Jiragen Ukraine marasa matuƙa masu amfani da fasahar Yamma don kai hari Rasha

Wani hoton da aka ɗauka da tauraron ɗa Adam da aka ɗauka a 25 ga Agusta na tashar man Proletarsk.

ASALIN HOTON,PLANET LABS

Bayanan hoto,Tashar man Proletarsk da Rasha da ke yankin Rostov da ta ƙone bayan harin Rasha
  • Marubuci,Jonathan Beale
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari,Defence correspondent

Ukraine na samun tallafin fasahohin yaƙi da kuɗaɗe daga ƙasashen Yamma wajen kai ɗaruruwan hare-hare masu dogon zango a cikin Rasha.

Wannan ne zuwa ne a daidai lokacin da NATO take cigaba da ƙin amince da ba Ukraine damar amfani da alburusan ƙasashen Yamma - saboda gudun ta'azzarar yaƙin.

Ukraine na ta ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare masu dogon zango a cikin Rasha a cikin ƴan watannin nan, inda jiragenta marasa matuƙa suka kai wasu hare-hare a tare a wurare masu muhimmanci a mako guda.

Daga cikin wuraren da aka kai harin sun haɗa da sansanin soja da tashar man fetur da alburusai da cibiyar kula da harkokin yaƙi.

Yanzu Ukraine tana aiki jirage marasa matuƙa suna kai ɗaruruwan hare-hare a wata.

Wani kamfanin ya bayyana wa BBC cewa tun yanzu waɗannan hare-haren sun fara tasiri a kan Rasha.

 AQ 400 Scythe

ASALIN HOTON,TERMINAL AUTONOMY

Bayanan hoto,Jirgi mara matuƙi na AQ 400 Scythe da katako ana haɗa shi, kuma yana iya tafiyar kilomita 750.

BBC ta samu jin ta bakin wasu waɗanda suke cikin harkokin hare-haren nan ka'in da na'in.

Ciki har da wani kamfanin da ya ƙera ɗaya daga cikin jiragen da kai hare-haren, da kuma wani kamfanin da ya ƙirƙira wa Ukraine wata manhaja tattara bayanai domin kai hare-haren.

Francisco Serre-Martins ya ce tsarin ya fara ɗaga hankalin Rasha. Ya yi amannar cewa idan Ukraine ta ƙara samun tallafi, yaƙin zai iya komawa kan uwa da wabi.

Wata 18 da suka gabata, wani kamfani da yake cikin waɗanda suka assasa mai suna Terminal Autonomy bai ma fara aiki ba.

Amma yanzu suna assasa ɗaruruwan jirage marasa matuƙa na AQ400 Scyth masu nesan zango a wata ɗaya, waɗanda za su iya kai hari mai nisan kilomita 750 (mil 465).

Haka kuma kamfanin ya ƙirƙiri wasu ɗaruruwa jiragen masu gajeren zango na AQ100 Bayonet waɗanda suka iya tafiya wasu ƴan kilomita.

Da katako ake amfani wajen haɗa jiragen, sannan a wajen aikin kafinta ne ake aikinsa a Ukraine.

Mista Serra-Martins, wanda tsohon sojan Austreliya ne sashen injiniya ya assasa kamfanin tare da wani abokinsa, tare da kuma tallafin Amurka.

Kamfanin na cikin kamfanoni aƙalla uku da suke haɗa jirage marasa matuƙa a Ukraine.

Misalin awa ɗaye ske yi wajen ƙirƙirar jirgin, sannan a ɗauki awa ɗaya ana harhada kayayyakin ciki na lantarki da wajen ɗaukar bama-baman.

Kamfanin yana sayar da jirgin ne a kan wasu ƴan dubban daloli.

A ɗaya ɓangaren kuma, jirgin kariya na Rasha da zai iya kakkaɓo zai kai farashin sama da Dala miliyan ɗaya.

Jirgin mara matuƙa na Bayonet ya kai $2,000

ASALIN HOTON,TERMINAL AUTONOMY

Ba wai sauƙin farashinsa ba ne kaɗai abin lura.

Palamtor, wani babban kamfanin fasaha na Amurka na cikin kamfanonin fasaha na Yamma na farko-farko da suka taimaka wa Ukraine.

Kamfanin ya fara ne taimakon Ukraine da fasahar da ke taimakon makaman Ukraine masu linzami wajen kai hari.

Yanzu kuma kamfanin ya ba Ukraine wasu kayan aiki domin tsara yadda za su kai hari mai nisan zango cikin sauƙi.

Haka kuma wasu injiniyoyi daga kamfanin Palantir, tare da haɗin gwiwar abokan aikinsu na Ukraine, sun ƙirƙira wata manhaja da take fitar da taswirar da ke taimakawa wajen kai harin daidai inda ake so.

Palantir ya fito ya bayyana cewa babu ruwansa da yaƙin, amma kuma ya taimaka wajen horar da mutanen Ukraine sama da 1,000 yadda ake amfani da manhajar.

An gwada wa BBC yadda ake amfani da manhajar. Ta hanyar amfani da wasu bayanai, tana iya tattaro bayanan taswirar sararin samaniyar Rasha, da tsaron samanta.

Ta hanyar amfani da manhajar, Ukraine ta gano yanayin tsaron sararin samaniyar Rasha.

Louis Mosley na kamfanin Palantir ya ce manhajar na taimakon Ukraine wajen tattara bayanan sirrin fasahar yaƙin, musamman tsaron sararin samaniyar ƙasar, domin sanin yadda za ta kai hare-hare da kyau.

"Fahimta da ganin hotunan yadda sararin samaniyar ƙasar zai taimaka wajen kai hare-haren," in ji shi.

Ana kai waɗannan hare-haren masu dogon zangp ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa ƙarƙashin jagorancin sashen leƙen asiri na rundunar sojin Ukraine, inda suke aiki a sirrance. Amma wasu majiyoyi sun bayyana wa BBC wasu bayanai game da yadda suke gudanar da aikin.

Ana iya aiki jirage marasa matuƙa da dama suka kai hare-hare a tare - ina iya aika har guda 60 a tare.

Wani jirgi mara matuƙi ya sama wani gidan mutane a Saratov a ranar 26 
 ga August

ASALIN HOTON,EPA

Bayanan hoto,Kamar sauran hare-haren soji, jirage marasa matuƙa na Ukraine ɗin sun raunata fararen hula.

Yawanci an fi kai waɗannan hare-haren a cikin dare. Sai dai ana kakkaɓo da yawa daga cikinsu, amma kamar kashi 10 suna dacewa.

Wasu jiragen ma tsaron sararin samaniyar Ukraine ɗin na gida ne yake kakkaɓo su.

Manhajar Palantie ya riga ya fitar da taswirar yanayin sararin samaniyar Rasha.

Mista Serra-Martins ya ce aika jiragen marasa matuƙa da dama a tare ne zai gajiyar da aikin tsaron sararin samaniyar Rasha.

Wannan ke na ya sa suke haɗa jiragen masu sauƙi da suka fi sauƙi a kan masu kakkaɓo su.

Farfesa Justin Bronk na Royal United Services Institute ya ce hare-haren jirage marasa matuƙan masu nesan zango suna ɗaga hankalin Rasha.

Duk da cewa Rasha na da tsaron sararin samaniya mai inganci, amma ba zai yiwu ta iya tsare komai ba.

Farfesa Bronk ya ce irin yanayin hare-haren Ukraine ɗin nan, sun sa yansu ƴan Rasha, "suna fargabar cewa Rasha ba za ta iya ba su cikakkiyar kariya ba."

Farfesa Justin Bronk ya ce kai hare-hare a kan sansanin sojin saman Rasha ne babbar hanyar da Ukraine take iya ɗaga hankalin Rasha.

Hare-haren sun tilast wa Rasha rage kai hare-hare.

Hoton tauraron ɗan Adam da ke nuna sansanin sojin sama na Marynovka kafin a kai masa hari da bayan harin.

Ukraine ta yi amannar cewa za ta iya yin sama abin da take yi a yanzu idan ta samu ƙarin taimako daga yamma, musamman na makamai masu dogon zango, sai dai ƙawayen ƙasar suna cigaba da yin watsi da buƙatar ta Ukraine.

Har yanzu akwai fargaba, musamman a Amurka da Jamus, na tsoron shigar da ƙasashen Yamma cikin rikicin.

Amma wannan bai hana Ukraine samun taimako daga kamfanonin Yamman da ma samun kuɗaɗe ba.

BBC ta tattauna da wani kamfanin Ukraine wanda yake aikin ƙirkira wani makami mai linzami, wanda farashin makami mai linzami na kamfanin Storm Shadow na Birtaniya ya ninka sau kusan 10.

Ita dai Ukraine a shirye take ta cigaba da kai hare-harenta a Rasha.

Mista Serra-Martins ya ce, "abin da ke faruwa yanzu ba komai ba ne a kan abubuwan da za su faru zuwa ƙarshen shekarar nan."