Katsewar intanet ta tsayar da al'amura cak a wasu sassan duniya
ASALIN HOTON,GETTY IMAGES
Bayanan hoto,An dakatar da tashin jirage a filayen jiragen sama da dama a faɗin duniya
Sa'a 1 da ta wuce
Manyan bankuna da wasu kafofin yaɗa labarai da manyan filayen jiragen sama na duniya sun fuskanci tsaiko sakamakon katsewar intanet a wasu yankunan duniya.
Lamarin - wanda aka fara fuskantarsa da safiyar ranar Juma'a - ya tsayar da al'amura cak a wasu sassan na duniya.
Batun na zuwa ne a daidai lokacin da babban kamfanin fasaha na Amurka Microsoft ya ce yana ''ɗaukar matakai'' bayan samun matsalar intanet.
Manyan filayen jiragen sama na duniya kamar na birnin Sydney a Australia da na Berlin a Jamus da sauran sassan duniya duka sun dakatar da tashi da saukar jiragen sama, sakamakon matsalar katsewar intanet ɗin.
Hukumomin filayen jiragen sama na duniya da kamfanonin jiragen sama sun fitar da jerin sanarwa da ke neman afuwa ga kwastomominsu dangane da tsaikon da matsalar za ta haifar musu.
Turai
Cikin wata sanarwa da hukumomin kula da filin jirgin saman Berlin na Jamus ya fitar a shafinsa na X, ya ce kwastomominsa za su samu tsaiko sakamakon matsalar katsewar sadarwar.
Haka ma a Sifaniya lamarin ya shafi duka filayen jiragen saman ƙasar.
Hukumar da ke kula da filayen jirgin sama a Sifaniya ta sanar da "matsalar kwamfuta" a duka filayen jirgin sama na ƙasar, kamar yadda kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito.
Kamfanin zirga-zirgar jirgin sama mafi girma a Turai, Ryanair, ya gargaɗi fasinjoji game da matsalar da aka samu, inda ya ce hakan zai iya shafar "dukkan jiragen da ke shirin tashi," kodayake dai bai fayyace abin da ya faru ba.
Birtaniya
Matsalar katsewar intanet ɗin ta kuma shafi kamfanonin hada-hadar hanayen jari na duniya da sufurin jiragen ƙasa, musamman a Birtaniya.
Manyan kamfanonin sufurin jiragen ƙasa na Birtaniya, Southern daThameslink d Gatwick Express da kuma Great Norther, sun wallafa sanarwa a shafukansu na sada zumunta game da matsalar.
Da safiyar yau ne, kafar yada labarai ta Sky News ta dakatar da shirye-shiryenta"
"Kafar ba ta samu damar gabatar da shirye-shiryenta kai tsaye ba, kamar yadda shugaban kamfanin ya bayyana.
Amurka
A Amurka manyan kamfanonin jiragen sama na Delta da American Airlines, sun fitar da sanarwar dakatar da tashin jiragensu a faɗin duniya.
Kamfanonin sun ce sun dakatar da duk wani jirgi bai tashi ba, sannan kuma sun ƙoƙari wajen ganin wadanda ke sama sun sauka ba tare da matsala ba.
'Yansanda a jihar Alaska na Amurka sun bayar da rahoton ɗaukewar sabis a wayoyyinsu na kiran gaggawa.
Cikin wani sako da 'yansandan suka wallafa a shafinsa na Facebook, sun ce lambar kiran gaggawa ta 911 ba ta aiki, sakamakon matsalar katsewar intanet a faɗin jihar.
Asiya
Matsalar ta kuma shafi yankin Asiya, inda filin jiragen saman Narita a Japan ya ce kamfanonin jiragen sama na JetStar, da Jeju Air da Qantas da HK Express da kuma Spring Japan sun fuskanci matsalar.
A Indiya, filin jirgin saman Delhi ya ce lamarin ya shafi wasu harkokin filin jirgin.
Me ya haifar da matsalar?
Kawo yanzu dai ba a san abin da ya haddasa wannan gagarumar matsalar ba.
To sai dai, kakakin ministan gida na Australia ya ce matsalar na da alaƙa da kamfanin tsaron intanet na duniya wato Crowdstrike.
Shugaban hukumar tsaron intanet na Australia ya bayyana matsalar ''Babbar matsalar sadarwa'', yana mai cewa kawo yanzu babu wasu bayanan da ke nuna cewa harin intanet ne.
BBC ta tuntuɓi kamfanin tsaron intanet ɗin na duniya, wato Crowdstrike, to sai dai har yanzu ba mu ji daga gare shi."
.