Select a date and time slot to book an Appointment
Date Of Appointment
An zartar wa wasu ƴan’uwan juna ƴan asalin Najeriya guda biyu hukunci kan laifin sanadin mutuwar wani matashi ɗan shekara 17 da suka yaudara ta hanyar lalata a intanet
Ƴan’uwan guda biyu ƴan asalin Legas, sun ja ra’ayin Jordan DeMay har ya tura masu hotunansa na tsaraici bayan sun yi ƙaryar cewa mace ce tsararsa – daga baya kuma suka ci amanarsa.
Ya kashe kansa, ƙasa da sa’a shida bayan sun fara magana a Instagram.
An yanke musu hukuncin ɗaure shekara 17 da wata shida a gidan yarin Amurka.
Wannan ne karon farko da aka hukunta ƴan Najeriya kan yaudara ta hanyar lalata a Amurka, wani al’amarin da ya yi ƙamari a intanet wanda kuma ake yawan alaƙantawa da Najeriya.
Mahaifiyar Jordan, Jenn Buta, ta yi maraba da hukuncin amma ta ce babu wani sakamakon da ya dace game da shari’ar.
Jordan DeMay ya yi fice kuma ɗan wasan tsere ne a makaranta daga Michigan.
Samuel Ogoshi,mai shekara 24, da Samson Ogoshi, mai shekara 21, sun tura masa saƙon neman zama aboki a Instagram inda suka yi ƙaryar cewa mace ce kyakkyawa kuma tsararsa inda suka ci gaba da kalaman batsa.
Da zarar sun samu hotunan matashin na batsa, sai su nemi daloli daga wajensa, tare da barazanar za su yaɗa hotunan a intanet ko da abokanansa idan har bai biya kuɗin ba.
Jordan ya tura masu kuɗi iya ƙarfinsa, tare da sanar da ƴan damfarar cewar zai iya kashe kansa idan har suka yaɗa hotunan.
Ƴan damfarar sun mayar masa da amsa cewa: “Da kyau... ka gaggauta – ko zan iya sa ka aikata.”
Ƴansandan Amurka sun yi gano masu laifin a Legas a bara, kuma suka yi nasarar karɓo su domin fuskantar shari’a.
Sun amsa laifinsu a watan Afrilu kan yadda suke yaudarar maza matasa a Michigan da sassan Amurka.
Sun kuma amince za su bayar da haɗin kai domin hukunta masu irin masu aikata laifinsu.
Akwai kuma wani ɗan Najeriya wanda ake zargi da alaƙa da mutuwar Jordan da aikata wasu laifukan da ake neman miƙa shi.
Da take magana da BBC a birnin Marquette a watan Mayu, mahaifiyar Jordan ta yaba wa ƴansanda kan ƙoƙarin da suka yi na bin sawun ƴan Najeriyar.
Amma ta ce tana da ra’ayinta ya sha bamban game da yadda ƴan’uwan junan ƴan Najeriya da ake tsare da su
“Sauƙi ne cewa ana tsare da wanda ake zargi amma kuma babu wani abin jin daɗi da ke fitowa daga ɓangaren iyalina ko kuma waɗanda suka aikata hakan,” in ji ta.
“Ina kewar ɗana wanda ba ya misaltuwa, amma mahaifiyar waɗannan mutane ita ma tana kewarsu, ita ma ba ta da laifi kan wannan laifin, in ji Jenn Buta.
Masu bincike da hukumomin tsaro sun ce irin wannan matsalar ta fi yin ƙamari a Najeriya.
A watan Afrilu, an kama wasu ƴan Najeriya biyu bayan da wani ɗan makaranta a Australia ya kashe kansa.
Akwai kuma wasu mutanen biyu da ke fuskantar shari’a a Legas bayan wani matashi ɗan shekara 15 ya kashe kansa a Amurka da kuma wani ɗan shekara 14 a Canada.
Ƴansandan Najeriya kuma na aiki tare da ƴansandan Scotland domin binciken mutuwar wani ɗan shekara 16 Murray Dowey wanda ya kashe kansa a Disamba.
A Janairu, wata cibiyar bincike ta intanet a Amurka ta nuna wani shafin intanet ƴan Najeriya a TikTok da YouTube da ke koyar da dubarun damfara ta hanyar lalata, kuma yawancin bayanan na turancin buroka ne na Najeriya.
Wani masanin tsaron Intanet a Najeriya Farfesa Adedeji Oyenuga daga Jami’ar jihar Legas ya ce yana fatan yadda ake hukunta masu aikata wannan taɓi’a zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar.
Matsalar na ƙaruwa inda ƴan Najeriya ma na faɗa wa tarkon ƴan damfarar, kuma a cewar Farfesa Oyenuga ƴansanda suna samun nasarar kama su.
Wannan ba shi ne karon farko ba da ƴan Najeriya musamman matasa ke faɗawa cikin wannan aikata laifin.
An fi sanin su da sunan ƴan Yahoo, waɗanda ke damfara ta intanet domin samun kuɗi. Wannan matsalar ta bayyana ne a farkon shekarar 2000 inda ake turo da sakwannin imel ta Yahoo.
Dr Tombari Sibe, daga wani kamfanin tsaro na intanet a Najeriya ya ce, damfara a intanet ba wani sabon abu ba ne tsakanin ƴan Najeriya musamman matasa, amma yana fatan hukuncin da aka yanke wa su Ogoshi zai zama darasi.
“Ya kamata a yaɗa wannan hukuncin sosai domin ya zama darasi ga matasa cewa yaudara ta intanet zai iya kai wa ga rasa ran mutum da kuma hukunci a gidan yari mai tsauri,” in ji shi.
Hukumar ƴansanda ta Tarayyar Turai da FBI ta Amurka da hukumomin tsaro na Birtaniya dukkaninsu sun yi gargaɗi a bara kan ƙaruwar aikata laifukan damfara ta hanyar lalata a intanet.
We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!
Have a great day!
Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support