Abin da ya kamata ku sani kan sabuwar Babbar mai Shari'a ta Najeriya

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya rantsar da Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin mai riƙon muƙamin Babbar Mai Shari'a ta ƙasar.
A yanzu Kekere-Ekun ta maye gurbin Mai shari’a Olukayode Ariwoola, wanda ya yi ritaya bayan ya kai shekara 70 a duniya.
Rantsarwar ta gudana ne yau (Juma'a 23, ga watan Agusta) a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
A cikin wannan mako ne Hukumar Kula da Harkokin Shari'a ta Najeriya (NJC) ta gabatar da sunanta ga shugaban na Najeriya domin amincewa tare da naɗa ta kan muƙamin.
A ranar Alhamis 22 ga watan Agustan 2024 ne Mai Shari'a Olukayode Ariwoola ya yi ritaya bayan cika shekara 70 da haihuwa, kamar yadda dokar aikin gwamnati ta Najeriya ta tanada.
Mai shari'a Ariwoola ya yi riƙe matsayin ne tun daga ranar 21 ga watan Satumban shekara ta 2022, zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
A ƙa'idar Kotun Ƙolin, babban alƙali mai biye da shi ne zai maye gurbinsa.
Yanzu haka akwai alƙalai 21 a Kotun Ƙolin.
Bayan wannan rantsarwa, Mai shari'a Kekere-Ekun ta zama mace ta biyu da ta zama Alƙaliyar Alƙalan Najeriya bayan Mai shari'a Aloma Mukhtar, wadda ta riƙe matsayin tsakanin Yulin 2012 zuwa Nuwamban 2014.
Haka kuma hukumar ta amince tare da miƙa sunan mutum 27 domin zama alƙalan manyan kotunan jihohi da kuma waɗanda za su zama Kadi na kotun shari'a ta Abuja zuwa ga gwamnnoni da kuma Shugaban Ƙasa."
Wace ce Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun?
Mai shari'a Kudirat Motonmori Olatokunbo Kekere-Ekun tana ɗaya daga cikin manyan mata alƙalai na Kotun Ƙolin Najeriya.
An haife ta ne a ranar 7 ga Mayun 1958. Yanzu tana da shekara 66 ke nan.
Mai shari'a Kekere-Ekun ta yi digirinta na farko a ɓangaren shari'a ne a Jami'ar Lagos, sannan ta zama ƙwararriyar lauya a 1981.
Ta yi digirinta na biyu a London School of Economic and Political Science a watan Nuwamban 1983.
Ta fara aiki ne a Jihar Legas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.
Ta zama babbar majistare a Jihar Legas a Disamban 1989.
Sannan ta zama babbar alƙaliyar Babbar Kotun Legas a Yulin 1996.
Ta taɓa zama Shugabar kotu ta musamman a kan sata da ƙananan makamai na shiyya ta biyu a Legas daga Nuwamban 1996 zuwa Mayun 1999.
Sannan a 22 ga Satumban 2004, sai ta koma Kotun Ɗaukaka Ƙara da aiki.
Daga nan ne ta koma Kotun Ƙoli da aiki a 8 ga Yunin 2013.
Bayan aikinta, tana sha'awar karatu, waƙoƙi, fasahar zamani da bayar da shawarwari.
Alƙalan Alkalan Najeriya na baya
Mai Shari'a Stafford Foster Sutton: 1955-1958
Mai Shari'a Adetokunbo Ademola: 1958-1972
Mai Shari'a Taslim Olawale Elias: 1972–1975
Mai Shari'aDarnley Arthur Alexander: 1975–1979
Mai Shari'a Atanda Fatai-Williams: 1979- 1983
Mai Shari'a George Sodeinde Sowemimo: 1983–1985
Mai Shari'a Ayo Gabriel lrikefe: 1985–1987
Mai Shari'a Muhammed Bello: 1987–1995
Mai Shari'a Muhammadu Lawal Uwais: 1995–2006
Mai Shari'a Salisu Modibo Alfa Belgore: 2006–2007
Mai Shari'a Idris Legbo Kutigi: 2007–2009
Mai Shari'a Aloysius Iyorgyer Katsina-Alu: 2009–2011
Mai Shari'a Dahiru Musdapher: 2011–2012
Mai Shari'a Aloma Mariam Mukhtar: 2012–2014
Mai Shari'a Mahmud Mohammed: 2014–2016
Mai Shari'a W. S. Nkanu Onnoghen: 2016- 2019
Mai Shari'a Ibrahim Tanko Muhammed: 2019-2022
Mai Shari'a Olukayode Ariwoola: 2022 - 2024
Majiya: National Judicial Council