..

Asalin hoton, Getty Images

Yayin da al'ummar Najeriya ke ci gaba da kokawa dangane da halin matsin tattalin arziƙi irinsa na farko da suka ce suna fuskanta sakamakon waɗansu tsare-tsare da gwamnatin Shugaba Tinubu ke ɗauka, masana tattalin arziƙi na cewa akwai dabarun jure wa yanayin.

Dakta Lawal Habib Yahaya, malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano kuma masanin tattalin arziƙi ya lissafa wasu hanyoyi guda hudu da ya ce idan yan najeriya suka rungume su to za su samu sauƙi a rayuwarsu.

Haƙuri

Dakta Lawal ya ce mataki na farko na samun zaman lafiya a lokacin tsananin tattalin arziƙi shi ne haƙuri da yanayin da mutum ya samu kansa.

"Yawanci mutane kan shiga damuwa har su samu ciwon da zai kai ga ajalinsu sakamakon tunani da suke yi na cewa a baya ina iya yin kaza amma yanzu ba zan iya ba.

Abin da ya kamata mutum ya sa a ransa shi ne ya sanya ƙaddara a ransa ya amince cewa wata jarrabawa ce daga ubangiji." In ji Dakta Lawal.

Masanin ya ƙara da cewa duk da cewa abu ne mai tayar da hankali "to amma idan abu ya fi ƙarfinka yaya za ka yi? Dole ka fito da hanyar danne abin ba tare da ya yi sanadin ranka ba."

Fata/ƙudiri

Masanin ya ƙara da cewa abu na biyu shi ne samun fata ko kuma ƙudiri ta yadda "mutum zai ƙarfafa zuciyarsa da fatan cewa zai shiga a dama da shi wajen fafutukar nema har zuwa lokacin da yanayin zai wuce."

"Harwayau fata na nufin sanya wa a rai cewa yanayin da ake ciki na wucin gadi ne wato wata rana sai labari. Idan ka samu haƙuri ka haɗa da fata ko kuma ƙuduri to mutum zai kamo bakin zaren." In ji Dakta Lawal Habib.

Rage buri

..

Asalin hoton, Getty Images

Dakta Lawal ya ce bayan samun hakuri da ƙudiri abu na gaba shi ne rage buri kan abubuwan da a baya mutum yake iya yi.

"Yanzu dole ne mutum ya mayar da hankali kan abubuwan da suka zama wajibi a rayuwa sannan ya haƙura da waɗanda ba dole ba ne. Misali a baya gidanka ana cin shinkafa ƴar waje to a wannan lokaci sai ka koma ƴar gida. Ko kuma ka saba cin shinkafa to yanzu sai a haɗa da dambu da sauransu.' In ji Dakta Lawal.

Masanin ya ƙara da cewa "idan kuma mota gare ka to yanzu mutum zai iya komawa babur ko motar haya duk dai domin a samu a tsira daga yanayin da ake ciki."

Faɗaɗa hanyoyin samu

..

Asalin hoton, Getty Images

Wannan ce hanya babba da dama daga cikin mutane ba sa bi abin da ke jefa su cikin yanayi maras kyawu.

"Idan mutum ɗan kasuwa ne to maimakon ya ci gaba da tafiya da sana'a guda ɗaya sai ya samu wasu sana'o'in da zai yi domin tallafa wa wadda yake yi.

Idan kuma mutum ma'aikacin gwamnati ne to shi ma sai ya samu wasu ƴan kananan sana'o'in da za su rinƙa kawo masa kuɗi." In ji Dakta Lawal Habib.

Masani ya zayyana wasu sana'o'i guda huɗu da ya ce su ne ya kamata jama'a su yi a lokacin da tattalin arziƙin ƙasa ke fuskantar matsala kamar haka;

  • Kayan abinci: Kayan abinci ya zamo dole ga jama'a saboda haka kasuwanci a harkar na kawo alkairi.
  • Magunguna; Buƙatar magani ta zama dole saboda ciwo da ake yi. Wannan ne ya sa ake ganin sana'ar harkar magani na kawo riba sosai kuma sana'a ce da ba a daina ta.
  • Harkar sufuri: Ita sana'ar sufuri a mota ko babur dole ce duk tsananin tattalin arziƙin da ake ciki saboda haka yana da kyau ƴan kasuwa da ma'aikata su faɗaɗa harkokin samu ta shiga harkar sayar da magunguna.
  • Harkar sadarwa: Mutane suna raina harkar saye da sayar da katin waya ko kuma datar intanet amma sun zama dole a wannan zamani kuma suna taimaka wa mutane sosai wajen rage dogaro ga sana'ar da suke yi.

Gargaɗi

Sai dai daga ƙarshe masanin ya yi gargaɗi ga ma'aikata masu karɓar bashin banki a wannan yanayin.

"Ina son jan hankalin ma'aikatan da ke karɓar bashin banki su sayi mota ko babur ko kuma wani abun da dai ba zai sama musu kuɗin shiga ba.

Ban ce ka da a karɓi bashin banki ba amma idan aka karba to ya kamata a saka su wajen da za su hayayyafa. Misali ka shiga harkar kayan abinci ko magunguna ko sufuri ko kuma sadarwa. Hakan zai sa mutum ya rinƙa samun kuɗin shiga ta yadda ko banki na cire masa kuɗin daga albashinsa ba zai girgiza ba." In ji Dakta Lawal Habib, masanin tattalin arziƙi a Kano.