by MUHAMMAD AUWAL UMAR
July 14th 2024.

An samu gobara a fadar Sarkin Kano

.

ASALIN HOTON,KANO STATE GOVT

Fadar Sarkin Kano ta sanar da cewa an samu tashin wuta a wani bangare na ginin masarautar da ke Kofar Kudu a daren Asabar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar wadda ta samu sa hannun Dan Buram na Kano, Munir Sanusi Bayero ta ce: “An samu ibtila’in wuta a fadar waje da ke fadar mai martaba sarkin Kano ta Kofar Kudu da asubahin ranar Asabar 13 ga watan Yulin 2024“.

Sanarwar ta ci gaba da cewa “Ba a samu wata mummunar barna ba kuma babu wanda ya jikkata sanadiyyar lamarin.”

Haka nan sanarwar ta kara da cewa ana daukar duk matakan da suka dace wajen kare lafiyar wadanda ke zaune a fadar.

Tun farko, ɗaya daga cikin 'ya'yan sarkin Ashraf Sanusi ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin, wanda ya ce tun tsakar daren jiya aka cinna wutar.

Ya ce har yanzu ba a kai ga gano waɗanda suka cinna wutar ba.

''Waɗanda suka cinna wutar ba a kai ga gano su ba, amma dai alhamdullahi babu wanda ya ciwo sakamakon faruwar lamarin, sannan an riga an kashe wutar da safe'', kamar yadda ya shaida wa BBC.

A cikin watan Mayu ne dai gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16, bayan sanya hannu kan dokar da ta yi gyara ga dokar da ta kafa masarautun Kano guda biyar ta 2019.

Tun daga lokacin ne kuma ake cikin turku-turka dangane da sarautar Kanon , bayan da ɓangarenb sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero suka garzaya kotu don nuna rashin amincewarsu da matakin.

Kotun dai ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da sabuwar dokar masarautun har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci game da batun.

Tun wancan lokacin ne kuma Sarki Aminu Ado ke ci gaba da zama a gidan sarki na Nasarawa, yayin da Sarki Muhammadu Sanusi ke zaune a gidan sarki na ƙofar Kudu.

A cikin makonnin da suka gabata ne rundunar ‘yansanda a Kano ta tura jami’anta domin tsaurara tsaro a fadar.

Rundunar ta kuma bayyana cewa ta kawar da ‘yan tauri da mafarauta wadanda suka yi dandazo a fadar tun bayan rudanin da ya turnuke game da batun halastaccen sarkin Kanon.

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
Search Website

Search

Explore

Tags

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support