Dalilai biyar da ke sa ma'aikatan Najeriya ƙaryar shekarun haihuwa

Batun ƙaryar shekarun haihuwa tsakanin ma'aikatan Najeriya shi ne ya zamo abin tattaunawa a ƙasar tun bayan da majalisar kula da harkokin shari'a ta Najeriya wato NJC ta bayar da shawarar yi wa wasu manyan alƙalai biyu ritaya saboda laifin yin ƙarya a shekarunsu na haihuwa.
Cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, National Judicial Council (NJC) ta ce ta gano Alƙalin Alƙalai na jihar Imo T. E. Chukwuemeka Chikeka, da shugaban kotunan shari'ar Musulunci na jihar Yobe Babagana Mahdi sun aikata laifi.
Haka nan majalisar ta ɗauki mataki kan wasu alƙalan da suka haɗa da na yin gargaɗi, da hana su albashi, da kuma saka musu ido bisa laifuka daban-daban da suka aikata.
Ana dai alaƙanta ƙaryar shekaru tsakanin ma'aikata a Najeriya da wasu dalilai manya guda biyar kamar haka:
Dalilai uku da ke sa ma'aikata rage shekaru
Kwamared Nasir Kabiru mamba a ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ya lissafa dalilai biyu da ya ce su ne ke sa ma'aikata yin ƙaryar shekarun haihuwa domin kwashe tsawon lokaci suna aiki.
- Rashin ingantaccen albashi da tsarin walwala bayan ritaya: Yawanci ma'aikatan da ke yin ƙaryar shekaru na yi ne saboda yadda albashin da suke karɓa ba ya isar su da har zai ba su damar ajiye wani abu da idan sun bar aiki za su mora. Sannan kuma babu wani ingantaccen tsari ga waɗanda suka yi ritaya, inda a wani lokacin ma har sai mutum ya rasu haƙƙoƙinsa na ritaya ba su fito ba.
- Tsoron talauci bayan barin aiki: Sakamakon rashin ingantaccen albashi da tsarin ritaya mai kyau ga ma'aikata, ya sa wasu ma'aikatan ke ƙaryar shekaru saboda tsoron talaucin da ka iya samun su bayan ritaya.
- Son zuciya: Wasu ma'aikatan kuma duk da wurin irin albashin da suke samu amma za ka ba su da wadatar zuci abin da ke sa su rage shekaru domin su daɗe suna cin moriya.
- Buƙatar son cimma wani mataki: A kan samu yanayin da ma’aikata a gwamnati ko kuma a wuraren aikin da ba na gwamnati ba kan rage shekarunsu domin daɗewa suna aiki da manufar cimma wani muƙami a rayuwarsu ta aiki.
- Ƙoƙarin dacewa da ƙa'idar wani aiki: A Najeriya akwai yanayin da masu ɗaukar aiki musamman a wuraren da ba na gwamnati ba kan sanya ƙa’ida dangane da shekarun da ake so ma’aikaci ka da ya wuce domin samun aikin. Wannan kuma na ɗaya daga cikin dalilan da ke sanya masu neman aikin su rage shekarunsu na haihiwa domin dacewa da wannan aiki.
Me doka ta ce kan ƙaryar shekaru a Najeriya?
Barrister Haruna Zakari wani lauya mai zaman kansa a Najeriya ya shaida wa BBC cewa ƙaryar shekaru walau ragewa ko kuma ƙarawa ta ci karo na tsarin dokar ma'aikatan Najeriya da ke kundin tsarin mulkin ƙasar.
" Yin rantsuwa domin sauya shekarun da ba na gaskiya ba Wannan ya ci karo da tanadi na 02908 saki layi na 1 da na 2 na dokar ma'aikata wato Public Service Rule ta 2021.
Kuma aikata hakan daga ma'aikaci yana cikin abin da ake kira rashin ɗa'a wanda kan iya jawo kama shi da gurfanar da shi a gaban kotu."In Barrister Haruna.
Sai dai kuma sashe na 477 na dokar laifuka ta Najeriya ta tanadi hukuncin zaman gidan kaso na shekaru bakwai tare da biyan tara