'Sun yi min tsirara, suka tattaɓa min wuraren da ba su dace ba'

- Ibrat Safo
- BBC News Uzbek
“Kina da sura mai kyau, ya faɗa. Wane irin jima'i kika fi so?''
Kamilla Norova, mai shekara 25 wadda ta sauya jinsi daga namiji zuwa mace, ta kaɗu matuka yayin da take bayyana yadda aka ci zarafinta lokacin da take tsare a hannun jami'an tsaro a Uzbekistan, ƙasar da ke tsakiyar nahiyar Asiya da kuma ta kasance cikin tsohuwar jamhuriyar Soviet.
Ya bar Rasha lokacin da yake da shekara 17 a duniya, saboda yana son sauya jinsi, sai dai ya ajiye shaidarsa ta ɗan ƙasar Uzbekistan.
Shin sauya jinsi na da sauƙi a Uzbekistan?
Babu wuraren sauya jinsi a Uzbekistan kamar yadda yake a wasu ƙasashe.
Yayin da ya kasance babu alkaluman yawan mutanen da suka sauya jinsi, sai dai wasu bayanai sun nuna cewa mutane na iya sauya jinsi a cikin ƙasar, duk da cewa ba kasafai ake iya ganin haka ba, amma mutane na sauya jinsinsu.
Sai dai yawancin ƴan Uzbekistan da ke son sauya jinsi na barin ƙasar zuwa Rasha ko kuma wasu ƙasashe.
Bayan yi mata aikin sauya jinsi, Kamilla ta koma Tashkent, babban birnin Uzbekistan kawai domin sabunta fasfo ɗinta, kuma ta ce an tsare ta a can da yi mata tambayoyi, ta shafe kwanaki 25 a tsare, inda ta fuskanci cin zarafi, duka, barazana ga rayuwa, da kuma binciken lafiya.
Babu hakkokin masu sauya jinsi a cikin kundin tsarin mulkin Uzbekistan.
Duk da haka, ana bai wa mutane sabbin shaidar zama ɗan ƙasa da kuma fasfo ɗin da tabbatar da cewa sun sauya jinsi, ko da a waje aka yi musu aikin.

Yayin da muke magana da ita a kafar sada zumunta, Kamilla ta nuna min katin shaida da ta karɓa tun da farko kafin a tsare ta a Tashkent wanda ke nuna jinsin ta a matsayin mace.
"Daga lokacin da na karɓi katin shaida ta, na nemi fasfo ɗin fita waje," in ji ta.
"Shugaban ofishin bayar da fasfo ya ce za a min ƴan tambayoyi, saboda hakan na cikin ka'idoji ga duk wanda ke zaune a waje."
Ta amince da hakan inda aka kai ta wani ɗaki "Mai lamba 3" wanda ya kasance na bayar da fasfo a lardin Tashkent. A can, ta haɗu da wani matashin ɗansanda mai suna 'Bobur' wanda bai haura shekara 20 ba.
Bobur ya fara duba cikin wayarta wanda ke ɗauke da hotunan jikinta bayan da aka yi mata aikin sauya jinsi, kamar yadda Kamilla ta iya tunawa.
'Ya buƙaci na buɗe kirjina'
"Ya ce, kina da jiki mai kyau, kirjinki gwanin ban sha’awa. Wane irin salon jima'i kika fi so? Kina iya hulɗa da maza biyu a tare a lokaci guda?”
Duk da cewa Kamilla ta fusata da waɗannan maganganu, Bobur ya ci gaba inda ya kuma ya buƙaci "ta buɗe kirjinta don ya taɓa nononta". Ba ta yi hakan ba, inda ta buge hannun ɗansandan yayin da ya yi ƙoƙarin taɓa ta. Amma Bobur ya nace sai ya taɓa ta.
"Daga nan ya cire wata takarda ya rubuta lambar wayarsa a kai. Ya kuma saka lambarsa a wayata. Ya tambaye ni ina nake zaune, kuma ko akwai otal-otal a kusa da inda nake.
'Za mu iya haɗuwa a otal,' in ji shi. Na yi ƙoƙarin in ki kula shi da tambayar yaushe zan samu fasfo ɗina. 'Eh, za mu haɗu a otal, sannan za ki same shi nan ba da jimawa ba. Nan da nan na fara kuka kuma an bar ni na yi tafiya ta."
Daga baya shugaban ofishin bayar da fasfo ɗin ya faɗa mata cewa Bobur yana a ɓangaren binciken masu aikata ta'addanci ne na hukumar ƴansanda.

Sashen BBC a Uzbekistan ya tuntuɓi ‘Bobur’ ta wata manhajar tattaunawa ta hanyar amfani da lambar da ya bai wa Kamilla da kuma gabatar masa da zargin da ake yi masa. An karanta sakon amma ba a mayar da martani ba.
Bayan kaɗuwa da irin cin zarafinta da aka yi a ofishin, Kamilla ta ɗauki matakin shari'a da kuma gabatar da korafi a hukumance. Daga baya an sake kiran ta a wani ofishin gwamnati.
Ta haɗu da ƴansanda maza biyu a can, inda aka buƙaci ta bar wayarta a wani wurin ajiya a ɗakin saukar baƙi da kuma tafiya da ita zuwa ɗakin amsa tambayoyi. Ba a bar ƙawayenta da ƴan‘uwan da suka raka ta shiga ɗakin ba.
"Da farko komai ya tafi daidai, sai dai bayan mintoci kaɗan suka fara faɗa min abubuwa marasa daɗi," kamar yadda Kamilla ta faɗa.
'Dukkanku karuwai ne'
“Dukkan masu sauya jinsi ɗaya suke, dukkanku karuwai ne,' suka faɗa. Sun zarge ni da samun masoya a manya-manyan wurare, kamar cikin ƴan majalisa. Bayan wani lokaci, na buƙaci a ba ni ruwa.
"Zan yi fitsari cikin kwalba, kuma za ki sha fitsari na,' ɗaya daga cikin ƴansanda ya faɗa. 'Me ya sa kika yi korafi kan Bobur?' ɗayan ya tambaya. 'Yanzu za ki girbi abin da ya sa kika yi haka."
Nan da nan barazana da zagi ya koma duka, in ji Kamilla. Akwai lokacin da ɗaya daga cikin jami'an ƴansandan, ya riƙe maƙogoronta, ya tura ta jikin bango, ya fitar da bindigarsa sannan ya ce, "Za ki mutu a nan", yayin da take ta haki, kamar yadda ta iya tunawa.
“Daga nan kofa ta buɗe, inda ƴansanda mace da miji suka shigo. Jami'in da ya riƙe min maƙogoro kawai ya fara marina, ya tura ni kuma saboda ina sanye da takalma masu tsini kawai na faɗi a ƙasa. Sauran suka yi ta dariya.
"Yayin da nake ƙoƙarin tashi, kawai ya ci gaba da duka na. Na nemi taimakon macen da ke cikinsu, 'Ke mace ce, ba ki ganin abin da ke faruwa, yana dukan mace?' Na faɗa. 'Ke ba mace ba ce, ya kamata a kashe mutane irin ku,' ta faɗa."
An sauraron buƙatar da ta yi na neman lauya. Maimakon haka ma, ƙarin ƴansanda suka shigo cikin ɗakin kuma suka taru suka ci gaba da dukan ta. An yi mata barazana da kuma tilasta mata saka hannu a kan wata takarda a Uzbekistan, amma saboda ba ta gama fahimtar harshen wurin ba, ba ta san a kan me ta saka hannu ba.
Yayin da aka kai ta gaban kotu, ta kaɗu bayan jin zarge-zargen da ake yi mata.
Alkalin ya ce a kan titi aka ɗauke ta, kuma ta ki bin umarnin jami'an ƴansanda.
Kamilla ta yi watsi da zarge-zargen amma an yanke mata hukuncin zaman gidan yari na kwanaki 15.
'Hakkin yin korafi'
Kamilla ta ce halin da ta shiga ya munana a gidan yari, inda ta fuskanci kunci, raɗaɗi da kuma gwajin lafiya na cin zarafi.
Bayan karewar kwanaki 15 na zaman wakafi da aka yi mata, ta ce an ƙara mata kwanaki takwas, da zargin bai wa wani jami'i cin hanci domin ta samu takardunta, abin da ta musanta.
Sashen BBC Uzbekistan, ya tuntuɓi Ma'aikatar Harkokin Cikin Gidan Uzbekistan tare da cikakkun bayanai kan zarge-zargen da ake yi wa Kamilla da kuma tambayar ko za a binciki jami'an da suka ci zarafin ta.
"Ɗan ƙasa da bai ji daɗin aikin hukumomi ba yana da hakkin shigar da korafi ta bin ka'idoji," kamar yadda ofishin yaɗa labaru na ma'aikatar ya bayyana a martanin da ya mayar.
Kallo mara kyau da ake yi wa masu sauya jinsi

A Uzbekistan, mutane na yi wa masu sauya jinsi da kuma masu auren jinsi daya kallo mara kyau. A kafafen sada zumunta, ana iya ganin hotunan bidiyo na cin zarafi da kuma dukan da ake yi wa masu sauya jinsi.
Kishin musulunci na ƙaruwa a ƙasar tun bayan da shugaba Shavkat Mirziyoyev ya ɓullo da ƴancin yin addini a ƙasar, inda masu da'awar addinin a kafafen sada zumunta da kuma malamai suka fito fili suka fara yin Alla-wadai da masu auren jinsi.
Masu auren jinsi da kuma masu sauyan jinsinsu da yawa sun kuduri aniyar barin Uzbekistan bayan jin ana yi musu barazana.
Kamilla ta bar ƙasar tana da shekara 17 inda ta tafi Moscow wurin ƴar‘uwarta. A can, ta fara aikin yin tiyata domin gyara jikinta don zama mace.
An soke zarge-zargen
Bayan fara rubutawa tare da rera waka a Rasha, Kamilla na da mabiya sama da 200,000 a shafin Instagram inda take wallafa hotuna da kuma bidiyon wakokin da take yi.
Hukumomin Uzbekistan sun ba ta sabon fasfo da ke nuna sabon jinsinta na mace.
Ta ce an faɗa mata cewa an soke dukkan zarge-zargen da ake yi mata.
Kamilla ta yi imanin cewa tana da ƴancin yin rayuwa yadda take so bayan irin tarin wahalhalu da ta fuskanta.
"Ina son na gina iyalina a yanzu, kuma idan dokoki suka bari, zan ɗauki rikon yarinya," in jiita