..
Bayanan hoto, Wasu randuna da ake amfani da su a garuruwan Hausawa

A garuruwan Hausa, akwai wata al’ada da ta samo asali tun shekaru aru-aru, inda a duk ranar Laraba ta ƙarshen a watan biyu wato Safar, ake alhini saboda fargabar da ake yi cewa rana ce mai tafe da masifa.

Ana siffanta ranar da cewa tana zuwa da masifu, wanda hakan ya sa a al’adar Bahaushe, ake gudanar da abubuwan neman kariya.

Saboda guje wa masifar da ake fargabar tana tattare da ranar, a zamanin an ce ko aure ko wani abu mai muhimmanci ba a cika so ana yi a ranar ba.

Abubuwan da ake yi ranar Larabgana

Ranar ta Larabgana, ana siffanta da ‘muguwar rana’ wadda ta fi kusa da haifar da masifa.

Hakan ne ya sa a gidajen Hausawa ba a barin abubuwa kamar randa ko tulu ko bokiti ko daro a buɗe ba tare da an rufe ko kife shi ba, a duk daren ranar Larabar ta ƙarshen watan Safar.

Kusan dai babu wani lokaci da masana suka bayar na fara wannan al'ada.

BBC ta tuntuɓi malami a sashen nazarin harsunan Najeriyana jami'ar Bayero da ke Kano, Dr Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible) a kan wannan ranar domin jin ta bakinsa.

“A al’adance, mata na haɗa ruwan rijiyoyi daban-daban guda biyu ko uku zuwa bakwai sai a sa gishiri ko toka sai a yi wanka a sha a matsayin maganin masifa.

“Kuma an ce ranar ‘Larabgana muguwar rana’. Suka ce komai aka yi dashe a ranar sai an kuma; ko daɗi ko wuya. Wato komai ya samu mutum idan alheri ne sai ya maimaita kansa, haka ma in sharri ne.”

Mahangar Musulunci

BBC ta tuntuɓi Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa domin jin ko akwai wani tanadin addinin Musulunci a game da ranar.

Babban malamin addinin Musuluncin ya ce babu ranar Larabgana da aka ware a Musulunci a watan Safar domin addu’o’in neman tsari ko bukukuwa.

Sai dai ya ce, “Akwai hadisin Manson Allah cewa akwai wata rana a shekara da bala’i yake sauka, idan ya sauka ba zai bar tukunya a buɗe ba sai ya shiga ciki ko wani abu buɗaɗɗe sai wannan bala’in ya shiga ciki.

Don haka ku riƙa ku kife ƙoranku da tukwananku da randunanku. Amma bai ayyana wace rana ba ko wata ba.”

A game da ko akwai laifi, malamin ya ce, “ba za a ce sun yi laifi ba, amma tunda Manzon Allah bai ce ga rana kaza ba, bai kamata wani malami ya ce ranar kaza ce ba. Idan ma akwai laifin zai koma kan wanda ya ce rana kaza ce idan ba yana da dalili ba musamman idan aka jingina da Musulunci,” inji Sheikh Daurawa.

Sai dai ya ce idan ana yi ne da sunan al’ada ko gargajiya ko wani ilimi daban, “to ka ga ke nan zai zama biki ne na al’ada kamar yadda ake da wasu bukukuwa na al’ada.”