by MUHAMMAD AUWAL UMAR
July 18th 2024.

"Tinubu ya sanar da sabon albashi mafi ƙanƙanta ga maikatan Najeriya



ASALIN HOTON,PRESIDENCY NIGERIA

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da naira 70,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikatan gwamnatin ƙasar.

Tinubu ya sanar da sabon albashin ne a ganawarsa da wakilan ƙungiyoyin ƴan ƙwadago na ƙasar a ranar Alhamis.

Ministan yaɗa labaru na Najeriya, Mohammed Idris ya sanar da manema labaru cewa "ina farin cikin shaida muku cewa a yau (Alhamis) ƙungiyoyin ƴan ƙwadago na Najeriya da Gwamnatin Tarayya sun amince da wani ƙari a kan naira 62,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta.

Sabon albashin mafi ƙanƙanta da ake sa ran shugaban ƙasa zai gabatar wa Majalisar Dokokin Tarayya shi ne naira 70,000."

Wannan na zuwa ne bayan kwashe tsawon lokaci ana taƙaddama tsakanin ƴan ƙwadago da gwamnatin Najeriya game da sabon albashin mafi ƙanƙanta ga ma'aikata.

Ƙungiyar ƙwadago ta dage kan cewa wajibi ne gwamnatin ƙasar ta yi wa ma'aikata ƙarin albashi domin yin daidai da halin da ake ciki na rayuwa.

Tashin farashin kayan masarufi ya yi ƙamari a ƙasar mai yawan al'umma sama da miliyan 200.

Cire tallafin man fetur da shugaban ƙasar ya yi a ranar da ya karɓi mulki cikin watan Maris na shekara ta 2013, ya sanya farashin kayan masarufi ya nunnunka, lamarin da ya jefa al'ummar ƙasar cikin mummunan hali."
 

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
Search Website

Search

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support