Yadda rundunar ƴansandan duniya ke artabu da ƙungiyar Black Axe ta Najeriya

.

Asalin hoton,Interpol

Bayanan hoto,A cikin ayyukan Interpol har da kamen ƴan ƙungiyar Black Axe a ƙasar Switzerland
  • Marubuci,Charlie Northcott
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari,BBC Africa Eye

Ƴansanda a faɗin duniya sun haɗa hannu inda suka gudanar da wani samame domin daƙile ayyukan ɗaya daga cikin ƙungiyoyin masu aikata laifuka mafiya hatsari - wato Black Axe.

A lokacin gagarumin samamen da ƴansandan suka aiwatar wanda aka yi wa laƙabi da Operation Jackal III, jami'ai sun kai samame a ƙasashe 21 tsakanin watan Afrilu zuwa Yulin 2024.

Samamen wanda rundunar ƴansanda ta duniya 'Interpol' ta aiwatar, ya samu nasarar kama mutum 300 waɗanda ke da alaƙa da ƙungiyar ta Black Axe da wasu ƙungiyoyi masu alaƙa da ita.

Hukumar ƴansandan duniya ta Interpol ta bayyana lamarin a matsayin wata 'babbar illa' ga gungun masu aikata miyagun lafiuka na Najeriya, sai dai hukumar ta yi gargaɗin cewa har yanzu ƙungiyar na da matuƙar haɗari idan aka yi la'akari da yawan ƴan ƙungiyar a faɗin duniya da kuma ƙarfin da take da shi.

A ɗaya daga cikin irin wannan samame, hukumomi a Canada sun ce sun bankaɗo wani tsarin damfara mai alaƙa da ƙungiyar Black Axe na kuɗi sama da dala biliyan biyar (£3.8bn) a shekarar 2017.

"Suna da tsari sosai kuma sun iya shiri," in ji babban jami'in sashen yaƙi da laifukan kuɗi na rundunar Interpol, Tomonobu Kaya.

Wani rahoto na rundunar ƴansandan Interpol a shekarar 2022 ya ce "Black Axe da wasu ƙungiyoyi irin ta ne ke da alhakin akasarin laifukan da suka shafi kuɗi ta intanet da wasu manyan laifuka da aka tafka a doron ƙasa.

Mista Kaya ya ce ƴan ƙungiyar na amfani da fasahohin zamani da manhajoji da kuma kuɗaɗen kirifto wajen ayyukan damfara da suka kai na ɗumbin miliyoyin dalolin Amurka.

"Waɗannan masu aikata laifi, babu shakka suna amfani da sabbin fasahohin zamani... Akwai kamfanonin fasahar tura kuɗaɗe na zamani waɗanda ke taimakawa wajen sauƙaƙe safarar kuɗaɗe a faɗin duniya," in ji shi.

An daɗe ana tsara wannan samame na 'Operation Jackal III' wanda ya haifar da ƙwace dala miliyan uku na haramtattun kadarori da kuma rufe asusun bankuna sama da 700.

Da dama daga cikin ƴaƴan ƙungiyar Balack Axe mutane ne da suka kammala karatunsu na digiri, kuma ana shigar da su ƙungiyar ne a lokacin da suke karatu.

Balack Axe wata ƙungiyar asiri ce da take ayyukan safar miyagun abubuwa da harkar karuwanci da kuma kashe-kashe a faɗin duniya.

Damfarar mutane da satar kuɗi ta intanet ne babbar hanyar samun kuɗi na ƙungiyar.

An gudanar da ayyukan samame kan ƙungiyar da dama tun daga shekara ta 2022.

Gomman ƴaƴan ƙungiyar ne aka kama tare da ƙwace kwamfutocinsu da wayoyi a lokacin irin wannan samame.

Wannan ya sa rundunar Interpol ta tara bayanai da dama, waɗanda yanzu take bai wa jami'anta a ƙasashe 196 na duniya.

"Muna buƙatar tattara bayanai daga waɗannan ƙasashe domin samun cikakken bayani kan yadda suke gudanar da ayyukansu," in ji Mista Kaya.

Ƴansandan ƙasar Switzerland na bincike kan abubuwan da suka ƙwace a wuraren da suka kai samame

Asalin hoton,Interpol

Bayanan hoto,Ƴansandan ƙasar Switzerland na bincike kan abubuwan da suka ƙwace a wuraren da suka kai samame

Duk da kamen da ake yi a ƙasashe daban-daban, wasu masana na ganin cewa ba a yin ƙoƙarin da ya kamata wajen kawo ƙarshen irin waɗannan miyagun ayyuka a Yammacin Afirka.

"Ya kamata ne a mayar da hankali kan hana faruwar irin waɗannan laifuka a maimakon kama su bayan sun aikata laifin," in ji Dr Oluwole Ojewale, shugaban nazari kan lamarin tsaro a Yammacin Afirka.

Najeriya, ƙasar da ta fuskanci zanga-zangar adawa da ayyukan rashawa a kwanakin nan, na daga cikin ƙasashen Afirka mafiya ƙarfin tattalin arziƙi a Afirka, sai dai tana da mutane kimanin miliyan 87 waɗanda ke rayuwa cikin ƙangin talauci, in ji Bankin Duniya.

Kuma ita ce ƙasar da ƙungiyar Black Axe ta fi ɗaukar mambobi.

Interpol ta ce tana bayar da horo ga jami'an ƴansanda da sauran masu ruwa da tsaki a Najeriya. To amma zarge-zargen haɗin baki tsakanin ƴan ƙungiyar Black Axe da jami'an gwamnati ya zama babban ƙalubale.

"Ƴan siyasa ne ke samar wa waɗannan yaran," in ji Dr Ojewale. "Gazawar gwamnati a ƙasar ya jefa mutane cikin mawuyacin hali ta yadda yake da sauƙi su shiga cikin wannan ƙungiya (Black Axe)."

Duk da cewa jami'an Interpol da ke gudanar da irin wannan aiki na gudanar da shi a ƙasashe da dama na duniya, amma tushensu na a ƙasar Ireland ne.

Bayan wasu jerin samame da jami'an rundunar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta Ireland (GNECB) suka ƙaddamar a 2020, an samu nasarar kama wasu ƴan ƙungiyar ta Black Axe, lamarin da ya fara bankaɗo ayyukan ƙungiyar.

"Sun kasance suna ayyukansu cikin matuƙar sirri," in ji Michael Cryan, babban jami'i a rudunar tsaro ta GNECB.

Ya ƙara da cewa "kuɗaɗen da suka yi safara ta ƙasar Ireland ba ƙanana ba ne."

Wayoyin da ƴansanda suka ƙwace

Asalin hoton,Interpol

Bayanan hoto,Rundunar ƴansandan duniya ta Interpol ta fitar da hoton wasu wayoyin hannu da ta ƙwace lokacin wani samame a Afirka ta Kudu

Daga baya ƴansanda sun gano mutum 1,000 waɗanda ke da alaƙa da ƙungiyar Black Axe a ƙasar Ireland kuma sun samu nasarar kama ɗaruruwan mutane kan laifin damfara ta intanet.

"Yanzu ana yin fashin banki ne ta amfani da kwamfutar laptop - suna da ƙarewa sosai," in ji Cryan.

Ya yi ƙiyasin cewa kudi yuro miliyan 200 ($220m; £170m) ne aka sace ta intanet a ƙasar Ireland a cikin shekara biyar da ta gabata, kuma wannan bai fi kashi 20 cikin ɗari na laifukan damfarar kuɗi ta intanet da aka bayar da rahoto a kai ba.

"Wannan ba laifukan damfara da muka saba gani ba ne... Ya kamata shugabanni su san girman wannan matsala, in ji shi.

Wani bincike na ƴansandan ƙasar Ireland a 2023 ya bankaɗo cewa kuɗaɗen kirifto - waɗanda ake iya turawa cikin hanzari ta intanet a faɗin duniya - sun zamo wata babbar hanya da ƴan ƙungiyar Black Axe ke amfani da itya wajen safarar kuɗaɗe.

An karɓe kuɗaɗen kirifto da suka kai darajar yuro miliyan ɗaya a lokacin binciken.

Interpol ta yi amfani da tata fasahar wajen yaƙi da wannan matsala.

Ana yin wani ƙoƙari wajen ganin an yi musayar bayanan sirri kan ƙungiyar Black Axe da ƙungiyoyi makamantanta a Yammacin Afirka da faɗin duniya.

"Idan za mu iya tattara isassun bayanai, za mu magance wannan matsala," in ji Mista Kaya.