Lebanon ta fuskanci mummunar rana sakamakon hare-haren Isra'ila kan Hezbollah

- David Gritten
- BBC News
Sama da mutum 270 aka kashe yayin da 1,000 suka jikkata sakamakon hare-haren bama-baman Isra'ila a Lebanon, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta sanar.
Wannan na zuwa bayan Isra'ila ta yi gargadin cewa za ta ƙarfafa hare-hare kan Hezbollah.
Dubban mutane ne suka tsere daga gidajensu bayan da rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hare-hare wurare 800 na maɓuyar Hezbolla tare da gargaɗi ga fararen hula.
Hezbollah ta ƙaddamar da hare-haren rokoki a arewacin Isra'ila bayan hare-haren. Amma jami'an lafiyar Isra'ila sun ce mutum ɗaya kawai ya ji rauni.
Rana ce mai muni kusan cikin shekara a faɗan kan iyaka da ke ƙara haifar da barazanar yaƙi.
Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya António Guterres ya ce yana tsoron rikicin zai iya mayar da Lebanon "wata Gaza."
Watanni sha ɗaya na faɗa tsakanin Hezbolla da Isra'ila wanda yaƙin Gaza ya haddasa ya kashe ɗaruruwan mutane, galibinsu mayakan Hezbollah, tare da raba dubban da muhallinsu musamman a yankunan kan iyakokin ɓangarorin biyu.
Hezbollah ta ce tana faɗa ne domin goyon baya ga ƙungiyar Hamas ta Falasdinawa, kuma ta ce ba za ta daina ba har sai an tsagaita wuta.
Dukkanin ƙungiyoyin biyu sun samun goyon bayan Iran waɗanda Isra'ila da Birtaniya da sauran ƙasashe suka ayyana a matsayin ƴanta'adda.
Kafofin yada labaran Lebanon sun ruwaito cewa jiragen yaƙin Isra'ila suka fara kai jerin hare-hare a ƙasar da safiyar Litinin.
Sun kai hare-hare a wurare da dama a kudancin Sidon da Marjayoun da Nabatieh da Bint Jbeil da Tyre da Jezzine da Zahrani, da kuma wasu sassa na lardin Bekaa mai tsaunika, kamar yadda kamfanin dillacin labaran NNA ya bayyana.
Daga baya, kafar ta ce hare-haren Isra'ila sun yi ƙamari da sassan kudanci da kuma Bekaa, wanda suka yi ta'adi sosai.
Ministan lafiya na Lebanon Firas Abiad a ranar Litinin ya ce mutum 274 aka kashe a hare-haren, yayin da mutum 1,024 suka jikkata.
Sai dai bai bayyana adadin fararen hula ba ko kuma mayaƙan da aka kashe amma ya ce 21 daga ciki yara ne, 31 kuma mata.
Ya ƙara da ce dubban mutane ne aka raba da gidajensu sakamakon hare-haren.

A sanarwar da ta fitar ranar Litinin, rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta kai hare-hare ta sama kusan 800 kan Hezbollah a kudancin Lebanon da kuma yankin Bekaa Valley.
Tun da farko, mai magana da yawun rundunar Rear Admiral Daniel Hagari ya shaida wa manema labarai cewa bidiyo ya nuna yadda makaman "Hezbolla suka tarwatse a cikin wani gida."
"Dukkanin gidajen da muka kai wa hari suna ɗauke da makamai - rokoki da masu linzami, wadanda ke shirin kashe ƴan Isra'ila, " kamar yadda ya yi iƙirari.
Ya kuma yi gargaɗi ga fararen hula su gaggauta ficewa daga wuraren makaman Hezbollah domin "lafiya da tsaronsu."
Tun da farko ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya faɗi a wani bidiyo cewa dakarun ƙasar za su ƙarfafa hare-hare a Lebanon." Aikin zai ci gaba har sai mun cimma burinmu na mayar da mutanen arewaci gidajensu lafiya," in ji shi.

Hezbollah ba ta ce komi ba kan iƙirarin Isra'ila cewa ta kai hare-hare inda take ɓoye makamai, amma a cikin wata sanarwa ta ce ta mayar wa hare-haren "rashin imani na Isra'ila" ta hanyar cilla rokoki a sansanonin sojin Isra'ila da ke arewaci da kuma wata cibiyar ƙera makamai a Zvulun da ke arewacin Haifa.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce aƙalla rokoki 125 suka tsallaka Lebanonin, kuma wasu da ba tantance ba sun faɗa yankunan Galilee da Carmel da yankunan HaAmakim da and Hamifratz da ke Golan Heights.
An tarwatsa wani gida da makamin roka a Givat Avni a yankin Galilee.
Wani mazauni yankin David Yitzhak ya shaida wa BBC cewa shi da matarsa da ƴarsa ƴar shekara shiga ba abin da ya same su domin sun yi ƙoƙarin fakewa daga wata babbar kofar daki lokacin da suka ji ƙarar gargaɗi.
Jami'n lafiyar Isra'ila sun ce sun yi wa wani mutum mai shekara 59 magani da ya samu rauni yayin da kuma wani ya samu rauni.
A ranar Lahadi, Hezbollah ta ce sama da rokoki 150 ta harba da jirage marar matuka a Isra'ila, yayin da kuma Isra'ila ta kai daruruwan hare-hare ta sama a kudancin Lebanon.