by MUHAMMAD AUWAL UMAR
September 11th 2024.

Bbc hausa l Labaran Ambaliyar Ruwa NiMet ta yi gargaɗin samun tsawa da ruwan sama na tsawon kwana uku a Najeriya

Ruwan sama

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi hasashen samun tsawa da ruwan sama daga Laraba zuwa Juma'a a faɗin Najeriya.

A wata sanarwa kan yanayi da hukumar ta fitar ranra Talata, ta ce ana sa ran samun tsawa a wasu sassan jihohin Borno, Adamawa, Taraba, Yobe, Katsina, Sokoto da kuma Kaduna ranar Laraba.

NiMet ta ce za a kuma samu tsawa a wasu ɓangarorin jihohoin Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Kebbi da kuma Jigawa da rana da kuma yammaci.

"A arewa ta tsakiya, ana sa ran samun tsawa a Abuja, babban birnin ƙasar da Nasarawa da kuma jihar Neja a ranar Laraban," in ji NiMet.

Hukumar ta ƙara da cewa a yankin kudancin ƙasar ma za a fuskanci tsawa da ruwan sama a jihohin Oyo da Osun da Ekiti da Ogun da Ondo da Lagos da Edo da Delta da Cross River da kuma Akwa Ibom daga Laraba zuwa Juma'a.

Hukumar ta NiMet ta kuma ce za a samu iska mai ƙarfi kafin saukar ruwan saman a yankuna da dama, inda ta ja hankalin jama'a cewa su ɗauki matakan kariya da hukumomi suka fitar domin kare kansu.

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
Search Website

Search

Explore

Tags

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support