by MUHAMMAD AUWAL UMAR
July 12th 2024.

Hanyoyi huɗu da Najeriya za ta bi don kauce wa faɗawa Yunwa



Getting IMAGE 
Bayanan hoto,
Manoma da dama musamman a arewa maso yammacin Najeriya sun gudu sun bar gonakinsu saboda matsalar tsaro
Yanzu haka mutum miliyan 31 ne ke cikin matsananciyar yunwa, a cewar rahoton WFP, waɗanda suke cikin aji na uku cikin biyar na ma'aunin yunwa.

Sai kuma miliyan 81 da ke fuskantar barazanar shiga yunwar nan da shekara shida masu zuwa, in ji rahoton hukumar.

"Babbar matsalar da ta haifar da halin da ake ciki ita ce tattalin arzikin ƙasa," in ji Dr Sulaiman. "Ɗagawar farashin abinci da sauran kayayyaki sun taimaka sosai."

Ya ƙara da cewa tashin farashin man fetur ta sa kayayyaki sun ƙara tsada saboda akan yi jigilar akasarin kayan noma ta tituna.

"Matsalar tsaro ma na saka mutane su yi gudun hijira, wanda ke sa su rasa gonakinsu," a cewarsa.

Matakan da suka kamata a ɗauka

ASALIN HOTON,SULAIMAN ABUBAKAR
Bayanan hoto,Dr Abubakar Sulaiman masani ne a harkar abinci kuma tsohon mataikamakin shugaban hukumar abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya
Dr Abubukar Sulaiman ya ce akwai matakai na gaggawa da kuma masu dogon zango da suka kamata a ɗauka. Ya yi bayani kamar haka:

Tallafi

Masanin ya ce akwai mutanen da suka riga suka galabaita, waɗanda hukumar WFP ta saka su cikin aji na biyu, da na uku a matakin matsalar yunwa.

Irin waɗannan lallai ne sai an taimaka musu, a ba su tallafi saboda ko ma me aka yi musu ba su da yadda za su yi su samu abincin saboda ba su da hanyar samun.

Kyautata tsaro

Akwai ƙarancin noma da kuma zuba jari a harkar noman kansa yanzu saboda matsalar tsaro.

Mutane kan yi noma amma ba su amfana da shi saboda wasu 'yanbindiga kan ƙwace amfanin ko kuma su ce sai sun biya haraji. Irin wannan kan sa noman ya ragu.

Sauya dabarun noma


Akwai buƙatar a sauya dabarun noma, musamman dabarun noman rani da kuma na ajiyarsa ta yadda abinci ba zai lalace a gona ko a rumbun ajiya ba.

Sannan sai an samar da iri na zamani waɗanda ba su buƙatar ruwa mai yawa.

Tallafa wa ƙananan manoma

Dole ne sai gwamnati ta tallafa wa ƙananan manoma saboda su ne ginshiƙin noma a Najeriya.

Ba wai gwamnati ba ta ba da tallafin ba ne, matsalar dai ba shi kaiwa ga manoma na ƙasa. Saboda dole sai an ƙara ƙoƙari.

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
Search Website

Search

Explore

Tags

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support