Masu cewa son banza ne ba su fahimci inda duniya ta fuskanta ba.
Abu ne wanda ilimi da canjawar duniya ta ɓangaren kimiyya da fasaha ta kawo, kuma abu ne na ilimi wanda ba a shigarsa sai da ilimi musamman kirifto, don haka wanda yake irin wannan tunanin zamani ya bar shi a baya.”
Ya ƙara da cewa babu laifi mutum ya riƙi kirifto a matsayin sana’a, “saboda abu ne da ake buƙatar ilimi , sannan kullum mutum zai iya shiga ya yi amfani da iliminsa ya samu kuɗi. Ke nan idan mutum zai riƙa samun kuɗin da zai biya buƙatun yau da kullum, ai ya zama sana’a.
“Amma mining wanda ba a yi kullum, wato ba a samu da shi a kullum bai kamata ya zama sana’a ba. Mining yakan kai wata biyu ko uku, wani lokacin ma yakan kai har shekara. Ka ga ai mutum ba zai zauna yana jira ba.”
Shi ma Baban Sadiq ya ce matashi na iya ɗaukar kirifto da manufar kasuwanci muddin zai jure yawan bincike, da karatu, da neman bahasi, da kuma raba kafa wajen zuba jari a harkar. “Amma idan mining ta hanyar waya ce, ba zan ba matashi shawarar ya riƙi hakan a matsayin sana'a ba.
Ya ƙara da cewa ƙwarewa a fasahar blockchain shi ne abin da ya kamata matasa su mayar da hankali. “Tabbas na san kwasa-kwasai kan wannan fasaha suna da tsada. Amma mu sani, da kuɗi ake neman kuɗi.”
A nasa ɓangaren, Sanusi Ɗanjuma Ali cewa ya yi, “Idan mining ne, su cigaba da yi, amma kar su riƙe shi kaɗai a matsayin sana’a domin ba zai hana wata sana’ar ba. Amma ina ganin bai kamata a ce mutum na da babbar waya ba kuma a ce ba ya mining domin ana samun alheri sosai.”
A nasa vangaren, Muhammad Ashir Yahaya, wanda shi ma yake harkar mining ya ce ana samun matsala ne idan mutum ya sa ran samun maƙudan kuɗaɗe.
“Daga cikin mining da ni na yi, Notcoin ne ya samar da kuɗi mai kyau. Amma irin su Avacoin da Param da wasu, sun shammace mu. Misali Avacoin an yi hasashen samun dala 0.05, kimanin 75 kowane guda ɗaya, amma ya fito a kan dala 0.01 wato naira 1.5. Don haka ana dan samu, amma bai kamata mutum ya rike shi a matsayin sana’a ba. Na samu naira dubu 180 a Notcoin.”