Hare-haren Lebanon: 'Rasa ido ba zai karya mana gwiwa ba'

Young Lebanese boys in blue shirts and yellow ties hold up paper with colour photocopied images of their school friend who was killed.
Bayanan hoto,Yara ƴan makaranta rike da hotunan yaron da aka kashe a harin na ranar Talata
  • Marubuci,Joya Berbery & Carine Torbey
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari,BBC News Arabic, Beirut

An sake jin ƙarar fashewar abubuwa karo na biyu lokacin da dandazon mutane suka taru domin yin jana'izar waɗanda suka mutu a fashewar na'urori a faɗin Lebanon.

Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce aƙalla mutum 14 ne suka mutu sannan 450 suka jikkata sanadiyar fashewar na'urorin.

A wajen ɗaya daga cikin wurare da aka fito jana'izar, masu jimami sun nuna fushinsu yayin tattaunawa da BBC.

A ɗaya gefen kuma, likitoci sun kwatanta irin munanan raunukan da mutane suka ji a matsayin abin da ba a saba gani ba..

Tawagar BBC da ke ƙasar na bin diddigin labarin a faɗin Beirut, babban birnin Lebanon:

00:48
Bayanan bidiyo,Bidiyo: Ɗaya daga cikin na'urorin sadarwa da aka gano bayan fashewar a Lebanon ranar Laraba

'Raɗaɗin da muke ciki ba zai misaltu ba'

Kowa na ɗari-ɗari da mutanen da ke amfani da wayar salula ko kuma wata na'ura bayan fashewar da aka samu ranar Talata, da kuma Laraba.

Yayin da ake gudanar da jana'izar waɗanda aka kashe a yau Alhamis, ciki har da wani karamin yaro, mun ji ƙarar fashewa nan take kuma mutane suka shiga fargaba.

Daga nan mutane suka fara guduwa ta ko'ina. Dole muka bar wurin jana'izar domin samun gidan ɓuya.

Duk da haka, na yi ƙoƙarin tattaunawa da mutane a wurin jana'izar domin sanin abin da ke faruwa.

Dandazon mutane ne suka taru a can domin halartar jana'izar wani karamin yaro ɗan shekara 11 da kuma wasu mambobin Hezbollah uku da aka kashe a fashewar na'urorin sadarwa ta Pager ranar Talata.

Wani karamin yaro a wajen jana'izar ranar Laraba 18 ga watan Satumba
Bayanan hoto,Wani karamin yaro a wajen jana'izar ranar Laraba 18 ga watan Satumba

Maza da mata har ma da yara ƴan makaranta ne aka gani a kan tituna rike da fostoci da alluna da ke ɗauke da hoton yaron da ya mutu.

Wasu sun rike tutocin Hezbollah masu launin ruwan ɗorawa, wasu kuma bakake waɗanda ke ɗauke da hoton jagoran Hezbollah, Hassan Nasrallah.

Mata sun ɗora furanni kan gawawwakin waɗanda lamarin ya rutsa da su. Wurin sananne ga mutane irina wanda ya sha halartar jana'izar mambobin Hezbollah a can baya.

Wasu iyaye sun je wajen da ƴaƴansu.

Mutane sun faɗa min cewa sun yi imani abin da ya faru babban laifi ne da kuma zalunci ga ɗan'adam, sai dai hakan zai ƙara musu karfin gwiwa da kuma rashin tsoro.

Kalamansu na nuna irin na mutane da ke cikin ɓacin rai da raɗaɗi. Mutane da yara da dama ne suka fito rike da lasifika suna addu'a sanye kuma da tufafi daban-daban domin yin bankwana da yaron mai shekara 11.

Mata rike da faranti na furanni sun ɗora su kan gawawwakin mutanen da suka mutu.
Bayanan hoto,Wasu mata rike da faranti cike da furanni sun ɗora su kan gawawwakin mutanen da aka kashe

Na tambayi wani matashi ko ya san wani daga cikin mutanen da suka ji rauni.

Ya faɗa cewa: "Kowa ya san wani a ciki. Raɗaɗin da muke ciki ba zai misaltu ba.

"Amma wannan abu ne da muka saba, kuma za mu ci gaba da jajircewa, in ji shi."

Wata mata mai shekara 45 da ke kusa da ni a wajen jana'izar ta faɗa min cewa: Wannan zai ƙara mana karfin gwiwa, duk wanda ya rasa ido ɗaya, zai yi amfani da ɗayan wajen yin faɗa kuma dukkan mu kan mu a haɗe yake'.

Dandazon mutanen sun kwatanta yaron da aka kashen a matsayin wanda ya yi shahada
Bayanan hoto,Dandazon mutanen sun kwatanta yaron da aka kashen a matsayin wanda ya yi shahada

'Na ga tashin hankalin da ban taɓa gani ba tsawon rayuwata'

Harabar asibitin Mount da ke birnin Beirut ta cika da ɗaruruwan mutane, amma abin ya fara sauki a safiyar yau Alhamis, inda mutane da dama ke jira a wajen asibitin domin jin halin da ƴan'uwansu ke ciki.

Abin ya sha bamban da daren Talata - lokacin da asibtin ya cika da ihu da kuma kukan mutanen da suka ji raunuka waɗanda aka kawo bayan fashewar na'urori.

Farfesa Elias Warrak likitan ido ne kuma ya ce a dare ɗaya kawai ya cire idanun mutanen da suka ji ranunuka fiye da wanda ya yi tsawon rayuwarsa ta aiki
Bayanan hoto,Farfesa Elias Warrak likitan ido ne kuma ya ce a dare ɗaya kawai ya cire idanun mutanen da suka ji ranunuka fiye da wanda ya yi tsawon rayuwarsa ta aiki

Na yi ƙoƙarin tattaunawa da Farfesa Elias Warrak wanda likitan ido ne a nan asibitin Mount da ke Lebanon, inda ya bayyana abin da ya gani ranar Talata tamkar a mafarki. Ya ce "ta kasance rana mafi muni a rayuwata."

Zaune a cikin ofishinsa ya faɗa min cewa: "Abin takaici, a daren jiya na cire idanu da yawa na mutanen da suka ji frauni iye da waɗanda na yi tsawon shekara 25 ina aiki a matsayin likita."

"Ina so na ceto idon aƙalla mutum ɗaya cikin waɗanda suka ji rauni, amma hakan bai samu ba, na cire dukkan idanun saboda abin fashewa ya shiga can cikinsu."

Yayin da muke tattaunawa a ofishinsa, ya nuna ya natsu amma cike yake da raɗaɗi, ya tuna abin da ya faru da kuma abin da ya gani.

Ya ce: "Ba za a iya jure wa abin ba. Yawancin waɗanda abin ya shafa sun kasance matasa da ba su fi shekara 20 ba kuma ta kai ga dole na cire dukkan idanun wasu. Ban taɓa ganin tashin hankali irin wanda na gani jiya ba tsawon rayuwata."

Ya ce ya kasance a asibitin yana kula da waɗanda suka jikkata kusan sa'o'i 24, inda yake ɗaukar hutu na karamin lokaci.

An samu raguwar hayaniyar mutane a harabar asibitin Mount da ke Lebanon ranar Laraba
Bayanan hoto,An samu raguwar hayaniyar mutane a harabar asibitin Mount da ke Lebanon ranar Laraba

A ɗaya gefen, Dakta Warak ya yaba wa ƴan uwa da kuma iyalan waɗanda suka jikkata da kuma jajircewarsu bayan abin da ya faru da ƴan uwansu na hakurin da suka yi.

Kusan mutum 3,000 ne suka jikkata, yayin da 200 ke cikin mawuyacin hali.

A sabuwar fashewa da aka samu, aƙalla mutum 14 ne aka kashe sannan sama da 450 suka ji raunuka, a cewar ma'aikatar lafiya ta Lebanon.

Mutane da dama da suka jikkata sun je asibiti ranar Talata da dare domin ba su magani
Bayanan hoto,Mutane da dama da suka jikkata sun je asibiti ranar Talata da dare domin ba su magani

Hezbollah wadda Iran ke mara wa baya, ta ce na'urorin pagers da suka faffashe sun kasance na ma'aikatan hukumominta ne da dama kuma ta tabbatar da mutuwar mayakanta.

Ƙungiyar ta ɗora laifin harin kan Isra'ila, kamar yadda shi ma Firaiministan Lebanon ya faɗa. Sojojin Isra'ila ba su ce uffan ba kan lamarin.

Jim kaɗan bayan faruwar fashewar, na yi magana da wasu jami'an lafiya.

"Abin tashin hankali ne da kuma firgitarwa," kamar yadda wani likita ya faɗa min.

Ya ƙara da cewa yawancin mutane sun ji raunuka ne a kwankwaso da fuska da idanu da kuma hannayensu.

An faɗa min cewa: "Mutane da dama sun rasa yatsunsu, wasu ma dukkansu."

Ɗaukacin ƙasar na cikin alhini da kuma kaɗuwa, inda mutane ke cikin ɗimuwar kuma suka kasa fahimtar abin da ya faru.

Zan iya cewa abin da ya faru yana da girman gaske kuma ba za a iya misalta shi ba har ma ga ƙasar da abubuwa suka saba faruwa.