Me ya sa ƴan mata ke nacin mallakar wayar iPhone?

Wayar iphone

Asalin hoton,Getty Images

Bayanan hoto,iphone ta zama wayar zamani da 'yanmata da samari ke yayinta a faɗin duniya
  • Marubuci,Abdullahi Bello Diginza
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari,BBC New, Abuja

Mallakar wayar zamani ta iphone tsakanin 'yanmata ta zama wani abu da ake kokawa ko gasa tsakanin 'yan matan da ke ganin karansu ya kai tsaiko.

Wayar iphone - wadda kamfanin Apple ke ƙerawa - na da abubuwa masu jan hankalin mutane, kama da kyamarorinta da manhajojin gyarawa da tace bidiyo da hotuna.

Nau'in farko na wayar iphone da Apple ya fara ƙerawa shi ne, iphone 1 da aka fara fitarwa kasuwa ranar 29 ga watan Yunin 2007.

Kuma wayar kamfanin mafi ƙololuwa a yanzu ita ce iphone 16 da ta fito a watan Satumban 2024.

Sai dai akwai sauran wasu wayoyin da Apple ke ƙerawa waɗanda ba iphone ba, amma ba su kai iphone farin jini ba.

Sababbin abubuwan zamani da wayar ke da su, ya sa ta ƙara samun karɓuwa tsakanin masu amfani da wayoyin hannu.

Ganin yadda a yanzu amfani da shafukan sada zumunta ya zama ruwan dare musamman tsakanin samari da 'yan mata, sai wayar iphone ta ƙara samun karɓuwa tsakanin waɗannan rukunai na mutane.

Sakamakon yadda wayar ke da tsada ya sa ba kowa ne ke iya mallakarta ba, hakan ne ma ya sa ake yi wa masu wayar kallon wasu isassu daga cikin mutane.

Wannan dalilin ne ya sa wasu 'yan matan ke kokawar mallakar wayar watakila don ''kankaro'' wa kansu aji tsakanin takwarorinsu 'yan mata da kuma samari.

'Abin da ya sa nake son mallakarta'

Wayar iphone

Asalin hoton,Getty Images

BBC ta tattauna da wasu 'yan mata masu amfani da wayoyin iphone ɗin don jin ra'ayoyinsu game da wayar.

'Yan matan - waɗanda muka ɓoye sunayensu na gaskiya - sun bayyana irin adadin kuɗin da za su iya kashewa wajen mallakar wayar.

Mafi yawa daga cikinsu sun ce suna sha'awar iphone ne saboda tana kankaro musu aji a wajen samari da kuma takwarorinsu 'yan mata.

Hajara (ba sunanta na gaskiya ba) ta ce tana son mallakar iphone ne saboda nuna isa da girma tsakanin takwarorinta 'yanmata.

Ta ce ''ai yanzu budurwa indai mai ji da kanta ne 'yar gayu mai aji, to a ganki da iphone, duk gayunki indai ba ki mallaki wayar iphone ba, to ba ki kai ba''.

''Wayar ta zama tamkar wani abu na yayi, kamar tufafi ne idan ana yayinsa, kuma ba ka da shi, ake maka kallon ba ka isa ba, to haka ma wayar iphone ta zama'', in ji ta.

Hajara ta ƙara da cewa wannan ne ma dalilin da ya sa 'yanmata ke rububin mallakarta.

''Yanzu a duk lokacin da kamfanin Apple ya ƙaddamar da sabuwar wayar, za ka ga 'yanmata na rububin mallakarta, domin kada a bar su a baya, saboda yadda ake ɗauki wayar yanzu a matsayin abin burgewa'', kamar yadda ta yi ƙarin haske.

''Ni a ganina duk wanda bai da wayar iphone to gaskiya bai san daɗin waya ba''.

Ita kuwa

'Da iphone nake auna saurayi'

Sajida (ba sunanta na gaskiya ba) ta ce idan ma saurayi ya zo wajenta, ko ya tare da da nufin yin zance da ita, to wayarsa za ta fara dubawa domin ta auna matsayinsa ko ya kai ta kula shi, ko kuma bai kai ba.

Ta ƙara da cewa daga irin wayar da saurayi ke riƙewa za ta iya gane shi ɗin ajinta ne ko akasin haka.

''Ko dai ba iphone ba ce, ai akwai manyan wayoyin android, idan na lura ɗaya daga cikinsu ne to zan iya kula shi, saboda na san ajina ne'', in ji ta.

"Amma da zarar na ga wasu ƙananan android ne to lallai na san ba a ji na ba ne, kuma daga nan zan rabu da shi, domin ni ɗin lashi moni ce'', kamar yadda ta bayyana.'', in ji ta.

'Zan iya kashe miliyan 10 don mallakar iphone'

Wayar iphone

Asalin hoton,Getty Images

Laura (ba sunanta na gaskiya ba) ta ce matsawar tana da kuɗi to babu iyakancewa na abin da za ta kashe domin sayen wayar.

''Zan iya kashe naira miliyan 10 don sayen wayar'', kamar yadda ta bayyana wa BBC.

Laura ta ce za ta iya sayar da sarƙa da zoben gwal ɗinta domin mallakar wayar, kuma za ta iya roƙon iyayenta ko nawa ne domin ta mallaki wayar.

Ta ce tana son wayar ne saboda daɗin charting da take da shi.

'Ina riƙe da android ne saboda larura'

Ita kuwa Nana (ba sunanta na gaskiya ba) mai riƙe da wayar Android ta ce tana riƙe da wayar ne saboda ba ta da damar mallakar iphone, amma ko yanzu ta samu dama za ta mallaka.

''Ai ka son abin dama ce, ko yanzu dama ta zo min zan mallaka domin in shiga jerin 'yan mata masu aji da kima, a riƙa min kallon babbar yarinya'', in ji ta.

To amma ta ce tun da ba ta da hali sai ta haƙura ba za ta saka kanta cikin rigima ba, ko ta je ta yi wani abin kunya don kawai mallakar iphone.

'Wasu ma ɗage suke yi, ba su kai su mallaka ba'

Wayar iphone

Asalin hoton,Getty Images

A cewar Nana wasu daga cikin masu iphone ɗin ba su kai su mallaki wayar ba, suna ɗage ne domin ƙarya.

''Wallahi wasu ma iyayensu raka-ni-kashi suke riƙewa, amma sai ka ga suna riƙe da iphone suna ɗaga wa mutane kai, ko wa ya saya musu?'' kamar yadda ta yi tambaya.

Ta ƙara da cewa ''Wallahi wasu babu ƙarfin da za a saya mata iphone a gidansu, amma za ta je ta bi ta ''ɓarauniyar hanya'' domin ta mallaka, don dai kawai ta kai kanta inda Allah bai kaita ba.

Samari kuma fa?

Sai dai samarin da dama da BBC ta zanta da su sun ce 'yan matan masu wayoyin iphone ba su fiya ba su tsaro ba, saboda a cewarsu mafi yawan 'yan matan suna mallakar wayar ne domin nuna isa da ƙarya.

Mujahid (ba sunansa na gaskiya ba) ya ce abin da yake fara dubawa idan ya ga budurwa mai iphone shi ne yanayin suturar jikinta, domin ganin ko ta cancanci riƙe wayar.

''Abin da nake fara dubawa shi ne yanayin jikinta, akwai matan daga ganinsu za ka son cewa lallai akwai arziki a gidansu, ko babu, to daga nan zan gane a gidansu ta mallaka a ko a 'hanyar Abuja'', kamar yadda ya ce

Don haka ya ce shi a wajensa 'yan mata masu iphone ba sa ba shi wata fargaba ko tsoro.

Shi kuwa Junaid (ba sunansa na gaskiya ba) cewa ya yi shi ya ma fi jin daɗin kula 'yan mata masu iphone.

''Ai indai ma ba iphone kika riƙe ba, to ni ba zan kula ki ba, saboda a wajena ba ki kai munzalin 'yan matan da zan kula ba'', in ji shi.

A nasa ɓangare, Anas (wanda shi ma ba sunansa ne na gaskiya ba) ya ce budurwa mai iphone razana shi take yi.

''Budurwa mai iphone kwarjini take min, idan na ganta da wayar, sai in ji gabana na faɗuwa, ba zan iya tunkararta ba, saboda gani nake ta yi mini girma'', in ji shi.

Don haka ne ma ya yi kira ga 'yan matan masu iphone su riƙa kula mutane irinsa, saboda su samu damar yi musu magana.