Me kashe Sarkin Gobir ke nufi ga tsaron Najeriya?

A ranar Laraba al'umma sun kaɗu game da labarin kisan da ƴan bindiga suka yi wa Sarkin Gobir na Gatawa Isa Bawa, bayan kwashe makonni a hannun ƴan bindiga.
Lamarin na zuwa ne kimanin mako ɗaya bayan sakin wani bidiyo da ya riƙa yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna sarkin a hannun masu garkuwa da shi yana roƙon gwamnati da iyalansa su cece shi daga hannun ƴan bindiga.
Duk da cewa ƴan bindigar sun kwashe shekaru suna kashe-kashe a yankin na arewacin Najeriya, amma ba kasafai ake samun irin haka ba.
Sai dai sau da yawa bayan an gama jimami, lamarin sai ya kwanta sai kuma idan wani lamarin makamancin haka ya sake faruwa a gaba.
Gwamnatin Najeriya dai ta daɗe tana cewa tana bakin ƙoƙarinta wajen shawo kan matsalar ta ƴan fashin daji, to amma abin na ci gaba da addabar al'ummar jihohi da dama.
Su ma gwamnonin jihohin na iyakar bakin ƙoƙarinsu ta wani fannin.
Tuni gwamnatocin jihohin yankin irin su Katsina da Zamfara da ita kanta Sokoto suka ƙaddamar da rundunonin ƴan sa-kai na jihohi domin shawo kan matsalar, amma har yanzu babu jihar da aka kawar da matsalar baki ɗaya.
'Sarakuna na cikin hatsari'
A tattaunawarsa da BBC, shugaban kamfanin Beacon Consulting, mai nazari kan tsaro a yankin Sahel, Kabiru Adamu, ya ce wannan lamari ya ƙara fito da hatsarin da sarakunan yankin arewa ke ciki.
Ya ce, “Akwai daga cikin ɓangaren gwamnati waɗanda suke da fahimtar cewa daga cikin abubuwa da ƴan bindigar nan suke so har da kawar da sarakuna, dalilin da suke cewa haka kuwa shi ne cikin burinsu har da kafa tasu daular, kuma babu yadda za su tafa tasu daular ba tare da sun kawar da sarakunan ba."
Sai dai wani abu shi ne a baya, hukumomi sun sha sanar da cewa an gwano wasu masu sarautun gargajiya da hannu a matsalar tsaro ta ƴan fashin daji.
To amma Kabiru Adamu ya ce sarakunan na daga cikin mutane da suka fi fuskantar barazana a wannan yanayi na rashin tsaro.
“Babu shakka suna cikin hatsarin kuma muhimman abu ne su fahimci cewa suna cikin hatsarin su ƙara inganta irin tsaron da suke tare da su."
Wasu buƙatu baya ga kuɗi
Bayan yin garkuwa da sarkin Gobir na Gatawa, abin da mutane suka sani shi ne ƴan fashin dajin sun buƙaci a biya su kuɗi kafin a karɓo shi.
Kuma abin da mutane suka yi tunani shi ne ana ci gaba da ƙoƙari ne na tattara kuɗin da za a karɓo sarkin.
To sai dai Kabiru Adamu ya ce wannan ba ita ce babbar buƙatar da ƴan bindigar suka gabatar ba.
“Akwai bayanai da ke nuna cewa waɗanda suka kama shi ɗin sun so a yi musayar fursunoni, wato akwai ƴan'uwansu waɗanda bayani ke nuna cewa sun dawo daga aikin Hajji aka kama su, to cikin buƙatun da suka gabatar, sun ce dole ne a sakar musu ƴan uwansu," in ji Kabiru Adamu.
Bayanin Dakta Adamu ya nuna cewa rashin biya wa ƴan fashin buƙatunsu na yin musayar fursunoni ne ya sanya suka fusata suka kashe sarkin.
Ko a lokutan baya an sha zargin faruwar irin hakan, sai dai ba kasafai lamarin kan fito fili ba, musamman idan idan aka sace mutane masu yawa ko kuma ɗalibai.
Gaba kura...
Wani abin da ya ƙara fitowa fili bayan sace sarkin na Gobir shi ne yadda ƴan uwa kan shiga hali mai wuya a duk lokacin da aka yi garkuwa da wani nasu.
A cikin watan Afrilun 2022 ne Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da dokar da ta tanadi ɗaurin shekara 15 ga duk mutumin da aka kama da laifin biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane.
Majalisar ta ce yin dokar zai rage ta'azarar matsalar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da ta addabi ƙasar, sai dai mutane da dama sun yi shakkun hakan.
Shi ma Kabiru Adamu ya ce "Wannan abu ne mai sarƙaƙiya domin akwai dokar ƙasa da ƙasa wadda kusan ta hana hakan (biyan kuɗin fansa)."
“Tun da majalisa ta fito da batun cewa za ta hana, har ta zo ta hana batun bayar da kuɗin fansa muka kawo shawarar cewa idan har za a yi hakan, to ya zama duk lokacin da ta gaza, aka samu irin haka, to ya zama ƴan'uwan mamacin za su iya kai gwamnati ƙara domin haƙƙinta ne kuma haƙƙi ne wanda yake cikin kundin tsarin mulkin ƙasa amma ba ta yi ba.
Me mutane ke cewa kan kisan Sarkin Gobir?
Tuni dai mutane ke ci gaba nuna damuwa game da kisan na Sarkin Gobir, Isa Bawa, tare da yin bayani kan matakan da suka kamata a ɗauka.
Shugaban Najeriya ya yi tir da lamarin, sannan ya bayyana cewa za a ɗauki matakin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar al'umma.
Sanarwar ta ce: "Shugaba Bola Tinubu ya yi alla-wadai da abubuwan da suka faru waɗanda suka kai ga kisan Sarki Alhaji Isa Bawa.
Shi kuwa jagoran ƴan'adawa a Najeriya, Atiku Abubakar ya ja hankalin gwamnati ne wajen ganin ta mayar da hankali kan batun tsaro a ƙasar.
Ya ce: ''Yana da muhimmanci mu ƙara jaddada wa gwamnati cewa dole ne ta samar da tsaron rayukan jama'a ta yadda mutane ba za su rayu cikin fargabar fusknatar irin haka ba.''