Musulman Ingila da ke cikin fargaba kan tarzomar da ke faruwa a Birtaniya

Huma Khan
Bayanan hoto,Huma ta ce ba za ta sauya yadda take tafiyar da lamuranta ba a yanzu amma kullum tana zaune cikin shiri
  • Marubuci,Reda El Mawy
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari,BBC News Arabic
  • Aiko rahoto dagaManchester

"Abin da mutane ke kira da zanga-zanga, ni a zahiri ina kiran sa da harin ta'adanci," a cewar Huma Khan.

Huma Khan, malama ce a wata makaranta a Stockport da ke Greater Manchester kuma ta kudiri aniyar cigaba da gudanar da ayyukanta na yau da kullun duk da ƙaruwar tashe-tashen hankali a biranen Birtaniya, amma kuma duk da haka, tana cikin farbaga da damuwa.

Khan ta shaida wa BBC cewa: "Gaskiya yanayin yadda tashe-tashen hankali suka yi ƙamari ya ba ni mamaki."

"Rikicin da mutane ke kira da zanga-zanga gaskiya ni ina kiransa da harin ta'adanci, kuma yadda jita-jita ta yaɗu kan rikicin a shafukan sada zumunta ya ba ni mamaki ƙwarai da gaske."

Ta ce ba za ta sauya yadda take tafiyar da lamuranta ba a yanzu amma za ta zauna cikin shiri.

Khan ta ƙara da cewa: “Da yake na girma cikin yanayin da a kodayaushe za a iya kai min hari saboda addinina da kamannina, da kuma yadda yanayin irin tufafin da nake sakawa."

"Ba zan dawwama cikin tsoro ba amma kuma duk lokacin da na fita daga gida, a cikin damuwar kada na shiga cikin wata matsala nake." in ji ta.

'Yar natsuwa

Alaa
Bayanan hoto,Alaa na da shagon sayar da litattafai na Larabci, "ba ni son nuna kai na saboda ba ni son sake fuskantar cin zarafi" in ji shi

Tashin hankali na iya haifar da yanayi maras daɗi.

Lokacin da muka ziyarci Cibiyar Sayayya ta Salford a kusa da Manchester ranar Talata da yamma, ko'ina shiru ba yadda aka saba gani ba.

An kuma shawarci ‘yan kasuwa da su rufe da wuri saboda jita-jitar intanet na yiwuwar zanga-zanga.

Mutane ƙalilan ne kawai ke wajen, kuma an ga ‘yansanda sun tsaya suna binciken wasu samari da fuskarsu take a rufe.

Amma kuma sabanin haka, ayyuka na cigaba da gudana a Moss Side da ke kudancin Manchester, wuri da aka fi sani da al'ummar musulmi daga Asiya da Gabas ta Tsakiya, da Afirka.

Mazauna da ma'aikata a yankin sun ce suna cikin kwanciyar hankali a cikin al'ummarsu, amma sun damu matuƙa da abubuwan da ke faruwa a sauran sassan ƙasar.

Abdul
Bayanan hoto,Abdul Hakeem ya tsere daga yaƙi a Somaliya sama da shekara 20 da suka gabata. Ya nuna damuwa kan rikici tsakanin masu tsattsauran ra'ayi da kungiyoyin Musulmi

Alaa, wanda ya fita daga Siriya a cikin 2018 kuma yanzu yake da kantin sayar da litattafan Larabci a Manchester, ya ce danginsa sun samu mafaka a Birtaniya. Duk da haka, abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun sa shi cikin fargaba.

"Ba ni son nuna kai na saboda ba ni son sake fuskantar cin zarafi" kamar yadda ya shaida wa BBC.

Abdul Hakeem kuma, wanda ya tsere daga Somaliya da yaƙi ya daidaita sama da shekaru 20 da suka gabata, ya nuna damuwa kan rikici tsakanin masu tsattsauran ra'ayi da kungiyoyin musulmi. "Idan wadannan kungiyoyin suka hadu, hakan na iya haifar da tarzoma ko ma yakin basasa, kamar abin da ya saka na tsere daga Somalia zuwa Manchester," in ji shi.

Alaa ya ce ya kuma damu da kiranye-kirayen da ƙungiyar Musulmi a can suka yi na cewa a kare masallatai da sana'o'i ko da a ce za a yi amfani da tashin hankali.

'Na san muna da ƴancin kare masallatanmu da kuma addininmu, amma kuma idan muka yi amfani da tashin hankali wajen yin hakan, dama za su samu wajen kiranmu ƴanta'adda."

'Ban taɓa fuskantar nuna wariya ba a nan'

Jawad
Bayanan hoto,"Tabbas mun taɓa ganin tashin hankali a shekaru 20 da suka gabata" in ji Dr Jawad Amin

Saeed ɗan asalin Syria, ya je Birtaniya shekara uku da suka wuce, kuma ya shafe lokaci mai tsawo a balaguro tsakanin ƙasashen Turai.

"Na yi yawo a ƙasashen Turai kuma ina da shaidar zama ɗanƙasar Sweden. Na zo nan Ingila ne da gangan saboda ana girmama dukkan addinai. Musulami, da Kiristoci, da Yahudawa - kowa na zaune cikin salama.

"Na yi mamaki ƙwarai lokacin da na ji kalaman wariyar da ake yi kwanan nan. Ban taɓa fuskantar wariya ba. Mun ɗan firgita lokacin da muka fara jin hakan. Shekarata uku a nan, mutane a nan na da kirki sosai."

Boren ya karaɗe Birtaniya ne da kuma Ireland ta Arewa tun bayan kisan da wani mahari ya yi wa wasu 'yanmata uku da wuƙa a Southport da ke arewa maso yammacin Ingila ranar 29 ga watan Yuli.

Tarzomar ta ƙara ta'azzara ne sakamakon labaran ƙarya da aka dinga yaɗawa a intanet, da masu tsattsauran ra'ayi da ke ƙin jinin 'yancirani.

"Tabbas mun ga tashin hankalii cikin shekara 20 da suka wuce," a cewar Dr Jawad Amin, shugaban ƙungiyar kare Musulman Manchester ta Greater Manchester Muslim Safety Forum.

"Abin da ya fi damun mu game da wannan [na Southport] shi ne ya faru ne kawai saboda labaran ƙarya da ake yaɗawa a shafukan zumunta, wanda masu neman aikata laifukan ƙiyayya ke yaɗawa," kamar yadda ya shaida wa BBC.

"Ko maharin Musulmi ne ko ba haka ba babu dalilin da zai haifar da tarzomar da muka gani."