Gargaɗin MDD kan yadda tumbatsar tekuna za ta illata duniya

..

Asalin hoton,Getty Images

Bayanan hoto,Tsibiran Pacifik na fuskantar babban hatsarin tumbatsar teku

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres ya ce ko dai manyan ƙasashe da kamfanoni su rage fitar da abubuwa masu jawo gurɓacewar muhalli ko - ko kuma su jefa duniyar cikin bala'i.

"Yanzu tsibirin Pacifs ne ya fi fuskantar ƙalubale a duniya," kamar yadda ya shaida wa BBC a taron jagororin Tsibiran Pacific a Tonga. "Akwai rashin adalci babba dangane da tsibiran nan, wannan dalilin ne ya sa na zo."

"Ƙananan tsibirai ba su jawo sauyin yanayi, amma su ne suka fi fama da matsalar da take biyo baya."

Amma kuma, "tumbatsar tekunan na neman cinye mu baki ɗaya," inji shi a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron bayan MDD ta fitar da rahotanni guda biyu a game da tumbatsar tekuna da yadda hakan ke barazana ga ƙasashen yankin tsibirin Pacific.

Ƙungiyar Kula da Sauyin Yanayi na duniya ta ce sauyin yanayi a Kudu maso Yammacin Pacifc ta ce yankin na fuskantar ruɓanyawar hauhawar tashin tekunan sai uku, da hauhawar yanayin asid na tekunan da kuma ƙarin janye sinadarin carbon dioxide.

"Dalilan nan a bayyane suke:iskar gas da ake fitarwa-waɗanda yawanci kamfanoni suke fitarwa-suna neman dafa duniyarmu." inji Mista Guterres a jawabinsa.

Taken taron na bana-kawo sauyi da juriya- an gan shi a zahiri inda a ranar farko na taron, mamakon ruwa ya mamaye wajen taron.

A kusa da wajen taron kuma, mutanen yankin suna zanga-zanga ne, inda suka manya wata babbar banar da aka rubuta a jiki cewa, "Tekuna suna tumbatsa, mu ma muna tunbatsa." wata banar kuma aka rubuta cewa, "Ba ruwa ba ne zai ci mu, ƙwatar ƴanci muke yi."

Wannan ya nuna ƙalubalen da duniyar ke fuskanta, wanda zai iya cinye duniyar baki ɗaya.

..

Asalin hoton,Getty Images

Bayanan hoto,Antonio Guterres (a hagu) yana magana da Shugaban Majalisar Tonga Lord Fatafehi Fakafanua.

Kamar yadda rahoton ya nuna, tekunan sun hauhawa da aƙalla santimita 9.4cm (3.7in) a shekara 30 da suka gabata, amma a yankin Tsibirin Pacific kuwa, hauhawar ta kai santimita 15.

"Yana da muhimmanci da shugabanni, musamman irin su Austeliya da Aotearoa su zo su gane wa idonsu yadda abubuwa suke, sannan yadda mutanenmu suke jure wahalar da muke fuskanta," inji Mista Sikulu.

"Babbar ɗabi'ar mutumin Tonga shi ne ɓoye damuwa tare da cigaba da rayuwa cikin farin ciki duk rintsin da ake ciki. Wannan ne ya sa muke da juriya. Amma ina ganin yana da kyau a zo yadda mukerayuwa cikin hatsari."

Wannan ne karo na biyu da Sakataren Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya yake halartar taron na Tsibirin Pacific. Taron na shekara-shekara, jagorori ne daga tsibiran Pacific guda 18 da Austreliya da New Zealand suka taruwa domin tattauna muhimman abubuwa.

A daidai lokacin da ake gudanar da taron ne aka fara mamakon ruwan sama. Sannan jim kaɗan kuma aka yi girgizar ƙasa a yankin na Tonga, wanda hakan ya nuna wa mahalarta taron haɗarin da yankin ke ciki.

A 2029, Mista Guterres ya je Tuvalu, inda ya bayyana gargaɗin barazanar tumbatsar tekuna, yanzu shekara biyar ke nan da wancan taron, inda a cewarsa, ya fara ganin sauyi.

Mista Guterres ya koma ziyarci garuruwan da suke fuskantar barazana saboda hauhawar tekunan. Shekara bakwai ke nan suna jiran ganin yadda za a yi da su.

..

Asalin hoton,BBC/ Katy Watson

Bayanan hoto,Mutanen Tonga suna raye-raye domin bayyana buƙatarsu a daidai lokacin da ake gudanar da taron.

Yawancin mahalarta taron sun bayyana babbar ƙasar da ta fitar da fi fitar da abubuwan da suke jawo gurɓacewar muhalli- Austreliya.

Tun a farko wannan shekarar, Firaminista Anthony Albanese ya ce Austireliya za ta kara faɗaɗa tacewa da amfani da gas zuwa "2050 ko sama da haka" duk da kiraye-kirayen da ake yi ga kasar ta rage amfani da makashin.

"Akwai aiki babba a kan manyan ƙasashe da suka fi fitar da waɗannan abubuwa," inji Mista Guterres lokacin da BBC ta tambaye shi ko yana da wani saƙo zuwa ga ƙasashen irin su Austireliya.

Idan ba a yi abin da ya dace ba, duniyar za ta kai matakin tumbatsar tekuna na 1.5 da ba a so kai kamar yadda aka cimmawa a yarjejeniyar Paris ta 2015. An yi yarjejeniyar ce domin rage ɗumamar yanayi zuwa ja 2C.

"Idan muka iya rage ɗumamar yanayi zuwa tsakanin 1.5C ne za mu iya yaƙar durƙushewar Greenland da dusar ƙankarar Yammacin Antarctic, da kuma bala'in da zai iya biyo baya," inji Mista Guterres.

"Wannan na nufin rage fitar da abubuwan da suke jawo sauyin yanayi da kashi 43 a 2030 idan aka kwatanta da shekarar 2029, da kuma ƙarawa zuwa kashi 60 a shekarar 2035."

Amma a bara, maimakon raguwa, ƙaruwa aka samu da kashi 1.

"Wannan nauyi da ya rataya a kan ƙasashen G20 da kusan kashi 80 na abubuwan da suke jawo sauyin yanayin ke fitowa daga gare su. Ya kamata su zauna, su tattaunawa yadda za su iya rage faruwar hakan," inji Mista Guterres.