by MUHAMMAD AUWAL UMAR
July 12th 2024.

Wane ne sabon Firaiministan Birtaniya, Keir Starmer?

Keir Starmer making a speech


Asalin hoton, Getty Images

Sa'o'i 4 da suka wuce


Sir Keir Starmer ya zama sabon Firaiministan Birtaniya bayan jagorantar jam'iyyar Labour zuwa ga gagarumar nasarar da ta samu a zaɓen da aka gudanar a ƙasar.


Keir ya maye gurbin Jeremy Corbin a matsayin jagoran jam'iyyar Labour ne shekara huɗu da suka gabata, kuma tun wancan lokacin ne ya yi ta fafutikar ganin jam'iyyar ta ƙara samun goyon baya daga al'umma.


Jam'iyyar Labour ta kwashe shekara 14 ba tare da ta jagoranci gwamnati ba a Birtaniya.

Rayuwarsa kafin shiga siyasa


Sir Keir ya zama ɗan majalisa ne daga baya, lokacin da ya zarta shekara 50 a duniya, bayan ya kwashe shekaru yana aikin lauya.


To amma, a tsawon rayuwar tasa ya kasance mutum ne mai son harkokin siyasa, kuma mutum ne mai son kawo sauyi tun lokacin ƙuruciyarsa.


An haife shi ne a birnin Landan a shekarar 1962 - ɗaya a cikin ƴaƴa huɗu a wurin mahaifinsa - ya girma a yankin Surrey da ke gabashin ƙasar Ingila.


Mahaifinsa ma'aikacin kamfani ne yayin da mahaifiyarsa kuma malamar jinya ce.


Iyayensa sun kasance riƙaƙƙun magoya bayan jam'iyyar Labour.


An raɗa masa sunan Keir ne albarkacin sunan shugaban jam'iyyar Labour na farko, kuma mai haƙar ma'adanai ɗan asalin Scotland, Keir Hardie.


Rayuwar mahaifansa na cike da ruɗani. Sir Keir ya ce mahaifinsa ba mutum ne mai jansu a jiki ba.


Mahaifiyarsa ta yi fama da wata lalurar garkuwar jiki, inda a mafi yawancin rayuwarta ba ta iya tafiya ko kuma magana.


Haka nan lamarin ya kai ga datse mata ƙafa.


Sir Keir ya shiga cikin gungun matasa ƴan jam'iyyar Labour a yankinsa lokacin yana ɗan shekara 16.


Haka nan a wani lokaci na rayuwarsa ya kasance editan jaridar 'Socialist Alternatives', mai rajin kawo sauyi.


Sir Keir lokacin da yake karatu a jami'a

Sir Keir ne mutum na farko a gidansu da ya taɓa zuwa jami'a. Ya yi karatun harkar shari'a Leeds da Oxford, daga nan sai ya yi aikin lauya a ɓangaren kare hakkin ɗan'adam.


A lokacin da yake harkar lauyanci, ya yi fafutikar ganin an kawar da hukuncin kisa a ƙasashen yankin Karebiya da kuma wasu ƙasashen Afirka.


A wata mashahuriyar shari'a kan ke nufin cewa da aka tafka cikin shekarun 1990, Keir ya kare wasu ƴan gwagwarmayar kare muhalli biyu, waɗanda babban gidan cin abinci na MacDonalds ya shigar da su ƙara bisa zargin ɓata suna.


A shekarar 2008, an naɗa Sir Keir a muƙamin shugaban sashen gabatar da ƙara na Birtaniya, wanda hakan na nufin babu wani mai gabatar da ƙara a Ingila da Wales sama da shi.


A watan Mayu ya shaida wa BBC cewa: “Akwai yiwuwar mu sauya shawara kan wannan batu saboda mun samu kanmu cikin wani yanayi na rashin kudi.”


Sai dai Sir Keir ya ce gwamnatin Jam’iyyar Labour za ta rika karbar harajin hada-hadar kudi kan kudin makaranta na makarantu masu zaman kansu.


Sir Keir da matarsa Victoria suna daga wa ‘yan jam’iyya hannu

Bayanan hoto,An rika ganin matar Sir Keir, Victoria a lokutan yakin neman zabensa

Muhalli


Jam’iyyar Labour ta zabtare alkawarin da ta dauka a 2021 na cewa za ta kashe fan biliyan 28 a shekara daya kan shirye-shiryen samar da tsaftataccen makamashi, sai dai ya ce zai dore da shirye-shiryen samar da cibiyoyin samar da lantarki ta hanyar iska da kuma bangaren samar da baturan motoci masu amfani da lantarki.


Wannan ya janyo masa suka daga ‘yayan jam’iyyar Conservatives, wadanda ke zargin shi da kokarin “zulle” wa wasu manyan alkawurra da ya dauka.


A baya-bayan nan Sir Keir ya dauki alkawarin zuba jarin kudi fan biliyan takwas a bangaren tsaftataccen makamashi ta hanyar wani kamfani da ake kira GB Energy.


Haka nan ya yi alkawarin kawar da amfani da abubuwa masu gurbata muhalli wajen samar da makamashi wajen samar da lantarki a Birtaniya, nan da shekara ta 2030.

........

Ya riƙe muƙamin har zuwa shekarar 2013, kuma masarautar Birtaniya ta karrama shi da ɗaya daga cikin lambar yabo mafiya daraja a shekarar 2014.



Sir Keir lokacin da masarautar Birtaniya ke karrama shi


Wannan ya janyo masa suka daga ‘yaya

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
Search Website

Search

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support