Hanyoyi huɗu da za ku iya yin aiki da rayuwa a ƙasashen Turai

..

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,Turai

"Ina son zuwa Turai, amma ba ta kowane hali ba," in ji Abdel K, wanda muka samu a wani kamfanin shirya tafiye-tafiye da ke birnin Dakar.

A hirar da muka yi da shi, mun fahimci yadda yake da ƙwarin gwiwa, game da yiwuwar tafiyar tasa, domin ya shafe fiye da mako guda yana tattaunawa da kamfanin domin samun biza, don ci gaba da karatunsa a Faransa.

A wani kantin sayar da kayayyaki da ke birnin, mun haɗu da Houessou A, ɗan asalin ƙasar Benin, mai kimanin shekara 40.

Ya ce hutu ya zo tare da iyalinsa daga Belgium inda yake zaune. Ya ce a shekarar 2010 ne ya fice daga ƙasarsa ta gado bayan kammala karatunsa na Diploma inda ya samu aiki a Belgium.

"Na samu bizar a kan lokacin, wato bizar damar aiki a ƙasar. A yanzu ina zaunea ƙasar tare da iyalaina cikin kwanciyar hankali, duk bayan shekara biyu muna zuwa hutu ko mu je Cotonou ko kuma mu zo nan Dakar, inda na yi karatuna,'' in ji shi.

Kamar dai wannan, da yawa daga cikin matasan Afirka ko wasu ƙasashe da ke fatan zuwa ci-rani ƙasashen Turai. Wasu na ƙoƙarin tabbatar da mafarkinsu ta hanyar bin doka, yayin da wasu ke yunƙurin tabbatar da burin ta ɓarauniyar hanya, inda kuma daga ƙarshe suke faɗa wa hannun hukumomi.

Cikin gomman shekaru, Turai ta kasance cibiyar 'yan ci-rani, inda take jan ra'ayin miliyoyin matasa a fa din duniya, saboda ingantuwar tattalin arzikin nahiyar, da tsarin shugabanci mai inganci.

A yayin da annobar korona ta rage tuɗaɗar 'yan ci-rani zuwa nahiyar a 2020 zuwa 2021, a yanzu batun na sake farfaɗowa.

"Tarayyar Turai ta gabatar da wasu dokokin ci-rani," in ji Adama Mbengue, shugaban ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta 'Action for Human Rights and Friendship (ADHA), mai mazauni a birnin Dakar, na Senegal.

A yanzu 'yan ci rani za su iya samun damar shiga Turai ta halastacciyar hanya. Musamman bayan da kungiyar Tarayyar Turai ta sake nazarin dokokinta kan 'yan ci-rani a shekarun baya-bayan nan, domin bai wa 'yan ci-ranin da suka cika sharudan da ƙungiyar ta gindaya damar zama a ɗaya daga cikin ƙasashen nahiyar.

'Yan ci-rani a Turai

.

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,Tarayyar Turai ta gindaya sharuɗan zaman 'yan ci-rani a nahiyar.

Ɗan ci-rani "shi ne mutumin da ke zaman wucin-gadi a wata ƙasa r da nan aka haife shi ba, kuma yake samun muhimman abubuwan buƙata a ƙasar'', kamar yadda hukumar UNESCO ta bayyana.

A wasu lokutan zaman ɗan ci-rani a ƙasar ka iya zama halastacce ko haramtacce.

To sai dai Tarayyar turai ce kawai ke da alhakin gindaya sharuɗan shiga ko kuma zama a ɗaya daga cikin ƙasashensta, ciki har da batun zuwan iyalan ɗan ci-rani.

Yarjejeniyar Geneva ta 1951 - wanda daga ta haifar da ta Schengen da sauran yarjejeniyoyi, musamman ta Lisbon, sun yi bayanin sharuɗan da ya kamata 'yan ci-rani su cika kafin samun izinin zaman Turai.

Ga wasu hanyoyi huɗu da za ku samun izinin shiga Turai da sauran ƙasashen da ke maraba da 'yan ci-rani.

1- Haɗuwa da iyali

Za ka iya shiga Turai ƙarƙashin sharaɗin haɗuwa da iyali. Wannan hanya ce da za ta bai wa ɗan ci-rani - ƙarƙashin wasu sharuɗa - damar shigar da wasu makusantan iyalansa, ciki har da mata ko miji da ƙananan yara.

Mutanen da ke wajen ƙasashen Turai masu bizar zama a ɗaya daga cikin ƙasashen Turai na aƙalla shekara guda, waɗanda kuma ke da damar neman izinin zama na dindindin, za su iya neman buƙatar kai iyalansu, domin su zauna tare.

Kenan a taƙaice iyalan waɗanda ke zaune a Turai, ko 'yan ƙasashensu ka iya komawa Turai domin samun ɗan'uwansu ta hanyar amfani da yarjejeniyar 'Haɗuwa da iyali'.

Sharaɗin neman buƙatar haɗuwa da iliya, da kuma takardun da ake buƙata, za a duba su a matakin ƙasar da mutumin ake buƙatar shiga.

2- Izinin kwangila ko aiki

Wata hanya da ake iya samun izinin shiga Turai ta halastacciyar hanya ita ce samun aiki a ɗaya daga cikin ƙasashen nahiyar.

Hanya mafi kyau ita ce samun aiki a Turai, musamman ƙasar da kake son zuwa.

Idan ka samu aikin, kuma ka cika sharuɗan aikin da ake son ɗaukarka Turan, to Kamfanin da ya ba ka aikin ne da kansa zai nemar maka bizar daga hukumomin da ke da alhakin bayar da ita.

Da farko mutumin ne zai rubuta takarda neman bizar aiki a ƙasar da ya samu aikin.

Hanyoyin sun bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, kuma zai iya ɗaukar makonni ko ma watanni.

Abubuwan da ake buƙata na samun wannan biza ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa.

Kuma dole ne kamfanin da ya ba ka aikin shi ma ya rubuta takardar nemar maka bizar domin tabbatar da buƙatarka.

Mista. Mbengue ya ce, "wasu ƙasashen irin Jamus da Faransa da wasu suna bayar da biza ga mutanen da ke da wata ƙwarewa a wasu ɓangarori."

..

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,Ci rani

3- Bizar karatu

Haka ma bizar karatu, halastacciyar hanya ce ta shiga Turai, musamman ga waɗanda ba 'yan nahiyar ba.

Wannan biza za ta ba ka damar damar zama a wata ƙasar nahiyar Turai, har ma ka yi aikin wucin-gadi a lokacin dakake karatun.

Wannan ma sharaɗin da hanyar da ake bi sun bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa.

Dole ne ɗalibi ko ɗaliba su nuna shaidar samun izinin gurbin karatu a ɗaya daga cikin ƙasashen Turai, sannan sai yana da kuɗin da zai iya ɗaukar nauyin kansa a lokacin karatun nasa.

"Wannan bizar ta wucin-gadi ce, kuma za a iya tsawaitata idan ta ƙare. Hakan ya sa wasu 'yan Afirka ke amfani da damar don ci gaba da zama a Turai ta hanyar yin karatun Diploma a fannoni da dama'', in ji Adama Mbengue.

Ya kara da cewa "bayan kammala diploma, wasu kan buƙaci bizar aiki domin su zauna a can tare da yin wasu sana'o'i."

4- Neman mafaka da kariyar jinƙai

''Mai neman mafaka, shi ne mutumin da ayyana kansa a matsayin ɗan gudun hijira, amma bai samu wannan matsayin ba a ƙasar da ya nemi iznin zama'', kamar yadda UNESCO ta bayyana.

Yarjejeniyar Geneva ta 1951, ta bayyana matsayin ɗan gudun hijira da cewa '' shi ne duk mutumin da ya ƙaurace wa mazauninsa, bisa dalilai na gudun cutarwa saboda ƙabilarsa ko addininsa ko ƙasarsa ko kasancewarsa cikin wata kungiyar siyasa ko ta ra'ayi, zuwa wata ƙasar da ba tasa ba domin samun kariya daga fargabar da yake fuskanta a ƙasarsa''.

“Mutanen da ke guje wa ƙasashensu sakamakon yaƙi, ko muzgunawa ko rayuwa cikin hatsari a ƙasashensu na asali, kan zaɓi zuwa Turai saboda yadda take bai wa mutane mafaka,” in ji Adama Mbengue.

A yanzu, masu son bizar neman mafaka na ɗaya daga cikin hanyoyin da 'yan ci-rani ke shiga Turai. Kuma waɗanda suka samu wannan biza kan shiga Turai ta halastacciyar hanya.

Baya ga waɗannan hanyoyi, akwai kuma bizar kasuwanci da ake bai wa ƙwararrun ma'aikatan da ke buƙatar shiga Turai da masu zuba jari.

Akwai kuma bizar zama na wucin-gadi a duka ƙasashen Turai, in ban da Cyprus da Ireland, biza ce da ke bai wa mutane damar zaman wata uku a duka kasashen Turai in ban da guda biyun can.

''Bayan wata ukun dole ne mutum ya fice daga yankin, misalin wannan biza ita ce bizar yawon buɗe idanu,'' in ji Mbengue.

Rukunin 'yan ci-ranin da ke samun wannan bizar sun haɗa da ɗalibai, da masu ƙwarewa, kamar injiniyoyi da likitoci da masu aikin jinya, da ƙwararun masu fasaha da sauransu.

Ƙasashen Turai da 'yan ci-rani suka fi shiga

 .

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,Turai

A maganar gaskiya, 'yan ci-rani ka iya shiga kusan duka ƙasashen Turai, sai dai kawai sharuɗa shiga ƙasashen ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa.

France : Ofishin kula da 'yan gudun hijira da marasa muhalli na Faransa (OFPRA) ya wallafa rahotonsa na 2023 kan masu neman mafaka ranar 18 ga watan Yuli.

Rahoton ya nuna cewa a shekarun baya-bayan na Faransa a samu ƙarin masu neman mafaka da kashi 8.7 a 2023 idan aka kwatanta da 2022.

Daga cikin mutum 142,649 da suka nemi izini a 2023, mutum 56,204 daga nahiyar Afirka suke.

Kuma ƙasashen nahiyar biyu, DR Kongo da Guinea na cikin ƙasashe biyar da al'umominsu suka fi neman mafaka a Faransa.

Sharaɗun neman biza da ƙasar ta sanya na da sauƙi, hakan ya sa 'yan ci-ranin suka fi neman Faransa a takardunsu na neman shiga Turai, kamar yadda masanin haƙƙin ɗan'adam ya bayyana.

Jamus : Jamus na da tsare-tsare masu sauƙi ga samun iznin shiga ƙasar daga 'yan ci-rani musamman ƙwararrun ma'aikata, kamar yadda ADHA ta bayyana.

"Jamus ta ɓullo da shirye-shirye na musamman domin ɗaukar hankalin 'yan ci-rani."

Sweden : Masanin haƙƙin ɗan'adam din ya ce Sweden na da tsare-tsare masu kyau da ke bai wa 'yan-ci rani saukin shiga ƙasar.

Spain : "Ƙasa ce da ke bai wa 'yan ci-rani damarmaki musamman ma'aikata da ɗalibai da 'yan kasuwa, inda take da sharuɗa masu sauki ga 'yan ci-rani," in ji Adama Mbengue.

Portugal : Ita ma wannan ƙasa na da sauƙin dokoki ga masu buƙatr shiga ƙasar, musamman masu zuba jari da 'yan kasuwa da ma'aikata masu ƙwarewa ta musamman.

Akwai kuma wasu kasashe irin su Albania masu sauƙaƙan dokoki ga masu neman biza domin shiga cikinsashen